ukarofi

12504 Posts
Ta’addanci a Arewa: Ina mafita ta ke?

Ta’addanci a Arewa: Ina mafita ta ke?

A halin yanzu, babu shakka Arewa na matuƙar buƙatar mafita daga matsalolin rashin tsaro, musamman ta'addanci, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma hare-haren 'yan bindiga. A cikin wannan makon ne muka samu rahoton yadda wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne suka yi garkuwa da wani Alƙalin Babbar Kotu a Jihar Kebbi. Haka kuma, an kuma yi garkuwa da wani ɗan siyasa a Jihar Zamfara. Waɗannan al'amura abin takaici ne matuƙa. Sai dai, a wani ɓangaren kuma, an kama wasu da ake zargi da hannu wajen sace ɗalibai a Jihar Oyo, inda ake cewa alamu sun nuna…
Read More
Mu koyi hana juna ɓarna da yin ba daidai ba

Mu koyi hana juna ɓarna da yin ba daidai ba

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Mai karatu yau za ka ji rubutuna na wannan makon ya ɗauki wani salo kamar na mai wa'azi to, ba wa'azi ba ne, faɗakarwa ce da tunatarwa daga almajiri mai neman ilimi. Domin shi wa'azi malamai masu tawali'u da tsoron Allah ne ke yin sa, da baki ko a cikin ayyukansu. Na ce haka ne don mu fahimci shi wa'azi ba kawai sai a wajen aikin addini ko a wurin ibada ake yin sa ba. Muna ganin abubuwan wa'azi da dama daga ayyukan malamai da koyarwar su, da kuma abubuwan da ke faruwa a kewayen mu.…
Read More
Makarantun tsangaya (almajirci) gyara kaɗan suke buƙata ba haramta su ba

Makarantun tsangaya (almajirci) gyara kaɗan suke buƙata ba haramta su ba

Daga ABUBAKAR SANI (KWAMARED DAN BAHAUSHE) Karatun tsangaya wani irin karatu ne wanda ake yi a makaratun koyar da addinin musulunci a ƙasar Hausa shekaru da dama da suka wuce. Karatun ana yin sa ne ta hanyar yin rubutu a allo da kuma alƙalami. Ma fi yawan waɗanda suke yin wannan karatun su ne suke ciyar da kansu ta hanyar yin bara domin su samu abinci. Masu yin wannnan karatun yawancin su karatun alƙur'ani kaɗai suke yi babu ruwansu da karatun boko. Haka kuma ma fi yawancin su ba su cika yin sana'a ba sai dai bara, wanda ake kira…
Read More
Sunayen dawaki

Sunayen dawaki

Bisa ga sarauta, akwai jerin dawaki da martabarsu. 1. Kili Mago. Doki ne mai farin gashi baki daya, babu ko sofane. Kili Mago yana da idanu masu bakar fata haka kwadar ma baka ce. Shine na farko a daraja. 2. Kili:- Shima kamarsa daya ce da Kili Mago saidai yana da idanu masu jar fata haka kwarar ma ja ce. Shine na biyu a daraja.  3. Akawali: Doki ne baki wuluk. Wanda ya samu fari biyar watau goshi, da kafafu hudu (kofato zuwa gwiwa) ya fi duk sauran akawali daraja. A jerin darajar Dawaki, akawali yana matsayi na ukku. 4.…
Read More
Gwamnatin Katsina ta raba babura 50 ga masu sa ido kan makarantu

Gwamnatin Katsina ta raba babura 50 ga masu sa ido kan makarantu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta raba babura 50 ga jami'an kula da ingancin ilimi da sa ido kan makarantu a faɗin jihar, a ƙarƙashin shirin Transforming Education Systems at State Level (TESS), domin inganta sa ido da tabbatar da ingancin harkokin koyarwa. Kwamishinan ma'aikatar ilimi a Jihar Katsina, Malam Yusuf Suleiman Jibiya, ne ya ƙaddamar da rabon baburan a ranar Litinin. An rabawa daraktan sashen tabbatar da ingancin ilimi, daraktocin shiyyar tabbatar da ungancin ilimi guda 12, da jami'an tallafa wa makarantu guda 34 baburan domin sauƙaƙa musu gudanar da aikin sa ido a makarantu. A…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira miliyan 500 don yaƙi da tamowa

Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira miliyan 500 don yaƙi da tamowa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya amince da fitar da Naira miliyan 500 a matsayin gudunmawar gwamnatin jihar ga Child Nutrition Fund, domin ƙarfafa yaƙi da tamowa da inganta lafiyar yara. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da sabon shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Shafeeq Ur-Rehman, ya kai masa ziyarar girmamawa. Ya ce haɗin gwiwar gwamnati da UNICEF ya taimaka wajen rage matsalar tamowa, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da saka hannun jari a fannonin lafiya da ilimi. Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗauki malamai…
Read More
Dubban mutane sun tarbo ɗan takarar mataimakin gwamnan ADC a Kebbi

Dubban mutane sun tarbo ɗan takarar mataimakin gwamnan ADC a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Dubban mutane ne suka tarbo ɗan takarar kujerar mataimakin gwamnan jihar Kebbi Dokta Musa Muhammed Zagi ƙarƙashin jagorancin shugaban jam'iyyar ADC ta jihar Kebbi Injiniya Sufiyanu Bala a karon farko bayan tabbatar da shi a matsayin ɗan takara. Dokta Musa Zagi ya bayyana wannan ranar a matsayin rana ta musamman a rayuwar sa saboda irin yadda ƴan uwa da abokan arziki da masoya suka bar harkokin su suka ba shi lokacin su.Ya ce wannan ba ƙaramin abin alfahari ba ne ganin yadda dubban mutane suka tarbo shi saɓanin yadda a ke yi wa waɗansu ihu…
Read More
Alƙalin da aka yi garkuwa da shi a Kebbi ya shaƙi iskar ‘yanci

Alƙalin da aka yi garkuwa da shi a Kebbi ya shaƙi iskar ‘yanci

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Rahotanni daga garin Bunza sun bayyana cewa alƙalin babbar kotun da aka yi garkuwa da shi makon da ya gabata Faruku Hassan Bunza ya sami kan sa bayan kwashe sati ɗaya hannun ƴan bindiga da suka yi garkuwa da shi. Malam Ahmed Bunza ya bayyanawa waƙilin jaridar Blueprint Manhaja da cewa yau Litinin ɗin nan ne labarin dawowar Alƙali Faruku Hassan Bunza ya karaɗe garin na Bunza.Ya ƙara da cewa kawo yanzu dai babu wani sahihin bayani dangane da ko kuɗi ne aka biya ko kuma da wace manufa ce aka ɗauke shi amma dai…
Read More
Oyinkansola Badejo-Okusanya: Matar da ta karya tarihin shekaru 34 ta zama zaɓaɓɓiyar shugabar NBA ta farko

Oyinkansola Badejo-Okusanya: Matar da ta karya tarihin shekaru 34 ta zama zaɓaɓɓiyar shugabar NBA ta farko

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS  Funke Adekoya (SAN) ta yi takara sau biyu, a shekarun 2006 da 2014, amma ba ta yi nasara ba. Foluke Dada-Lawanson ma ta shiga tseren 2026 kafin daga bisani ta janye bayan cimma matsayar bai ɗaya da aka yi a yankin Yammacin ƙasar. Saboda haka, lokacin da Oyinkansola ta sanar da cewa ita ma za ta shiga takara, mutane da dama ba wai suna kallon zaɓen na zaɓar shugaba kawai ba. Suna kallon ko tarihi zai sake bai wa mace damar zama shugabar ƙungiyar ta hanyar cikakken zaɓe a karon farko. Tambayar…
Read More
Ƙungiyar Miyetti Allah za ta yaƙi ‘yan ci da ceto a Kebbi

Ƙungiyar Miyetti Allah za ta yaƙi ‘yan ci da ceto a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ƙungiyar Miyetti Allah reshen ƙaramar hukumar Augie da ke jihar Kebbi ta ce ta ja ɗamarar yaƙi da 'yan ci da ceto a yankin.Alhaji Rugga Shehu shugaban ƙungiyar na ƙaramar hukumar Augie ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da waƙilin jaridar Blueprint Manhaja a garin Augie ƙarshen makon nan. Alhaji Rugga Shehu ya ce lokaci ya yi da za a hana duk wani mutum shiga tsakanin fulani da hukuma idan wata shari'a ta samu saboda sau da yawa waɗansu fulani suna shiga tsakani da sunan ƙungiyar Miyetti Allah suna tatsar kuɗi…
Read More