ukarofi

12504 Posts
Tinubu ya umarci jami’an tsaro su farauto maharan da suka kashe mutum 30 a Kaduna

Tinubu ya umarci jami’an tsaro su farauto maharan da suka kashe mutum 30 a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai ƙauyen Naridon da ke ƙaramar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 30, tare da umartar jami’an tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki. Harin, wanda ya faru da safiyar ranar Litinin, ya jawo suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na cikin gida da na ƙasashen waje, yayin da har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin. A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga,…
Read More
ADC ta buƙaci Tinubu ya mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci maimakon ‘yan adawa

ADC ta buƙaci Tinubu ya mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci maimakon ‘yan adawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankali wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar nan, maimakon shiga rigingimun siyasa da jam’iyyun adawa. Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaranta na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, inda ta mayar da martani kan kalaman da Shugaba Tinubu ya yi na cewa a shirye yake ya yi “faɗan ƙarshe” a fagen siyasa. A cewar ADC, bai kamata shugaban ƙasa ya fi mayar da hankali kan fafatawa da ‘yan…
Read More
DSS ta kama wani babban jagoran Ansaru da ake zargin yana da alaƙa da Boko Haram — Rahoto

DSS ta kama wani babban jagoran Ansaru da ake zargin yana da alaƙa da Boko Haram — Rahoto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS) ta kama Khalid Albarnawi, wani fitaccen jagoran ƙungiyar Ansaru da ake zargin ta sake ƙulla alaƙa da Boko Haram. A cewar rahoton, an kama Albarnawi ne a Lokoja, Jihar Kogi, kafin daga bisani a mayar da shi wani wuri a ranar Juma’a. Rahoton ya samo asali ne daga wani masani kan harkokin Boko Haram, Ahmad Salkida, wanda ya wallafa bayanin a shafinsa na ɗ. Rahotanni sun bayyana Albarnawi a matsayin ɗaya daga cikin manyan shugabannin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya,…
Read More
Muna siyasa domin ci gaban al’umma, ba don son kai ba – Baffan Matasa

Muna siyasa domin ci gaban al’umma, ba don son kai ba – Baffan Matasa

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Dan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar Hukumar Rano a yaryashin jam'iyyar NDC, Hon. Isa Ahmed Tijjani, wanda aka fi sani da Baffan Matasa, ya bayyana cewa babban dalilinsa na neman kujerar majalisa shi ne tabbatar da ci gaba mai ɗorewa ga al'ummar mazaɓarsa, ba don biyan wata buƙata ta kansa ba. Hon. Isa Ahmed Tijjani ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a lokacin bikin yaye ɗaliban Makarantar Sakandaren 'Yan Sanda da ke Dawakin Kudu. Ya ce idan Allah Ya ba su nasara a zaɓen 2027, za…
Read More
Police Secondary School Dawakin Kudu ta yaye ɗalibai 184 karo na farko

Police Secondary School Dawakin Kudu ta yaye ɗalibai 184 karo na farko

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Makarantar Police Secondary School (PSS) da ke Dawakin Kudu a Jihar Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai 184 da suka kammala karatunsu, wanda shi ne karo na farko tun bayan kafuwar makarantar a shekarar 2023. Da yake jawabi a wajen taron, Kwamandan makarantar, SP Mukhtar Haruna Hadeja, ya bayyana cewa tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa, Hon. Mustapha Bala Dawaki, ne ya samar da makarantar tare da miya ta ga Gwamnatin Tarayya da Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya. SP Hadeja ya bayyana farin cikinsa da samun damar jagorantar makarantar a…
Read More
Ayyukan raya ƙasa a Arewa: Tinubu na cika alƙawari

Ayyukan raya ƙasa a Arewa: Tinubu na cika alƙawari

A cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar da manyan shirye-shiryen raya ƙasa da suka shafi sassa daban-daban na Nijeriya, musamman fannin tsaro, ababen more rayuwa, noma, ilimi da makamashi. Arewacin ƙasar na daga cikin yankunan da ake aiwatar da wasu daga cikin waɗannan ayyuka. A fannin tsaro, gwamnati ta amince da ƙirƙirar sabbin Rukunonin Sojoji (Divisions), tare da sake tsara yankunan aiki domin ƙarfafa yaƙi da ta'addanci, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka. Haka kuma an amince da ƙarin kayan aiki da gina sabbin barikoki domin inganta ayyukan jami'an tsaro. A ɓangaren…
Read More
Yilwatda ne Gwarzon Blueprint na 2025

Yilwatda ne Gwarzon Blueprint na 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin jaridun Blueprint da Mahana ya zaɓi Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a matsayin Gwarzon Shekara ta 2025 bisa irin jagorancinsa, gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa dimokuraɗiyya da kuma ƙoƙarinsa na ƙarfafa cibiyoyin siyasa a Nijeriya. Lambar yabon, wadda ita ce mafi girma da kamfanin ke bayarwa a duk shekara, na karrama mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasa ta fuskar shugabanci, hidimar jama'a da kuma ayyukan raya ƙasa a shekarar da ake dubawa. Daraktan Gudanarwa na Kamfanin Jaridun Blueprint, Salisu Umar, ya ce an zaɓi Farfesa Yilwatda…
Read More
Amurka za ta dakatar da ayyukan bada biza a Abuja daga watan Agusta

Amurka za ta dakatar da ayyukan bada biza a Abuja daga watan Agusta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa daga ranar 1 ga Agustan 2026, za ta dakatar da ayyukan karɓa da sarrafa buƙatun bizar yau da kullum a Ofishin Jakadancinta da ke Abuja, tare da wasu ofisoshin jakadanci guda 24 da ke faɗin nahiyar Afirka. A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, matakin na daga cikin wani sabon shiri na sake fasalin ayyukan ofisoshin jakadancinta a ƙasashen waje, domin tattara ayyukan sarrafa biza a wasu cibiyoyi na yankuna. Hakan, a cewarta, zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron ƙasa, rage kuɗaɗen gudanarwa, tare da tabbatar da daidaito wajen tantance masu neman…
Read More
Mun gaza tantance takardu kafin amincewa da hukumar bogi – Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Mun gaza tantance takardu kafin amincewa da hukumar bogi – Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Esther Walson-Jack, ta amince cewa ofishinta bai gudanar da cikakken bincike da tantance takardun da aka gabatar masa ba kafin ya amince da tsarin ma’aikata da kuma izinin ɗaukar ma’aikata na wata hukuma da ake zargin ta bogi ce mai suna Majalisar Shugaban ƙasa kan Bunƙasa Zuba Jarin ƙasashen Waje (PFIPC). Walson-Jack ta bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da take ba da shaida a gaban Kwamitin Musamman na Majalisar Wakilai, wanda ke binciken rikicin da ya dabaibaye PFIPC da kuma ware mata kuɗaɗe har Naira biliyan 1.3 a cikin kasafin kuɗin…
Read More
‘Yan sanda sun kama wani dillalin miyagun ƙwayoyi a Katsina

‘Yan sanda sun kama wani dillalin miyagun ƙwayoyi a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar 'yan sanda sun kama Muhammad Lawal ɗan shekara 30 da haihuwa ɗauke da miyagun ƙwayoyi 1220 a ƙaramar hukumar Rimi. 'Yan sanda da ke ƙarkashin ofishin garin Rimi sun kama wannan matashi ne a hanyar Tsagero bayan samun bayanan sirri a kan matashin da ake zargi. A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa 'yan sandan a yayin da suke gudanar da bincike,sun gano yana ɗauke da ƙwayar Exol 5 guda 1000 da D5 guda 200 sai fakiti 10 na Pregablin da kuma fakiti 10 na Tramadol…
Read More