ukarofi

12521 Posts
Na zo domin na yi tasiri, ba don cike gurbi ba, inji Oyinkansola, sabuwar shugabar NBA

Na zo domin na yi tasiri, ba don cike gurbi ba, inji Oyinkansola, sabuwar shugabar NBA

“Takun mace ta farko da aka zaɓa kai tsaye ta jagoranci ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya” Daga AISHA ASAS Akwai kwanakin da ba su buƙatar shela domin a san cewa sun bambanta da sauran kwanaki. Kwanaki ne da tarihi kan buɗe sabon shafi, al'umma kuma ta tsaya ta na kallon yadda sabon labari ke samun gurbi a cikin littafin tarihi. Irin waɗannan kwanaki ba su sauya labarin mutum ɗaya kaɗai; su na sauya yadda ake kallon abin da zai yiwu a gaba. A ranar da aka sanar da sakamakon zaɓen shugabancin ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), ba wai kawai an bayyana sunan wadda…
Read More
Annobar cutar aladu ta ɓarke a Jihar Filato – Gwamnatin Filato

Annobar cutar aladu ta ɓarke a Jihar Filato – Gwamnatin Filato

Daga HABU ƊAN SARKI, a Jos Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da ɓarkewar annobar cutar African Swine Fever, mai saurin kashe aladu, wacce kawo yanzu ta kashe aladu fiye da 5000 daga gonakin kiwon aladu 280. Gwamnatin ta sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ma'aikatar kula da dabbobi ta Jihar Filato, inda aka bayyana cewa, kawo yanzu cutar ba ta da magani kuma ba ta da rigakafi. Harwayau, sanarwar ta bayyana takaici kan yadda kimanin wata biyu da fara ganin alamun cutar amma masu gonakin ba su yi gaggawar sanar wa hukumomin abin ya…
Read More
Ɗan takarar PDP na Zamfara ya yi Allah-wadai da harin Bungudu

Ɗan takarar PDP na Zamfara ya yi Allah-wadai da harin Bungudu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na mazabar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa, Alhaji Sanusi Bala Gusau, ya yi Allah wadai da harin ‘yan bindiga na baya bayan nan a ƙaramar hukumar Bungudu, sannan ya yi alƙawarin bai wa tsaro fifiko idan aka zaɓe shi. A cikin sakon ta’aziyyar da ya aika wa mutanen Bungudu ranar Lahadi, Gusau ya bayyana kisan a matsayin abin baƙin ciki da zafi, inda ya ce yadda talauci da wahala suka bazu cikin al’umma ya sa siyasa ta zama ta biyu, domin yanzu rayuwa ce ta farko. “Mutane…
Read More
Babbar Kotun Kebbi ta tura wasu mata gidan yari bisa taimaka wa ‘yan ta’adda

Babbar Kotun Kebbi ta tura wasu mata gidan yari bisa taimaka wa ‘yan ta’adda

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR, Birnin Kebbi Wata babban kotun Jihar Kebbi da ke zamanta a Birnin Kebbi, ta yanke ma wasu mata guda uku ɗaurin shekara 14 kowanensu a gidan yari, bisa dalilin haɗa kai da taimakawa 'yan ta'adda da kuma kasancewa cikin ƙungiyar 'yan ta'adda. Amma kotun ta sallami, kuma ta wanke wadda ake tuhuma ta farko dangane da duk laifuffukan da aka gabatar a kan ta. Da yake yanke hukuncin, Justice Hassan Shehu Kuwwa, yayi amanna cewar ɓangaren gabatar da ƙara ya sauke nauyin da ke kafaɗarsa na tabbatar da laifuffukan a kan waɗanda ake tuhuma, ta biyu…
Read More
‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da wani alƙalin babban kotun Kebbi

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da wani alƙalin babban kotun Kebbi

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi Mahukuntan babban kotun Jihar Kebbi sun tashi tsaye tare da haɗin gwiwan hukumomin tsaro domin ceto wani alƙalin kotun, Justice Faruq Hassan Bunza, wanda 'yan bindiga suka wuce da shi daga gidansa dake Bunza da tsakar daren Asabar. Rahotanni na nuna cewar Justice Faruq Bunza yayi tafiya zuwa maƙwabciyar Jihar Sokoto, a sa'ilin da ya dawo gida da sha-biyun dare, ya tarar da 'yan bindiga na jiransa a ƙofar gidansa, a inda suka dinga aman-wuta da bindigogi ta sama, domin razana jama'a, daga nan kuma, suka wuce da alƙalin na babban kotu. Tuni dai…
Read More
Gwamnatin Katsina ta jaddada ƙudirinta na cigaba da gyara makarantun da suka lalace

Gwamnatin Katsina ta jaddada ƙudirinta na cigaba da gyara makarantun da suka lalace

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Katsina ta damu da labarin da wasu al'ummomi suka ɗora a soshiyal midiya kan lalacewar wata makaranta,hakan ya sanya gwamnati ta jaddada ƙudirin ta na gyara makarantu a faɗin jihar. Kwanan nan gwamnatin jihar ta kammala gina makarantun sakandare guda 30 da wasu alƙawarin bada kwangilar wasu guda 49 a faɗin jihar. Wata sanarwa ɗauke da sanya hannun kwamishinan Ilimi,Hon Yusuf Suleiman Jibiya, ya yaba wa alummomi da ke fitowa suna miƙa irin wannan buƙata tasu. Kwamishinan ya tabbatar wa alummar cewa dama gwamnatin jihar ta sanya wannan makaranta cikin makarantun da gwamnati za…
Read More
Gwamnatin Katsina ta gudanar da jarrabawa ga mahaddatan Alƙur’ani

Gwamnatin Katsina ta gudanar da jarrabawa ga mahaddatan Alƙur’ani

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya gudanar da jarrabawa ga mahaddatan Alƙur'ani mai girma a faɗin jihar Katsina domin ɗaukar nauyin karatun su a ɓangaren aikin likita da sauran ɓangarorin kiwon lafiya. An gudanar da jarrabawar a ɗakunan jarrabawa da ke jami'ar Umaru Musa Yar'adua nan cikin garin Katsina. Shirin wanda ofishin mai bawa gwamna shawara na musamman a kan karatun Alkur'ani da yaran da ba su zuwa makaranta, Hon Injiniya Tasi'u Dahiru Dandagoro ke gudanarwa. Da yake gabatar da jawabin sa Hon. Tasiu Ɗandagoro ya bayyana cewa" wannan shiri gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam…
Read More
Jam’iyyar NDC a Zamfara ta yi Allah-wadai da harin ‘yan ta’adda a jihar

Jam’iyyar NDC a Zamfara ta yi Allah-wadai da harin ‘yan ta’adda a jihar

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Reshen jam’iyyar National Democratic Congress, NDC a Jihar Zamfara ta yi Allah-wadai da sabbin hare-haren ‘yan ta’adda da suka kai a ƙananan hukumomin Talata Mafara da Bungudu. Jam’iyyar ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal su ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen ayyukan 'yan ta'adda a jihar. A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi mai magana da yawun jam’iyyar, Alƙassim Mustapha Kayatawa ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce ta karɓi labarin hare-haren cikin alhini da bakin ciki. A cewar NDC, ‘yan bindigar sun kashe manoma da dama…
Read More
Rufe mashigar Hormuz ya bankaɗo raunin tsarin makamashin Afirka

Rufe mashigar Hormuz ya bankaɗo raunin tsarin makamashin Afirka

Rufe mashigar ruwa ta Hormuz ya sake tayar da hankulan masana kan irin raunin da tsarin makamashin Afirka ke da shi, bayan haɗuwa da tasgaro a safarar mai da ya bayyana yadda ƙasashen nahiyar ke ci gaba da dogaro da ƙasashen Asiya da Gabas ta Tsakiya wajen biyan bukatunsu na makamashi. Wani rahoto da shafin Oil.com ya wallafa ya ce ci gaba da takaita zirga-zirgar jiragen dakon makamashi ta mashigar Hormuz na iya sauya alƙiblar hulɗar makamashi a nahiyar, inda ake hasashen ƙasashe irin su Rasha da Turkiyya za su ƙara faɗaɗa alaƙarsu da gwamnatocin Afirka. Rahoton ya ce ƙasashen…
Read More
Houthi ta sauya akalar safarar man Saudiyya yayin da yaƙin Amurka da Iran ke ƙara tsananta

Houthi ta sauya akalar safarar man Saudiyya yayin da yaƙin Amurka da Iran ke ƙara tsananta

Rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ya sake ɗaukar sabon salo bayan ƙungiyar Houthi ta Yemen ta buɗe wani sabon fagen matsin lamba ta hanyar kakaba takunkumin ruwa kan Saudiyya, matakin da ya fara girgiza harkokin safarar mai da zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Sabon matakin ya tilasta wasu manyan jiragen dakon danyen man Saudiyya guda biyu da suka nufi kasuwannin Chana da Indiya sauya alkibla a Tekun Bahar Maliya, domin kauce wa mashigin Bab el-Mandeb bayan Houthi ta yi barazanar kai hari kan duk wani jirgin da zai dauki ko sauke man Saudiyya. Masana harkokin…
Read More