29
Jul
Daga JOHN D. WADA a Lafia Shugaban ƙungiyar 'yan fansho na jihar Nasarawa Hudu Baba Abdullahi yace gwamnatin jihar ta Injiniya Abdullahi Sule zuwa yanzu za a iya cewa ta cire wa masu karɓan fansho na jihar kitse a wuta idan aka yi la'akari da makudan kuɗaɗe da gwamnan ke cigaba da amincewa don warware matsalolin 'yan fansho din a jihar baki ɗaya. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa wasu tambayoyi daga 'yan jarida da suka ziyarci ofishin ƙungiyar ta 'yan fansho dake garin Lafia fadar gwamnatin jihar ranar Talata na makon nan. Hudu Baba Abdullahi yace…
