ukarofi

12504 Posts
Mutune 14,000 suka amfana da aikin ido na gidauniyar Mangal a Katsina

Mutune 14,000 suka amfana da aikin ido na gidauniyar Mangal a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gidauniyar Dahiru Barau Mangal ta yi wa mutane 14,000 aikin udo tun bayan fara gudanar da aikin a Jihar Katsina. Ɗaya daga cikin 'yan kwamitin amintattu na gidauniyar, Alhaji Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan yayin da ake ci gaba da aikin tiyatar ido kyauta ga mutum 600 a asibitin ido (Eye Centre) da ke tsohuwar kasuwa a birnin Katsina. Ya ce gidauniyar ce ta ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya, bayan kammala tantance waɗanda suka amfana, yana mai jaddada cewa ba a karɓar ko sisi daga hannun marasa lafiya. Alhaji Kabir ya bayyana cewa a…
Read More
Kashi 70 na manyan laifukan Kano na da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi – Muhuyi Magaji

Kashi 70 na manyan laifukan Kano na da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi – Muhuyi Magaji

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban kwamitin haɗin gwiwa na yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi na Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa kusan kashi 70 cikin 100 na manyan laifukan da ake aikatawa a jihar suna da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi. Muhuyi Magaji ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Kano, inda ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su mara wa gwamnatin jihar baya wajen wayar da kan al'umma kan illolin shan miyagun ƙwayoyi, fataucin haramtattun ƙwayoyi da kuma ayyukan 'yan daba. Ya ce, bisa ga ƙididdigar rundunar 'yan sandan Jihar Kano,…
Read More
Kwamintin da gwamnatin Katsina ta kafa na tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi ya ci gaba da aiki

Kwamintin da gwamnatin Katsina ta kafa na tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi ya ci gaba da aiki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamintin da gwamnatin Jihar Katsina ta kafa na tantance ma'aikatan ƙananan hukumomi 34 da ke jihar ta fara tantance masu ƙorafe-ƙorafe. Ma'aikata da dama da basu sami tsallake tantancewa ba suka miƙa takardar ƙorafe-ƙorafe wanda yasa gwamna Dikko Raɗɗa ya umarci kwamintin da ya sake duba koken su. Kwamintin ƙarƙashin shugaban mai ba gwamna shawara kan ƙananan hukumomi Alhaji Lawal Rufa'i Safana ya fara da ma'aikatan ƙananan hukumomin Kaita,Batagarawa da Katsina. Kwamintin ya fara da ma'aikata 100 da suka fito da ga waɗannan ƙananan hukumomin inda zai sake duba takardar karatu da na ɗaukar aiki…
Read More
Gwamnatin Abdullahi Sule ta cire wa ‘yan fansho kitse a wuta – Hudu Baba Abdullahi

Gwamnatin Abdullahi Sule ta cire wa ‘yan fansho kitse a wuta – Hudu Baba Abdullahi

Daga JOHN D. WADA a Lafia Shugaban ƙungiyar 'yan fansho na jihar Nasarawa Hudu Baba Abdullahi yace gwamnatin jihar ta Injiniya Abdullahi Sule zuwa yanzu za a iya cewa ta cire wa masu karɓan fansho na jihar kitse a wuta idan aka yi la'akari da makudan kuɗaɗe da gwamnan ke cigaba da amincewa don warware matsalolin 'yan fansho din a jihar baki ɗaya. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa wasu tambayoyi daga 'yan jarida da suka ziyarci ofishin ƙungiyar ta 'yan fansho dake garin Lafia fadar gwamnatin jihar ranar Talata na makon nan. Hudu Baba Abdullahi yace…
Read More
Kwamarade Yahaya Jibrin ya yaba wa Gwamna Sule game da gina sabbin hanyoyi

Kwamarade Yahaya Jibrin ya yaba wa Gwamna Sule game da gina sabbin hanyoyi

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Shugaban ƙungiyar masu babur na ƙasa reshen jihar Nasarawa Kwamarade Yahaya Jibrin yace ƙungiyar ta daɗe tana bada gagaruman gudumawa a fannin tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin jihar don samar da aikin yi da rage zaman banza tsakanin ɗimbin matasan jihar dama ƙasa baki ɗaya zuwa yanzu. Kwamarade Yahaya Jibrin ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishin sa dake tsohon gareji dake Lafia babban birnin jihar a makon da ake ciki. Yace kawo yanzu mambobin ƙungiyar sun kai sama da mutum 3000 wato a garin Lafia kaɗai kenan…
Read More
Shin ko kasan saka takalma marasa kyau na lalata ƙafa?

Shin ko kasan saka takalma marasa kyau na lalata ƙafa?

Daga AISHA ASAS  Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyar mu.  Na san mai karatu zai iya ɗan saka alamar tambaya kan darasin namu, wato kalamar 'takalma mai kyau'. Idan tunaninka ya tafi kan tsari na kyau da ake gani a zahiri ne, to ka dawo baya, hakan zai sa ka fahimci inda darasin namu ya dosa. Takalma masu kyau da muka ambata na magana ne kan takalma masu bada lafiya, ba masu wahalar da ƙafa ba. Akwai takalma da muke wa laƙabi da 'orthopedic shoes' su musamman an gina…
Read More
Yadda cutar damuwa ta iyaye ke shafar ‘ya’yansu 

Yadda cutar damuwa ta iyaye ke shafar ‘ya’yansu 

Daga AISHA ASAS Mai karatu, barkanmu da sake saduwa a shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu tattauna wani muhimmin batu da duk da girman tasirinsa ga rayuwar iyali, ba kasafai ake ba shi kulawar da ta dace ba, musamman a Arewacin Najeriya. Batu ne da ya shafi lafiyar ƙwaƙwalwa, musamman cutar damuwa (anɗiety) da kuma baƙin ciki mai tsanani (depression). A gidaje da dama, akwai matsalolin da ba sa bayyana a ido, amma suna girgiza zaman lafiyar iyali. Cutar damuwa da baƙin ciki na daga cikin irin waɗannan matsaloli. Mutane da yawa na rayuwa da…
Read More
Tarihin Muhammadu Kanta, wanda ya assasa Daular Kabi (II)

Tarihin Muhammadu Kanta, wanda ya assasa Daular Kabi (II)

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Bayan da Muhammadu Kanta ya samu nasarar tabbatar da 'yancin Daular Kabi, ya mayar da hankali wajen faɗaɗa mulkinsa. A cewar masana tarihi, mulkinsa ya bazu zuwa manyan yankuna na ƙasar Hausa da wasu sassan Yammacin Afirka. A gabas, iyakar mulkinsa ta kai har yankin Nguru, a masarautar Borno ta tsohon lokaci. A yamma kuma ya miƙa ikonsa zuwa yankunan da suka yi iyaka da tsohuwar Daular Oyo. A arewa kuwa, ya mamaye yankunan Arewa, Zabarma da wasu sassan da yanzu suke cikin Jamhuriyar Nijar. Haka kuma ya shimfiɗa ikonsa zuwa wasu yankunan da yanzu…
Read More
Kotu ta tsayar da ranar gabatar da hujjoji a shari’ar Shinkafi da Sanatan APC na Zamfara ta Arewa

Kotu ta tsayar da ranar gabatar da hujjoji a shari’ar Shinkafi da Sanatan APC na Zamfara ta Arewa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Babbar Kotun Tarayya da ke a Gusau, Jihar Zamfara, ta tsayar da Talata, 5 ga Agusta, 2026, domin karɓar ƙarshen-hujjojin rubutu a shari’ar da jigo a jam’iyyar APC, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya shigar kan sakamakon zaɓen fidda gwani na Sanatan Zamfara ta Arewa. Lauyan mai shigar da ƙara, Barr. Bello Galadi, ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan zaman kotun na yau Talata a harabar kotun da ke Gusau. A cewar Galadi, an ɗage zaman ne saboda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wadda ita ce ta ɗaya a cikin waɗanda ake…
Read More
SUBEB ta fara horas da malamai 2,500 a Katsina

SUBEB ta fara horas da malamai 2,500 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar ilimin bai ɗaya da makarantun sakandare ta Jihar Katsina ta fara gudanar da shirin horas da malamai da shugabannin makarantu 2,500 a babbar makarantar KCK da ke Katsina, domin ƙara inganta ingancin koyarwa da jagorancin makarantu a faɗin jihar Ana gudanar da horaswar tare da haɗin gwiwar British Council da Education Solutions Ltd, ƙarƙashin shirin Strengthening Teachers' English Proficiency (STEP) da kuma Instructional Leadership Programme, a ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ma'aikatar ilimin firamare da sakandare ta Jihar Katsina, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia. Da yake jawabi a wajen buɗe taron, Hon. Yusuf Sulaiman Jibiya ya bayyana…
Read More