26
Jul
Babban daraktan Hukumar Yaki da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC), Jean Kaseya, ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta janye takunkumin tafiye-tafiye da ta kakaɓa wa Uganda sakamakon ɓarkewar cutar Ebola, yana mai cewa babu wani dalili da zai sa a ci gaba da ɗaukar irin wannan mataki bayan ƙasar ta shafe kusan wata guda ba tare da samun sabon mai ɗauke da cutar ba. Kaseya ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Accra, babban birnin Ghana, inda ya ce ya aike wa Sakataren Lafiya na Amurka, Robert F. Kennedy Jr., wasiƙa yana rokon a soke takunkumin.…
