ukarofi

12521 Posts
Waƙa:Ta’aziyyar Hauwa Ƙamshi

Waƙa:Ta’aziyyar Hauwa Ƙamshi

Dags MUHAMMED BALA GARBA  1. Rabbana Sarki Ilahu,       Rabbi mai tayar da ruhu,    Rabbi ga baiwarka Hauwa. 2. Babu mai tsarki ya naka,  Babu mai rahama kamarka, Rabbi kai rahama ga Hauwa.  3. Babu mai jin ƙai kamarka,          Babu mai tausai irinka,   Don Rasulu ka dubi Hauwa. 4. Duk Karamci na wurinka,         Ragwame ita ce sifarka,   Rabbi rangwantawa Hauwa. 5. Yadda duk kayi babu mita,        Ba mu jayayya da yin ka, Rabbi kai rahama ga Hauwa. 6. Hauwa Ƙamshi jaruma ce,       Babu shakka malama ce,     Mai rubuce-rubuce Hauwa. 7. Rabbi duk an mata shaida,               Kamila ce mai ibada,      Sayyada laƙabi…
Read More
Cikakken jerin sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓen Kungiyar Lauyoyin Nijeriya na 2026

Cikakken jerin sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓen Kungiyar Lauyoyin Nijeriya na 2026

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An bayyana cikakken sakamakon zaɓen shugabannin ƙasa na ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) na shekarar 2026, bayan kammala zaɓe da kuma sanar da sakamakon da Kwamitin Gudanar da Zaɓen NBA (ECNBA) ya yi a ranar Lahadi. Kamar yadda aka ruwaito a baya, Babbar Lauya mai Matsayin SAN, Misis Oyinkansola Badejo-Okusanya, ta zama shugabar NBA ta 33 bayan ta doke sauran manyan lauyoyi biyu da suka fafata da ita a zaɓen shugaban ƙungiyar. Shugaban Kwamitin Gudanar da Zaɓen NBA (ECNBA), Aham Ejelam (SAN), ne ya sanar da sakamakon a hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja. Badejo-Okusanya ta samu ƙuri'u…
Read More
Kalubalen samar da ’yan sandan jihohi ga tsaro 

Kalubalen samar da ’yan sandan jihohi ga tsaro 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A yayin da nake wannan rubutu Majalisar Dattawa ta kammala aiki akan ƙudirin dokar da za ta bayar da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi bayan an yi wa ƙudirin dokar karatu na uku, lamarin da ya kawo ƙarshen muhawarar da aka ɗibi tsawon shekaru ana gudanarwa akan tsarin ‘yan sandan jihohi, domin warware matsalolin taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Rahotanni sun tabbatar da cewa, an cimma nasarar hakan ne bayan dogon nazari da kuma amincewa da ƙudirin a dokance daga biyu bisa uku na majalisar. Haka kuma, an amince da ƙudirin a zaman majalisar ne bayan…
Read More
Shehu bai ƙwace ƙasar kowa ba!

Shehu bai ƙwace ƙasar kowa ba!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Sam Shehu Mujaddadi bai ƙwace ƙasar kowa ba, hasalima waɗanda su ka karɓi tuta ‘yan asalin yankin da su ke sarauta ne. Shehu Mujaddadi Bagobiri ne ko ɗan Gobir a matsayin mahaifarsa a ƙasarsa ta gado Wallahi akwai takaici da ban mamaki wani dan kwangilar AIFOB ko na makiya Arewa wanda ba shi ma da alaƙa ta kusa ko nesa da Hausawa; ya rubuta wai Shehu Mujaddadi ya ƙwace ƙasar Hausa ko ya yaƙi wani Sarki da sauran shirmen makirci da sai a soshiyal midiya dandalin bulus na Bello Badum a ke gani. In ka deɓe…
Read More
Gwamnatin Katsina ta horar da ma’aikatan jihar kan shirin HOPE na Bankin Duniya

Gwamnatin Katsina ta horar da ma’aikatan jihar kan shirin HOPE na Bankin Duniya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta horas da jami’an gwamnati kan inganta aiwatar da Shirin HOPE na Bankin Duniya. Hukumar kula da tsare-tsaren cigaban Jihar Katsina (KTDMB) ta shirya wani kwas na kwanaki biyu domin horas da manyan jami’an gwamnati kan yadda za a inganta aiwatar da shirin Bankin Duniya na HOPE. HOPE na Bankin Duniya yana da manufar inganta yadda ake tafiyar da ayyukan gwamnati da kuma samar da cigaba ga al'umma. Shirin yana da ginshiƙai guda 3 da suka hada da ɓangaren tafiyar da gwamnati watau HOPE-Gov, ɓangaren inganta harkar ilimi watau HOPE-Edu da kuma…
Read More
Rabaran Mary Ovye ta jaddada muhimmancin aiki tare tsakanin Kiristoci

Rabaran Mary Ovye ta jaddada muhimmancin aiki tare tsakanin Kiristoci

Daga JOHN D. WADAa Lafia Matar babban bishop na Iklisiyar Threshing Floor Watchman Assembly da ake kira Salvation City dake Bukan sidi a birnin Lafia jihar Nasarawa wato Rabaran Mary Ovye ta jaddada muhimmancin aiki tare tsakanin mabiya addinin Kirista don cimma manufa guda musamman samun rahamar ubangiji da kuma rai madauwami. Rabaran Mary Ovye tayi kiran ne a lokacin da take wa'azin sujadar Iklisiyar ranar La'adi na mako da ake ciki a Iklisiyar. Tace tabbas kiran ya zama wajibi idan aka yi la'akari da ɗimbin alfanu da kuma nasarori da ake samu a duk lokaci da mabiya Annabi Isa…
Read More
Jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga 40 a Katsina

Jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga 40 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami’an tsaro sun halaka ’yan bindiga sama da 40 da suka haɗa da manyan kwamandojin su da daƙile hari da ’yan bindigar suka kai a garin Guga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar. Kwamishinan cikin gida da na jihar, Dr.Nasir Mu’azu, wanda ya fitar da sanarwar haka ya ce, sama da ’yan bindiga 200 ɗauke da makamai, ƙarƙashin jagorancin fitaccen shugaban ’yan bindiga Idi Abasu Aiki, tare da wasu ’yan ƙungiyar Ado Aleru, daga maƙwabciyar Jihar Zamfara, sun kai harin ramuwar gayya a garin Guga da misalin yammacin Lahadi. Sai dai jami'an tsaro,bayan samun…
Read More
Ruwan sama mai iska ya rusa gidaje sama da 200 da shaguna a Katsina

Ruwan sama mai iska ya rusa gidaje sama da 200 da shaguna a Katsina

Dagà UMAR GARBA a Katsina Mamakom ruwan kamar da bakin ƙwarya haɗe da iska ya rusa ɗaruruwan gidaje a garin Dangamau da ke ƙaramar hukumar Kusada ta jihar Katsina, al'umma a yankin sun rasa matsugunansu bayan wata guguwa mai ƙarfi haɗe da ruwan sama ta lalata gidaje, shaguna da sauran kadarori sama da 200, waɗanda darajarsu ta kai miliyoyin naira. Wannan ibtila'i da ya faru a cikin makon da ya gabata ya sa iyalai da yawa sun rasa matsuguni da kuma kawo cikas ga harkokin tattalin arziki. Da yake mayar da martani ga lamarin, Gwamnan jihar Katsina Dikko Raɗɗa ya…
Read More
Makarantar Sautus Sunnah ta yaye ɗalibai a Katsina

Makarantar Sautus Sunnah ta yaye ɗalibai a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Makarantar Sautussunnah International Comprehensive Secondary Schools Katsina ta gudanar da walimar yaye ɗalibai karo na tara. An yaye ɗalibai 60 bayan sun kammala jarabawar ƙarshe ta WAEC da NECO a fannonin Kimiyya da fasaha da ɓangaren adabi da fasaha (Science da Arts). Baya ga karatun zamani, makarantar ta ba da muhimmanci sosai ga tarbiyyar addinin musulunci da koyar da Alƙur'ani mai girma. Ɗaliban da aka yaye sun haɗa da: Ɗalibai 22 sun kammala hardar Alƙur'ani mai girma baki ɗaya, ɗalibai 15 sun haddace hizifi 50. Ɗalibai 13 sun harlddace hizifi 30,sai ɗalibai 10 da suka…
Read More
CITAD ta yi fatali da ƙudirin tilasta kamfanonin kafafen sada zumunta ɓuɗe ofisoshi a Nijeriya

CITAD ta yi fatali da ƙudirin tilasta kamfanonin kafafen sada zumunta ɓuɗe ofisoshi a Nijeriya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al'umma (CITAD) ta bayyana adawarta ga ƙudirin gyaran dokar kare bayanai ta Nijeriya ta 2023, wanda ke neman tilasta wa kamfanonin kafafen sada zumunta, masu sarrafa bayanai da masu kula da bayanai buɗe ofisoshi a cikin ƙasar. Cibiyar ta ce idan aka amince da kudirin, hakan na iya tauye haƙƙin dijital, rage ƙirƙire-ƙirƙire da kuma kawo cikas ga bunƙasar tattalin arzikin dijital na Nijeriya. Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar CITAD da ke Kano, daraktan zartarwa na cibiyar, Dakta Yunusa Zakari Ya'u, wanda…
Read More