ukarofi

12504 Posts
‘Yan sanda sun kama mutum biyu da ke da hannu wajen sace sojoji a Kebbi

‘Yan sanda sun kama mutum biyu da ke da hannu wajen sace sojoji a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta sanar da kama waɗansu mutane biyu da ke da hannu wajen sace sababbin sojoji a kan hanyar Anka zuwa Bukkuyum da ke jihar Zamfara yayin da su ke kan hanyar su bayan kammala karɓar horo daga makarantar horon ƙananan sojoji (Depot) Zaria. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi Sufurtandan ƴan sanda Bashir Usman ne ya sanar da haka ga manema labarai a garin Birnin Kebbi ranar talatar nan. Ya ce waɗanda aka kama sun haɗa da Abubakar Mallam Abubakar Gargam Bagega ƙaramar hukumar mulki ta Anka jihar Zamfara, Usman…
Read More
Annobar karuwanci a ƙasar Hausa

Annobar karuwanci a ƙasar Hausa

Daga MUKHTAR YAKUBU  Kasuwanci ana nufin saye da sayarwa. Duk wani aikin da mutum zai yi amfani da basirar sa ko kuma abin da ya koya daga wajen wani ko a makaranta ya aiwatar da shi domin neman kuɗi, shi ake cewa wa sana'a a Hausance. Ma'ana duk wata sana'a ta hannu kamar dinki, saka, kitso,kanikanci, tuki da makamantan su, su ake kira sana'ar  hannu. Ita dai kalmar karuwanci, kalma ce da bahuashe ya aro ta daga wajen Babarbare, a kalmar da suke cewa Karuwa, ma'ana mai yawun iska ko kuma iska, inda shi kuma Malam Bahaushe ya mayar da…
Read More
Masu ciwon sukari sun fi buƙatar kula da ƙafa

Masu ciwon sukari sun fi buƙatar kula da ƙafa

Daga AISHA ASAS Masu karatu, barkanku da sake saduwa a wannan makon cikin shafinmu na Kwalliya. Muna fatan darussan da muke tattaunawa suna ƙara wayar muku da kai kan yadda za a kare ƙafa da kuma kauce wa matsalolin da za a iya hana faruwarsu. A makonnin da suka gabata mun mayar da hankali kan muhimmancin kula da ƙafa, inda muka yi bayani kan matsalolin da rashin kula da ita kan haifar, tare da hanyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da lafiyarta. A yau kuma za mu ci gaba da wannan darasi ne ta fuskar da ta fi shafar…
Read More
Kasuwar Kurmi: Kasuwar da ta gina Jihar Kano ta kuma sauya tarihin kasuwancin Afirka ta Yamma

Kasuwar Kurmi: Kasuwar da ta gina Jihar Kano ta kuma sauya tarihin kasuwancin Afirka ta Yamma

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Blueprint Manhaja na ci gaba da kawo wa masu karatu shafinta na tarihi domin tunatar da al'umma muhimman abubuwan da suka taka rawa wajen gina tarihin Nijeriya, musamman waɗanda ba kasafai ake ba su kulawar da ta dace ba. A wannan makon, mun waiwayi tarihin Kasuwar Kurmi ta Kano, ɗaya daga cikin tsofaffin kasuwannin Afirka da ta yi fice wajen bunƙasa kasuwanci, sana'o'i da tattalin arziki tun sama da ƙarni biyar da suka gabata. Wannan nazari zai bayyana yadda kasuwar ta kasance ginshiƙin ci gaban Kano da kuma rawar da ta taka wajen haɗa Afirka Ta…
Read More
Rayuwa bayan ritaya: Tsari a ilimance don samun ingantacciyar rayuwa na biyu

Rayuwa bayan ritaya: Tsari a ilimance don samun ingantacciyar rayuwa na biyu

Tare da BILKISU YUSUF ALI P’hD Cigaba daga makon da ya gabata Gabatarwa Kamar yadda muka faɗa a baya cewa “ritaya wani mataki ne na rayuwa da kowane ma'aikaci zai iya fuskanta idan Allah Ya ba shi tsawon rai. A mafi yawan lokuta, mutane suna shiryawa ne domin samun aiki, samun albashi da gina iyali, amma ba sa bai wa rayuwa bayan ritaya muhimmancin da ta dace. Wannan rashin shiri kan haifar da matsalolin tattalin arziki, damuwa ta tunani, matsalolin lafiya da kuma rashin walwala”. Masana ilimin zamantakewa da tattalin arziki sun nuna cewa shiryawa tun kafin ritaya yana taimakawa…
Read More
IPAC ta yi jimamin ƙaruwar matsalar tsaro a Zamfara

IPAC ta yi jimamin ƙaruwar matsalar tsaro a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar gammayyar jam’iyyun siyasa a Najeriya, reshen Jihar Zamfara IPAC, ta bayyana babban damuwa kan taɓarɓarewar tsaro, halin da tattalin arziki da zamantakewa da al'ummar jihar suka tsinci kansu, da kuma yadda mulki ke tafiya a jihar, IPAC ta buƙaci Gwamna Dauda Lawal da Gwamnatin Tarayya su ɗauki mataki cikin gaggawa. A wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar ta da ke Gusau a yau Talata, Shugaban IPAC na jihar, Hon. Sulaiman Salisu, ya ce sun fitar da wannan matsaya ne bayan taron gaggawa da suka yi tare da shawarwari da shugabannin jam’iyyu,…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin tagwayen hanya a Katsina

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin tagwayen hanya a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina ya ƙaddamar da aikin gina tagwayen hanya mai tsawon kilomita uku a garin Mashi, ƙaramar hukumar Mashi. Aikin da zai laƙume Naira biliyan 4.5, kamfanin Mothercat za ta gudanar da aikin ƙarkashin sa ido na ma'aikatar ayyuka da gidaje. A jawabin sa Gwamna Raɗɗa ya bayyana kasuwar Mashi a mafi girma a faɗin Jihar da ya ce idan an kammala aikin tagwayen hanyar zai taimaka wajen safarar kayan masarufi ba ma a cikin Jihar ba har zuwa wasu jihohin kudu na ƙasar. Haka kuma tagwayen hanyar za ta taimaka wajen bunƙasa tattalin…
Read More
Dakta Bashir Ruwan Godiya ya zama shugaban JIBWIS a Katsina

Dakta Bashir Ruwan Godiya ya zama shugaban JIBWIS a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Kungiyar Izalatul bidi'a wa iƙamatul sunnah reshen Jihar Katsina ta naɗa Dr Bashir Ruwan Godiya a matsayin sabon darakta janaral. Naɗin ya zo ne a matsayin wani muhimmin ci gaba a jagorancin ƙungiyar a faɗin jihar. Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya Malami ne a sashen nazarin aikin jarida na kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina Polytechnic. Ya kuma riƙe muƙamin mai ba gwamna shawara kan Ilimi mai zurfi a Jihar lokacin mulkin tsohon gwamna Rt Hon Aminu Bello Masari. Tuni ƙungiyar ta ba sabon daraktan janaral takardar kama aiki.
Read More
Ƙungiya kare Pantami ta ce zarge-zarge da ake masa ba su da hujja

Ƙungiya kare Pantami ta ce zarge-zarge da ake masa ba su da hujja

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Wata ƙungiya mai suna Coalition of Northeast Movement for Gombe ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, kan zargin mallakar wasu kadarori a Abuja ta hanyar da ba ta dace ba. Ƙungiyar ta bayyana cewa zarge-zargen ba su da hujjoji, kuma tana ganin an yi su ne da manufar ɓata sunan tsohon ministan. A cikin wata sanarwa da kakakinta, Kwamared Tasiu Pantami, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce tana mayar da martani ne kan rahotannin da ke cewa wata ƙungiya…
Read More
Koya wa matasa kamun kifi

Koya wa matasa kamun kifi

A ƙasar mu Nijeriya, musamman yankin Arewa, zaman kashe wando da matasa ke yi na ci wa gwamnati da duk wani mai kishin cigaban matasa tuwo a ƙwarya. Mun wayi gari mafi yawan matasanmu basu da ayyukan yi. Yayin da wasu da dama sun gama karatun su na digiri a jami'o'i a fannoni daban-daban amma babu aikin yi.  Sai dai a maimakon waɗannan matasa su nemi ananan sana'o'i da za su yi, sai dai ka ga mafi yawan su sun raina ƙananan sana'o'i da ayyukansu, suna ganin in ba aikin gwamnati da za a biya su kuɗaɗe masu yawa ba,…
Read More