ukarofi

12504 Posts
Cikakken bayanin sabon albashin da sojojin Nijeriya za su riƙa karɓa

Cikakken bayanin sabon albashin da sojojin Nijeriya za su riƙa karɓa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sabon tsarin albashi ga jami’an rundunonin sojin Nijeriya, inda aka ƙara musu albashi da tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin ɗari, a wani mataki da Gwamnatin Tarayya ta ce zai inganta walwala da ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro. Sabon tsarin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumba, kuma ana sa ran sama da jami’an soji 250,000 za su amfana da wannan ƙarin. Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ne ya sanar da amincewar cikin wata sanarwa da…
Read More
Majalisar Dokokin Katsina ta nemi daidaita kuɗin makarantu masu zaman kansu

Majalisar Dokokin Katsina ta nemi daidaita kuɗin makarantu masu zaman kansu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina  Majalisar Dokoki a Jihar Katsina ta yi kira ga ɓangaren zartarwa na gwamnati da ta samar da tsarin da zai daidaita yadda makarantu masu zaman kansu da na al'umma ke gudanar da ayyukansu, musamman kan yawan kuɗin makaranta da kuma tsarin gudanarwarsu. Hakan ya biyo bayan   kudiri da ɗan majalisa mai wakiltar Katsina, Alhaji Aliyu Abubakar Albaba, ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan yawan ƙarin kuɗin makaranta ba tare da ingantaccen tsari na sa ido ba. A zaman Majalisar da Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, ya jagoranta, an kuma buƙaci gwamnatin jihar…
Read More
Ana naɗa Jamilu Lamir a matsayin Sarkin Maganin Fagge a Kano

Ana naɗa Jamilu Lamir a matsayin Sarkin Maganin Fagge a Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Sarkin Maganin Gargajiya na Jihar Kano, Dakta Rabilu Muhammad, ya naɗa Alhaji Jamilu Lamir Jibrin a matsayin sabon Sarkin Maganin ƙaramar Hukumar Fagge, bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi Dakta Lamir. An gudanar da bikin naɗin ne a fadar Sarkin Maganin da ke Kano a ranar Laraba, inda Sarkin ya shawarci sabon Sarkin Maganin da ya yi koyi da kyawawan halayen mahaifinsa na ƙaunar al'umma, karamci da biyayya ga masarautar maganin gargajiya ta Jihar Kano. Da yake jawabi a madadin iyalan marigayin, Alhaji Mukhtar Lamir ya gode wa Sarkin Maganin Kano da majalisarsa bisa wannan naɗi. Ya…
Read More
Gwamnatin Kano ta dakatar da shirin rigakafin zazzaɓin cizon sauro

Gwamnatin Kano ta dakatar da shirin rigakafin zazzaɓin cizon sauro

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da dukkan ayyukan Shirin Rigakafin Zazzaɓin Cizon Sauro na Lokacin Damina (SMC) a faɗin jihar, tare da kafa wani babban kwamitin bincike domin tantance yadda aka gudanar da shirin. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami'in Hulɗa da Jama'a na Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Nabilusi Abubakar K/Na'isa, ya fitar a ranar Alhamis. A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan kafa kwamitin da aka ɗora wa alhakin gudanar da cikakken bincike kan yadda aka tsara shirin, yadda aka rarraba rigakafin da kuma yadda aka aiwatar da shi, domin tabbatar…
Read More
Zan fice daga APC idan Tinubu ya ci mutuncin limaman Cocin Katolika — Orji Kalu

Zan fice daga APC idan Tinubu ya ci mutuncin limaman Cocin Katolika — Orji Kalu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Gwamnan Jihar Abia, kuma Sanatan da ke wakiltar Mazaɓar Abia ta Arewa, Orji Kalu, ya bayyana cewa zai yi murabus daga jam'iyyar APC matuaar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taɓa kimar limaman Cocin Katolika. Sanatan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya kare Shugaba Tinubu daga zarge-zargen cewa ya ci mutuncin Cocin Katolika bayan musayar kalamai da aka samu tsakanin Fadar Shugaban ƙasa da shugabannin cocin kan halin da ƙasa ke ciki. Orji Kalu ya ce,…
Read More
Sarkin Musulmi ya buƙaci a binciki zargin kashe Kanal Abdulkarim

Sarkin Musulmi ya buƙaci a binciki zargin kashe Kanal Abdulkarim

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya buƙaci gwamnatin tarayya da rundunar sojojin Nijeriya su gudanar da cikakken bincike kan zargin kisan jami'in soji, Kanal Abdur-Razaƙ AbdulKarim Ode, tare da tabbatar da cewa an gano waɗanda ke da hannu a lamarin kuma an hukunta su bisa doka. A cikin wata sanarwa da Yarima Bashir Adefaka ya fitar a madadin tawagar yaɗa labaran Sarkin Musulmi, Sarkin ya bayyana damuwarsa kan yadda aka ce an harbe Kanal Ode a gidansa da ke Abuja, yana mai cewa wajibi ne a gano haƙiƙanin abin da ya faru. Sarkin…
Read More
Sanata Ogoshi ya bayyana dalilinsa na barin jam’iyyar ADC

Sanata Ogoshi ya bayyana dalilinsa na barin jam’iyyar ADC

Daga JOHN D. WADA a Lafiya  Sanata Ogoshi Onawo mai wakiltar mazaɓar sanatan Nasarawa ta Kudu a majalisar dattawa ya bayyana cewa ya bar Jam’iyyar African Democratic Congress ADC ne saboda zaɓen fidda gwamnan jam’iyyar bai kasance cikin gaskiya da adalci ba. Onawo wanda a kwanan nan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Allied People’s Movement APM bayan ya sha kaye a zaɓen fidda gwamin ADC ɗin a hannun James Angbazo a kujerar gwamnan jihar na 2027 mai zuwa yace da an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci da zai karɓi sakamakon. Da yake tattaunawa da manema labarai a gidansa…
Read More
Alhaji Abubakar Alhaji (1937–2026): Dan kishin ƙasa da ya yi wa Nijeriya hidima cikin natsuwa da ƙwarewa 

Alhaji Abubakar Alhaji (1937–2026): Dan kishin ƙasa da ya yi wa Nijeriya hidima cikin natsuwa da ƙwarewa 

A makon jiya, Nijeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun jami'an gwamnati da suka yi wa ƙasa hidima cikin gaskiya da riƙon amana, wato Alhaji Abubakar Alhaji (Sardaunan Sakkwato). Rasuwar wannan dattijo ɗan kishin ƙasa, tsohon Ministan Kuɗi, kuma tsohon Jakaden Nijeriya a Birtaniya, bankwana ce da wani mutum wanda rayuwar sa ta kasance abar koyi ta ladabi, kishin ƙasa, tawali'u da sadaukar da kai wajen bautar ƙasa. Alhaji Abubakar Alhaji ya rasu bayan ya shafe makonni yana fama da rashin lafiya. Da farko an kwantar da shi a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Usmanu ɗanfodiyo da ke Sakkwato, kafin…
Read More
Rufe asusun gwamnatin Osun: Tinubu ya kare dimukraɗiyya a Osun

Rufe asusun gwamnatin Osun: Tinubu ya kare dimukraɗiyya a Osun

*Matakin da kotu da EFCC suka ɗauka gabanin zaɓe ya kunyata ni, cewarsa Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa, ba komai ake aikatawa a Gwamnatin Tarayya da shi shugaban yake da masaniya kafin yi ba. Don haka ya umarci Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Ta'annati (EFCC) da ta garzaya kotu, domin janye umarnin da ya bai wa hukumar damar rufe asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun tare da dakatar da duk wani matakin shari'a da ta ɗauka kan lamarin. A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙasar ya sanya wa hannu da kansa…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Augie ya ƙaddamar da yasar magudanun ruwa

Shugaban ƙaramar hukumar Augie ya ƙaddamar da yasar magudanun ruwa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie ya ƙaddamar da aikin yasar magudanun ruwa a manyan garururwan da ke ƙaramar hukumar. Da ya ke jawabi yayin ƙaddamar da aikin a garin Augie, Honarabul Yahaya Muhammed ya ce wannan yana daga cikin ayyukan da ya kamata a fuskanta saboda kaucewa barazanar ambaliya saboda masana sun yi hasashen akwai yiyuwar ambaliya a wannan daminar. Ya ƙara da cewa ko ba komai dai yana da kyau mutane su tsaftace muhallin su saboda gudun kamuwa da cututtuka musamman a yanayin damina. Ya nemi magidanta da su…
Read More