ukarofi

12504 Posts
Gwamna Raɗɗa Radda ya yi ta’aziyar rasuwar mawaƙi Kosan Waƙa

Gwamna Raɗɗa Radda ya yi ta’aziyar rasuwar mawaƙi Kosan Waƙa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Katsina ya bayyana rasuwar shahararren mawaƙin Muhammadu Buhari wanda aka fi sani da Kosan Waƙa a matsayin babban rashi ga ƙungiyar mawaƙan Hausa. Kosan Waka ɗan asalin ƙaramar hukumar Batagarawa a Jihar Katsina ya rasu yana da shekara 47 da haihuwa. A wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Muhammadu Kaula, Gwamna Raɗɗa ya bayyana Kosan Waƙa a matsayin mutumin kirki wanda yawancin waƙoƙin sa na ilmantarwa,da fadakarwa kan mahimmancin zaman lafiya. "Waƙoƙin sa na isar da saƙon zaman lafiya, ɗaukaka al'adunmu, ilmantar da al'umma akan siyasa da gwamnatin.Yana ɗaya…
Read More
An buƙaci Sarkin Daura ya ƙwace sarautar Rarara kan zargin cin mutuncin Sheikh Pantami

An buƙaci Sarkin Daura ya ƙwace sarautar Rarara kan zargin cin mutuncin Sheikh Pantami

Daga UMAR GARBA a Katsina Shugaban masu riƙe da sarautun gargajiya na jam’iyyar APC, Dakta Talba Abubakar ya yi kira ga Sarkin Daura da ya gaggauta tuɓe wa fitaccen mawaƙin siyasa Dauda Rarara rawaninsa na sarkin waƙar ƙasar Hausa, bisa zargin yin waƙoƙin cin mutuncin tsohon ministan sadarwa, Malam Isa Ali Pantami. Talba Abubakar ya buƙaci a tuɓe rawanin mawaƙin a cikin wata hira da aka yi da shi, inda ya ce bai kamata ya ci gaba da kasancewa da muƙamin ba sakamakon waƙoƙin da ake zargin ya yi kan Farfesa Isa Ali Pantami ɗan takarar gwamna na Jam'iyyar PDP…
Read More
Gwamnatin Gombe ta amince da haɗin gwiwa da BREACH kan ranar matasa ta duniya

Gwamnatin Gombe ta amince da haɗin gwiwa da BREACH kan ranar matasa ta duniya

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Gwamnatin Jihar Gombe ta bayyana shirinta na yin haɗin gwiwa da ƙungiyar BREACH Initiative for Leadership Development domin tabbatar da nasarar gudanar da bikin ranar matasa ta duniya ta 2026, wanda aka tsara domin ƙarfafa shugabancin matasa, wayar da kan jama'a game da alhakin ɗan ƙasa da kuma bunƙasa tsaro. An bayyana hakan ne yayin ziyarar neman haɗin gwiwa da ƙungiyar ta kai wa wasu manyan jami'an gwamnati, ciki har da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Hon. Adamu Dishi Kupto; Kwamishinan Matasa da Wasanni, Hon. Yusuf Abdu Kwadom; Mai Kula da Aikin…
Read More
Makarantar Threshing Floor International School ta ƙaddamar da sabbin ɗalibanta

Makarantar Threshing Floor International School ta ƙaddamar da sabbin ɗalibanta

Daga JOHN D. WADA a Lafia Makarantar Threshing Floor International School of Ministry and Biblical Studies wadda ita ce reshen ilimi na Threshing Floor Watchman Assembly wato Salvation City dake Bukan Sidi a Lafia jihar Nasarawa ta gudanar da taron ƙaddamar da sabbin ɗaliban ta na takwas a jiya Asabar inda ta ƙaddamar da sama da ɗalibai 20. Shugaban makarantar kuma Bishop na majami’ar Bishop Dr. Ovye John Attah ya taya sabbin ɗaliban murna tare da jagorar su da su riƙe hangen nesa da manufar cibiyar. A cewarsa makarantar ta himmatu wajen "haifar da zuriya ta manzanni na adalcin Allah…
Read More
Shugabar jam’iyyar LP ta yi kira da a yi zaɓen 2027 cikin lumana

Shugabar jam’iyyar LP ta yi kira da a yi zaɓen 2027 cikin lumana

Daga AHMID LAWAL a Abuja Shugabar Jam’iyyar LP Sanata Nenadi Usman, ta yi kira ga shugabannin siyasa da su ajiye ƙiyayya, su kuma tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya kasance gasa ta ra’ayoyi ba yaƙi ba. Usman ta yi wannan jawabi ne a Jos, babban birnin Jihar Filato, yayin bikin cika shekara 80 da haihuwa na tsohon Gwamnan Jihar Filato da tsohuwar Jihar Benue, Sanata Jonah David Jang, jiya. Wannan jawabi ya fito ne daga wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar a ƙasa, Ken Asogwa, ya fitar a Abuja, ranar Asabar. Asogwa yace shugabar jam’iyyar tace, makomar Najeriya…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya yi kira ga al’ummar jihar su guji siyasantar da matsalar tsaro

Gwamna Raɗɗa ya yi kira ga al’ummar jihar su guji siyasantar da matsalar tsaro

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya yi kira ga al'ummar jihar da su ci gaba da yin addu'o'in zaman lafiya, su mara wa jami'an tsaro baya, tare da kauce wa masu amfani da matsalar tsaro wajen cimma muradun siyasa. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin bikin Yaumul Shukur 2026, bikin godiya na shekara-shekara da ake gudanarwa domin tunawa da haɗewar tsoffin Lardunan Katsina da Daura a shekarar 1934. Gwamna Raɗɗa ya ce tabbatar da tsaro alhakin kowa ne, kuma bai kamata a mayar da shi batun siyasa ko son zuciya…
Read More
Masu fassarar finafinan Indiya na buƙatar tallafin gwamnati – Shugaban ƙungiyar Auwal Badi

Masu fassarar finafinan Indiya na buƙatar tallafin gwamnati – Shugaban ƙungiyar Auwal Badi

"kaso 95 cikin masu harkar fassarar fim matasa ne" Daga MUKHTAR YAkUBU Harkar fassarar finafinan Indiya da kasuwancin sa wata babbar hanya ce da dumbin matasan mu musamman na Arewa suka dogara da ita wajen tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum.  A yanzu wannan harka ta fassarar finafinan Indiya da kasuwancin sa tana ɗaya daga cikin manyan kasuwancin da take samar wa matasa aikin yi. kuma hakan ya taimaka wajen samun hanyar dogaro da kai ga matasa sama da miliyan ɗaya a faɗin ƙasar nan. Ganin irin kallon da ake yi wa Ita harkar da kuma yadda gwamnati ba…
Read More
Mazauna Abuja sun buƙaci gwamnati ta kafa ƙarfafan dokokin haya

Mazauna Abuja sun buƙaci gwamnati ta kafa ƙarfafan dokokin haya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matsalar gidaje a Babban Birnin Tarayya, Abuja, na ci gaba da ta'azzara sakamakon tsadar haya, ƙarancin gidaje masu araha da kuma saurin ƙaruwa da yawan jama'a. Lamarin ya sa samun ingantaccen masauki ya zama wani babban ƙalubale ga mazauna birnin, musamman ma'aikatan gwamnati, masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu matsakaitan kuɗaɗen shiga. Binciken da jaridar Blueprint ta gudanar ya nuna cewa ma'aikatan gwamnati, masu ƙananan sana'o'i da sauran masu ƙaramin albashi na daga cikin waɗanda wannan matsala ta fi shafa, yayin da masu gidaje ke ci gaba da ƙara kuɗin haya ba tare da wata doka…
Read More
’Yan Nijeriya miliyan 17 na iya fuskantar matsananciyar yunwa a 2027 – FEWS-NET

’Yan Nijeriya miliyan 17 na iya fuskantar matsananciyar yunwa a 2027 – FEWS-NET

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Aƙalla 'yan Nijeriya miliyan 16.99 ake hasashen za su fuskanci matsananciyar yunwa nan da watan Janairun 2027, a cewar sabon rahoton Cibiyar Kula da Gargaɗin Matsalar Yunwa (FEWS NET), wanda ya nuna cewa matsalar ƙarancin abinci a ƙasar na ci gaba da tsananta duk da ana sa ran girbin damina zai ɗan rage ta. Rahoton na cikin Takaitaccen Hasashen Tallafin Abinci na watan Yulin 2026 da FEWS NET ta fitar, wanda ya yi nazari kan yadda matsalar yunwa ke ƙara ta'azzara a ƙasashen da rikice-rikice da sauyin yanayi suka fi shafa, ciki har da Nijeriya. FEWS…
Read More
Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta cire rajistar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) da wasu jam'iyyun siyasa huɗu. A hukuncin da alkalai uku suka yanke baki ɗaya, kotun ta bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron shari'ar, saboda ƙarar da aka shigar ba ta cika ka'idojin doka ba. Haka kuma ta ce babu ingantacciyar hujja da za ta ba da damar cire rajistar jam'iyyun. Kotun ta kuma bayyana cewa alkalin Babbar Kotun Tarayya…
Read More