02
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa alƙawarin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, na yin wa'adi ɗaya kacal idan ya lashe zaɓen 2027, ba zai amfani muradun siyasar yankin Kudu maso Gabas ba. Mai taimaka wa Mataimakin Shugaban ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa, Stanley Nkwocha, ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan kalaman Obi a wata hira da ya yi da Channels Teleɓision, inda ya ce a shirye yake ya yi wa'adin shekara huɗu kawai. Nkwocha ya ce burin al'ummar Ndigbo na samar da shugaban…
