ukarofi

12504 Posts
Hisbah ta haramta DJ da haɗa maza da mata a bukukuwa a Sakkwato

Hisbah ta haramta DJ da haɗa maza da mata a bukukuwa a Sakkwato

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato ta sanar da haramta wasu al'adu da ake gudanarwa a bukukuwan aure da sauran tarukan jama'a, ciki har da amfani da DJ, bikin gabatar da kayan neman aure da aka fi sani da 'Na Gani Ina So', haɗa maza da mata wajen nishaɗi, da kuma yawan kashe kuɗi wajen kayan lefe, tana mai cewa waɗannan abubuwa ba su da tushe a koyarwar Musulunci. Hukumar ta kuma hana amfani da waƙoƙin Wazigidi a bukukuwa, ɗaura lasifika a kan baburan adaidaita sahu (Keke Napep), zaman mata kusa da direbobin adaidaita sahu, salon aski…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Sanata Rufa’i Hanga ya fice daga NDC ya Koma APC

Da ɗumi-ɗumi: Sanata Rufa’i Hanga ya fice daga NDC ya Koma APC

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Sanatan Kano ta tsakiya Alhaji Rufa'i Sani Hanga, ya fice daga jam'iyyarsa ta NDC Kwankwasiyya, ya koma APC. Hanga ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da Nasir Salisu Zango a yau Alhamis, inda yace ya ɗauki matakin ne bisa raɗin kansa da kuma nema wa kansa mutunci da kima a siyasance. Wannan na zuwa ne tun bayan rasa takarar Sanatan da yake kai, da kuma aiwatar da wasu sauye- sauye a jam'iyyar ba tare da saninsa ba. Ko a makon da ya gabata ne ma dai an hangi Sanata Hanga da Shugaban ƙasa Bola…
Read More
Mutane huɗu sun mutu a wani artabu a Kebbi

Mutane huɗu sun mutu a wani artabu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Aƙalla mutane huɗu ne suka mutu yayin da soja ɗaya ya ɓace a wani hari na ranar Larabar nan da ƴan bindiga suka kai a garin Tudun Bicci da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu da ke jihar Kebbi. Shugaban ƙaramar hukumar mulki Danko/Wasagu Honarabul Hussain Aliyu Bena ya bayyanawa waƙilin jaridar Blueprint Manhaja ta wayar tarho da cewa waɗanda suka rasu sun haɗa da jami'an gandun daji biyu da waɗansu farar hula biyu sannan kuma soja ɗaya ya ɓace yayin artabun na ranar Laraba.A ɗaya ɓangaren kuma ya bayyana cewa da yawa daga cikin maharan sun…
Read More
‘Yan bindiga sun yi yunƙurin sace wani alƙali ana tsaka da zaman kotu a Katsina

‘Yan bindiga sun yi yunƙurin sace wani alƙali ana tsaka da zaman kotu a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Alƙalin kotun shari'ar musulunci, Mohammad Mukhtar ya tsallake rijiya da baya bayan wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne suka yi yunƙurin sace shi ko kuma kashe shi gaba ɗaya. 'Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari a garin Gwarjo da ke ƙaramar hukumar Matazu inda suka yi dirar mikiya a wata kotun Shari'ar Musulunci da rana tsaka a jiya Laraba, a dai dai lokacin da alƙalin da sauran ma'aikatan kotu ke gudanar da aikinsu. Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun kutsa cikin harabar kotun a yunƙurin da suka yi na…
Read More
‘Yargiwa ya tallafa wa marayu da manoma

‘Yargiwa ya tallafa wa marayu da manoma

Daga JAMIL GULMA a Kebbi A cikin shirin sa na tallafi ga marayu da manoma masu ƙaramin ƙarfi Honarabul Sani Yakubu Ƴargiwa ya raba abinci da takin zamani da motocin noma.Honarabul Sani Yakubu ya bayyana cewa waɗannan kayan dama ba nasa ba ne na al'umma ne saboda haka ya karɓo kuma ya isar da waƙilci kamar yadda aka tura shi. Ya ƙara da cewa wannan ba zai isa ga kowa ba amma dai mutane kowa ya yi haƙuri da abinda ya samu saboda duk wanda ke bibiyar harkokin majalisun tarayya yana sane da cewa tun kasafin shekarar 2025 da ta…
Read More
‘Yan bindiga sun yi yunƙurin sace wani alƙali ana tsaka da zaman kotu a Katsina

‘Yan bindiga sun yi yunƙurin sace wani alƙali ana tsaka da zaman kotu a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Alƙalin kotun shari'ar musulunci, Mohammad Mukhtar ya tsallake rijiya da baya bayan wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne suka yi yunƙurin sace shi ko kuma kashe shi gaba ɗaya. 'Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari a garin Gwarjo da ke ƙaramar hukumar Matazu inda suka yi dirar mikiya a wata kotun Shari'ar Musulunci da rana tsaka a jiya Laraba, a dai dai lokacin da alƙalin da sauran ma'aikatan kotu ke gudanar da aikinsu. Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun kutsa cikin harabar kotun a yunƙurin da suka yi na…
Read More
Tafiya da kowa a gwamnati har yanzu na fama da ƙalubale – Halima Mahdi

Tafiya da kowa a gwamnati har yanzu na fama da ƙalubale – Halima Mahdi

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Wata mai rajin tabbatar da daidaito da tafiya da kowa a harkokin shugabanci, Hajiya Halima Mahdi, ta ce duk da yawaitar kira da wayar da kai kan muhimmancin tafiya da kowa (inclusiveness), har yanzu mata, matasa da masu nakasa ba sa samun isasshen wakilci a gwamnati da wuraren yanke manyan hukunci. Halima Mahdi, ta bayyana haka ne a wata hira, inda ta ce ana yawan jin gwamnati da hukumomi suna magana kan tafiya da kowa, amma hakan bai bayyana sosai ba a naɗe-naɗen muƙamai, tsara manufofi da aiwatar da shirye-shiryen gwamnati. Ta ce ainihin manufar…
Read More
Tinubu ya amince da biliyan 46 domin gyaran filin jirgin saman Kano – Iliyasu Kwankwaso

Tinubu ya amince da biliyan 46 domin gyaran filin jirgin saman Kano – Iliyasu Kwankwaso

Yayin da gwamnatin tarayya ta amince da kashe naira biliyan 46 domin gyarawa da sake gina titin sauka da tashi na biyu a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano, an shawarci ’yan Arewa su riƙa nuna godiya ga kyawawan ayyukan shugaban ƙasa Bola Tinubu, musamman ganin cewa wannan ƙoƙari ya nuna gaskiya da rashin son kai ga yankin. Yayin da yake mayar da martani kan amincewar aikin, daraktan kuɗi na hukumar kula da Kogin Hadejia-Jama’are, Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce:“Ina sa ran mutanena, ba tare da la’akari da jam’iyya ba, za su gode wa…
Read More
Adabi ba zai mutu ba sai babu wanda ya rage a duniya – Yusuf Gumel

Adabi ba zai mutu ba sai babu wanda ya rage a duniya – Yusuf Gumel

“Rubutu mai inganci ne tushen ci gaban marubuci” Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Wani salo da ya bambanta marubuta maza da mata shine, batutuwan da kowanne ɓangare ya fi mayar da hankali akansa, don faɗakar da al'umma. A yayin da a ɗaya ɓangaren akasarin marubuta mata ke rubutu kan batutuwan da suka shafi zamantakewar aure da rayuwa, maza sun fi baje basirarsu ne ta ɓangaren jarumta da almara ko abubuwa masu tsoratarwa, da kuma a wani batutuwan da suka shafi sarauta da siyasa. Ko da yake kowanne daga cikin waɗannan ɓangarori yana iya ninkaya a cikin salon ɗaya ɓangaren. Wani marubuci…
Read More
‘Yan Sanda sun daƙile yunƙurin satar shanu a Katsina

‘Yan Sanda sun daƙile yunƙurin satar shanu a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta sami nasarar daƙile wani yunƙurin satar shanu tare da ƙwato dabbobi 76 da aka sace, waɗanda suka haɗa da shanu 20 da tumaki 56, a wasu ƙauyuka biyu da ke ƙaramar hukumar Dutsinma. A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar ya ce lamarin ya faru bayan da wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai suka kai hari ƙauyukan Yarmaje da Alasawa tare da sace dabbobi da dama. Sanarwar ta bayyana cewa, bayan samun kiran gaggawa, jami’an ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da jami’an…
Read More