ukarofi

12521 Posts
‘Yan bindiga sun yi yunƙurin sace wani alƙali ana tsaka da zaman kotu a Katsina

‘Yan bindiga sun yi yunƙurin sace wani alƙali ana tsaka da zaman kotu a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Alƙalin kotun shari'ar musulunci, Mohammad Mukhtar ya tsallake rijiya da baya bayan wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne suka yi yunƙurin sace shi ko kuma kashe shi gaba ɗaya. 'Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari a garin Gwarjo da ke ƙaramar hukumar Matazu inda suka yi dirar mikiya a wata kotun Shari'ar Musulunci da rana tsaka a jiya Laraba, a dai dai lokacin da alƙalin da sauran ma'aikatan kotu ke gudanar da aikinsu. Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun kutsa cikin harabar kotun a yunƙurin da suka yi na…
Read More
‘Yargiwa ya tallafa wa marayu da manoma

‘Yargiwa ya tallafa wa marayu da manoma

Daga JAMIL GULMA a Kebbi A cikin shirin sa na tallafi ga marayu da manoma masu ƙaramin ƙarfi Honarabul Sani Yakubu Ƴargiwa ya raba abinci da takin zamani da motocin noma.Honarabul Sani Yakubu ya bayyana cewa waɗannan kayan dama ba nasa ba ne na al'umma ne saboda haka ya karɓo kuma ya isar da waƙilci kamar yadda aka tura shi. Ya ƙara da cewa wannan ba zai isa ga kowa ba amma dai mutane kowa ya yi haƙuri da abinda ya samu saboda duk wanda ke bibiyar harkokin majalisun tarayya yana sane da cewa tun kasafin shekarar 2025 da ta…
Read More
‘Yan bindiga sun yi yunƙurin sace wani alƙali ana tsaka da zaman kotu a Katsina

‘Yan bindiga sun yi yunƙurin sace wani alƙali ana tsaka da zaman kotu a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Alƙalin kotun shari'ar musulunci, Mohammad Mukhtar ya tsallake rijiya da baya bayan wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne suka yi yunƙurin sace shi ko kuma kashe shi gaba ɗaya. 'Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari a garin Gwarjo da ke ƙaramar hukumar Matazu inda suka yi dirar mikiya a wata kotun Shari'ar Musulunci da rana tsaka a jiya Laraba, a dai dai lokacin da alƙalin da sauran ma'aikatan kotu ke gudanar da aikinsu. Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun kutsa cikin harabar kotun a yunƙurin da suka yi na…
Read More
Tafiya da kowa a gwamnati har yanzu na fama da ƙalubale – Halima Mahdi

Tafiya da kowa a gwamnati har yanzu na fama da ƙalubale – Halima Mahdi

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Wata mai rajin tabbatar da daidaito da tafiya da kowa a harkokin shugabanci, Hajiya Halima Mahdi, ta ce duk da yawaitar kira da wayar da kai kan muhimmancin tafiya da kowa (inclusiveness), har yanzu mata, matasa da masu nakasa ba sa samun isasshen wakilci a gwamnati da wuraren yanke manyan hukunci. Halima Mahdi, ta bayyana haka ne a wata hira, inda ta ce ana yawan jin gwamnati da hukumomi suna magana kan tafiya da kowa, amma hakan bai bayyana sosai ba a naɗe-naɗen muƙamai, tsara manufofi da aiwatar da shirye-shiryen gwamnati. Ta ce ainihin manufar…
Read More
Tinubu ya amince da biliyan 46 domin gyaran filin jirgin saman Kano – Iliyasu Kwankwaso

Tinubu ya amince da biliyan 46 domin gyaran filin jirgin saman Kano – Iliyasu Kwankwaso

Yayin da gwamnatin tarayya ta amince da kashe naira biliyan 46 domin gyarawa da sake gina titin sauka da tashi na biyu a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano, an shawarci ’yan Arewa su riƙa nuna godiya ga kyawawan ayyukan shugaban ƙasa Bola Tinubu, musamman ganin cewa wannan ƙoƙari ya nuna gaskiya da rashin son kai ga yankin. Yayin da yake mayar da martani kan amincewar aikin, daraktan kuɗi na hukumar kula da Kogin Hadejia-Jama’are, Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce:“Ina sa ran mutanena, ba tare da la’akari da jam’iyya ba, za su gode wa…
Read More
Adabi ba zai mutu ba sai babu wanda ya rage a duniya – Yusuf Gumel

Adabi ba zai mutu ba sai babu wanda ya rage a duniya – Yusuf Gumel

“Rubutu mai inganci ne tushen ci gaban marubuci” Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Wani salo da ya bambanta marubuta maza da mata shine, batutuwan da kowanne ɓangare ya fi mayar da hankali akansa, don faɗakar da al'umma. A yayin da a ɗaya ɓangaren akasarin marubuta mata ke rubutu kan batutuwan da suka shafi zamantakewar aure da rayuwa, maza sun fi baje basirarsu ne ta ɓangaren jarumta da almara ko abubuwa masu tsoratarwa, da kuma a wani batutuwan da suka shafi sarauta da siyasa. Ko da yake kowanne daga cikin waɗannan ɓangarori yana iya ninkaya a cikin salon ɗaya ɓangaren. Wani marubuci…
Read More
‘Yan Sanda sun daƙile yunƙurin satar shanu a Katsina

‘Yan Sanda sun daƙile yunƙurin satar shanu a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta sami nasarar daƙile wani yunƙurin satar shanu tare da ƙwato dabbobi 76 da aka sace, waɗanda suka haɗa da shanu 20 da tumaki 56, a wasu ƙauyuka biyu da ke ƙaramar hukumar Dutsinma. A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar ya ce lamarin ya faru bayan da wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai suka kai hari ƙauyukan Yarmaje da Alasawa tare da sace dabbobi da dama. Sanarwar ta bayyana cewa, bayan samun kiran gaggawa, jami’an ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da jami’an…
Read More
Mutune 14,000 suka amfana da aikin ido na gidauniyar Mangal a Katsina

Mutune 14,000 suka amfana da aikin ido na gidauniyar Mangal a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gidauniyar Dahiru Barau Mangal ta yi wa mutane 14,000 aikin udo tun bayan fara gudanar da aikin a Jihar Katsina. Ɗaya daga cikin 'yan kwamitin amintattu na gidauniyar, Alhaji Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan yayin da ake ci gaba da aikin tiyatar ido kyauta ga mutum 600 a asibitin ido (Eye Centre) da ke tsohuwar kasuwa a birnin Katsina. Ya ce gidauniyar ce ta ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya, bayan kammala tantance waɗanda suka amfana, yana mai jaddada cewa ba a karɓar ko sisi daga hannun marasa lafiya. Alhaji Kabir ya bayyana cewa a…
Read More
Kashi 70 na manyan laifukan Kano na da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi – Muhuyi Magaji

Kashi 70 na manyan laifukan Kano na da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi – Muhuyi Magaji

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban kwamitin haɗin gwiwa na yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi na Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa kusan kashi 70 cikin 100 na manyan laifukan da ake aikatawa a jihar suna da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi. Muhuyi Magaji ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Kano, inda ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su mara wa gwamnatin jihar baya wajen wayar da kan al'umma kan illolin shan miyagun ƙwayoyi, fataucin haramtattun ƙwayoyi da kuma ayyukan 'yan daba. Ya ce, bisa ga ƙididdigar rundunar 'yan sandan Jihar Kano,…
Read More
Kwamintin da gwamnatin Katsina ta kafa na tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi ya ci gaba da aiki

Kwamintin da gwamnatin Katsina ta kafa na tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi ya ci gaba da aiki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamintin da gwamnatin Jihar Katsina ta kafa na tantance ma'aikatan ƙananan hukumomi 34 da ke jihar ta fara tantance masu ƙorafe-ƙorafe. Ma'aikata da dama da basu sami tsallake tantancewa ba suka miƙa takardar ƙorafe-ƙorafe wanda yasa gwamna Dikko Raɗɗa ya umarci kwamintin da ya sake duba koken su. Kwamintin ƙarƙashin shugaban mai ba gwamna shawara kan ƙananan hukumomi Alhaji Lawal Rufa'i Safana ya fara da ma'aikatan ƙananan hukumomin Kaita,Batagarawa da Katsina. Kwamintin ya fara da ma'aikata 100 da suka fito da ga waɗannan ƙananan hukumomin inda zai sake duba takardar karatu da na ɗaukar aiki…
Read More