ukarofi

12504 Posts
An ƙirƙiro masarautun iyayen ƙasa biyu a Kebbi

An ƙirƙiro masarautun iyayen ƙasa biyu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Gwamantin jihar Kebbi ta amince da ƙirƙiro sababbin sarautun iyayen ƙasa biyu daga ƙaramar hukumar Argungu a cikin yankin masarautar Sarkin Kabin Argungu. Sanarawar tana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu Honarabul Garba Umar Dutsinmari ranar Laraba ɗin nan. Takardar ta ce ƙirƙiro masarautun iyayen ƙasar Gwazange da Yamman ya biyo bayan yanke shawarar akwai buƙatar ƙarin sarautun iyayen ƙasa a cikin ƙwaryar garin Argungu, ƙaramar hukumar mulki ta Argungu ta kuma amince da haka inda aka ɗaga darajar hakimin anguwar Gwazange Muhammadu Ibrahim zuwa…
Read More
An yaba wa Bola Tinubu kan ƙarin albashi da ya yi wa sojoji

An yaba wa Bola Tinubu kan ƙarin albashi da ya yi wa sojoji

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban kwamintin sojoji a Majalisar Dattijai Sanata Abdul'aziz Musa yar'adua ya yaba wa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan ƙarin albashi da yayi wa sojoji daga naira dubu 100 zuwa dubu 180. A hira da wata kafar sadarwa national update.ng a Abuja, Sanata Abdul'aziz yar'adua ya bayyana wannan ƙarin albashi a matsayin wani jari a harkan tsaron Najeriya. Sanatan ya ce sabon tsarin albashin da zai fara aiki a wata mai zuwa , "Sojoji 25000 za su amfana da shirin wanda haka ya nuna cikakken goyon baya na gwamnatin Najeriya ga sojojin da ke sadaukar da…
Read More
Komai na mace yana da iyaka – Na’ima Daƙayyawa

Komai na mace yana da iyaka – Na’ima Daƙayyawa

“Babu wani abu da nake yi da nake so da ya wuce karatu da rubutu” Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Marubuciya Na’ima Sulaiman Daƙayyawa ba ɓoyayyiya ba ce tsakanin matasan marubutan Hausa a Jihar Jigawa. Ta fito ne daga ƙaramar Hukumar Kaugama. Tana da gogewa a harshen Larabci da Hausa, inda yanzu haka take karatun digirinta na biyu a Jami'ar Sule Lamiɗo dake Kafin Hausa. Marubuciya ce da ta bambanta da sauran marubutan adabi, saboda ita ta fi mayar da hankali ne kan muhimman abubuwa na tarihi ko al'adu. Akasari rubuce-rubucen da ta yi sun shafi zamantankewar al'umma ne da tarihinsu.…
Read More
Sautin Shehu ya taka inda ƙafarsa ba ta taka ba!

Sautin Shehu ya taka inda ƙafarsa ba ta taka ba!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Sautin Musulunci ya taimaki Shehu Mujaddadi ya kafa daula ba gidan rediyo, talaibijin ko soshiyal midiya ba. Shehu ba ya riƙe takobi ko mashi amma kullum hannunsa rike ya ke da alƙalami da tawada don yaɗa ilimi Idan mu ka duba rayuwar Shehu Mujaddadi daga 1754-1817 ba kafafe na sadarwa ko ɗaya balle a je ga maganar wayar tarho don sai bayan shekara kimanin 70 bayan rasuwar Shehu a shekarun 1880’s a ka ma fara aiki da sadarwar TELEGRAPH a Nijeriya da kan fidda saƙo na layi 100 a wasiƙance kuma har 1920 da ƙaddamar da…
Read More
Kwamishinan Gombe ya gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi kan gaskiya da riƙon amana

Kwamishinan Gombe ya gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi kan gaskiya da riƙon amana

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Kwamishinan ƙananan hukumomi da raya al'umma na Jihar Gombe, Sani Ahmed Haruna, ya buƙaci sabbin shugabannin ƙananan hukumomi da na cibiyoyin raya ƙananan hukumomi (LCDAs) su gudanar da ayyukansu bisa gaskiya, riƙon amana da kuma kula da dukiyar jama'a yadda ya kamata. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron farko na kwamitin raba kuɗaɗen ƙananan hukumomi (JAAC) tare da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Gombe. A cewarsa, al'ummar jihar sun ɗora wa shugabannin alhakin kawo ci gaba a matakin ƙasa, don haka ya buƙace su su tabbatar da amincewar da aka ba su…
Read More
Gwamna Sule ya naɗa sabbin kwamishinoni a Nasarawa

Gwamna Sule ya naɗa sabbin kwamishinoni a Nasarawa

-Majalisar dokoki ta shirya tantance su ranar Juma’a Daga JOHN D. WADA a Lafiya Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa sabbin kamishinoni takwas a matsayin wani mataki na ƙarfafa gwamnatinsa da inganta yadda ake gudanar da ayyuka bayan ya sallami wasu kwamishinonin nasa kwanan nan. Shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa Rt. Hon. Danladi Jatau ne ya sanar da hakan a lokacin wani zama na musamman da majalisar tayi a ranar Laraba, inda ya bayyana sunayen waɗanda aka naɗa a yayin da yake karanta wasiƙa daga gwamnan a zaman. Kamar yadda kakakin majalisar dokokin ya bayyana waɗanda gwamnan ya naɗa…
Read More
Shugaban NASEPA ya nemi ƙarin ma’aikata tare da yabon Gwamna Sule

Shugaban NASEPA ya nemi ƙarin ma’aikata tare da yabon Gwamna Sule

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Babban janar manaja na hukumar kula da tsabtace muhalli ta jihar Nasarawa da ake kira NASEPA Iliya Yusuf Adeka ya yi kira na musamman ga gwamnatin jihar da ta ɗauki ƙarin ma’aikata domin taimaka wa hukumar wajen magance yawan aikin da ke gabanta. Iliya Yusuf Adeka ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar. Adeka ya kuma  yaba wa gwamna Abdullahi Sule bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar ta hanyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta jihar akai-akai kawo yanzu. Ya ƙara da cewa hukumar…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya rantsar da sabbin manyan sakatarori

Gwamna Raɗɗa ya rantsar da sabbin manyan sakatarori

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya rantsar da sabbin manyan sakatarori (Permanent Secretaries) guda huɗu da suka haɗa da Malam Abdu Usman, Dakta Sani Suleiman, Dakta Shamsuddeen Yahaya Suleiman, da Dakta Hussaini Hamisu Yanduna. Da yake jawabi bayan rantsarwar Gwamna Raɗɗa ya ce wannan muƙamin nasu ya tabbata ne bisa cancanta, ƙwarewa da jajircewa, ba tare da la’akari da alaƙa ko sanayya ba. Ya buƙace su da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, riƙon amana da adalci domin inganta ayyukan gwamnati da hidima ga al’ummar jihar. Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta raba Naira biliyan huɗu ga gundumomi 361

Gwamnatin Katsina za ta raba Naira biliyan huɗu ga gundumomi 361

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya amince da fitar da Naira biliyan huɗu domin aiwatar da kashi na biyu na shirin cigaban Amal’umma (CDP) a dukkan gundumomi 361 na jihar, inda kowace gunduma za ta karɓi Naira miliyan 10 domin gudanar da ayyukan da al’umma suka fi buƙata. A sanarwar bayan taron Majalisar zartaswa da jami'in hulɗa da jama'a na gwamna, Muhammadu Kaula ya sanya wa hannu, majalisar zartarwa ta Jiha ta amince da:bayar da kuɗin haɗin gwiwa na shirin Nigeria for Women Project domin ƙarfafa tattalin arzikin mata. Majalisar ta amince da…
Read More
HISBA a Katsina ta hana jami’an ta shiga otel ba tare da takardar kotu ba

HISBA a Katsina ta hana jami’an ta shiga otel ba tare da takardar kotu ba

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar Hisba ta jihar Katsina ta umarci dukkanin jami'ai da kwamandoji na ƙananan hukumomi a kan su rika karɓo izinin kotu ko kuwa waranti, kafin shiga ɗakunan masaukan baƙi (hotels) ko kuma gidajen mutane don gudanar da aiki. Umurnin dai na ƙunshe ne da rattaba hannun babban kwamandan hukumar, sannan kuma an cimma matsayar hakan ne a lokacin taron yau da kullum na hukumar da ya gudana. A cikin wannan umurni dai, babu wani jami'i ko kwamanda da a ka amince ma wa ya shiga cikin wani masaukin baƙi ko gidajen mutane ba tare da…
Read More