ukarofi

12521 Posts
YAN za ta gudanar da babban taro na ƙasa a Abuja

YAN za ta gudanar da babban taro na ƙasa a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamitin Amintattu na ƙungiyar Matasan Nijeriya (YAN) ya sanar da kafa Kwamitin Shirya Babban Taron ƙasa, tare da ba da umarnin fara shirye-shiryen gudanar da zaɓuɓɓuka a matakin jihohi da Babban Birnin Tarayya, Abuja. A cikin wata sanarwar manema labarai da Kwamitin Amintattun ya fitar daga hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja ranar 19 ga Yuli, 2026, ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne bisa tanadin Sashe na 4, ƙaramin Sashe na 8 na Kundin Tsarin Mulkin YAN da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2024. Sanarwar ta jaddada cewa Kwamitin Amintattu shi ne mafi girman sashi…
Read More
MURIC ta buƙaci Tinubu ya amince da dokar hana wa’azi a motocin haya duk da adawar Kirista

MURIC ta buƙaci Tinubu ya amince da dokar hana wa’azi a motocin haya duk da adawar Kirista

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmi ta Nijeriya (MURIC) ta zargi wasu shugabannin Kirista a Nijeriya da fifita muradunsu na ƙashin kansu bayan sun nuna adawa da ƙudirin dokar Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) da ke neman haramta wa'azi da talla a cikin motocin haya. A cikin wata sanarwa da Daraktan Gudanarwa na ƙungiyar, Farfesa Ishaƙ Akintola, ya fitar a ranar Litinin, MURIC ta bayyana mamakinta kan yadda shugabannin Kirista suka yi watsi da ƙudirin, tana mai cewa manufarsa ita ce rage haɗurran hanya da kuma daƙile rikice-rikicen addini. ƙungiyar ta bayyana cewa adawar da aka nuna…
Read More
An buƙaci iyayen yara Musulmi a Legas su ƙara ba ilimin addini da na zamani muhimmanci

An buƙaci iyayen yara Musulmi a Legas su ƙara ba ilimin addini da na zamani muhimmanci

Daga DAUDA USMAN a Legas An shawarci iyayen yara Musulmi a Jihar Legas da ma Nijeriya baki ɗaya da su ƙara ƙaimi wajen sanya 'ya'yansu a makarantun koyar da Alƙur'ani Mai Tsarki da sauran ilimin zamani, domin su samu tarbiyya ta gari da ilimi mai amfani. Wannan kira ya fito ne daga shugaban kula da ci gaban ɓangaren kasuwancin kayan ƙamshin Yarabawa a Kasuwar Mile 12 da ke Legas, Alhaji Abdulmummuni Cikada, ɗan asalin ƙaramar Hukumar Kiru ta Jihar Kano. Ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi a taron bikin walimar yaye ɗalibai karo na biyar na Makarantar…
Read More
Yadda APC ke amfana da rikicin NDC a Kano gabanin zaɓen 2027

Yadda APC ke amfana da rikicin NDC a Kano gabanin zaɓen 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ƙara zage damtse wajen tattaunawa da manyan jiga-jigan adawa a Jihar Kano, yayin da jam'iyyar ke ƙoƙarin cin gajiyar rikicin cikin gida da ke addabar Nigeria Democratic Congress (NDC) gabanin babban zaɓen 2027. Daga cikin waɗanda APC ke ƙoƙarin jawo hankalinsu akwai Sanata Rufa'i Sani Hanga mai wakiltar Kano ta Tsakiya, wanda shi ne kaɗai sanatan NDC mai ci daga jihar, da kuma tsohon Sanata Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ta Kudu. Rahotanni sun nuna cewa Yilwatda ya gana da Sanata Hanga sau biyu…
Read More
2027: Kalaman Fadar Shugaba ƙasa sun nuna Tinubu na tsoron gudanar da zaɓe – APM

2027: Kalaman Fadar Shugaba ƙasa sun nuna Tinubu na tsoron gudanar da zaɓe – APM

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta zargi Fadar Shugaban ƙasa da ci gaba da kai hare-haren kalamai kan ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, tana mai cewa hakan alama ce da ke nuna Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fargabar zaɓen da ke tafe. A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam'iyyar, Abubakar Yusuf, ya fitar a Abuja, APM ta ce kalaman mai magana da yawun shugaban ƙasa, Daniel Bwala, kan Makinde sun nuna cewa gwamnatin Tinubu ta fara nuna damuwa game da zaɓen…
Read More
Zargin sauya ɗan takarar ADC a Adamawa ya janyo zanga-zangar magoya bayan Omarana

Zargin sauya ɗan takarar ADC a Adamawa ya janyo zanga-zangar magoya bayan Omarana

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ana ci gaba da fuskantar sabon rikicin siyasa a Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Adamawa, bayan zargin cewa wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar na ƙoƙarin sauya ɗan takarar gwamna, Ambasada Injiniya Omar Suleiman, wanda aka fi sani da Omarana, gabanin zaɓen 2027. A ranar Laraba, ɗaruruwan magoya bayan jam'iyyar sun gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Yola, babban birnin jihar, domin nuna adawarsu ga abin da suka bayyana a matsayin yunƙurin maye gurbin ɗan takarar. Masu zanga-zangar sun yi tattaki a manyan tituna da cibiyoyin gwamnati ɗauke da alluna masu ɗauke da saƙonni…
Read More
2027: Fubara ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu da ɗan takarar Wike

2027: Fubara ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu da ɗan takarar Wike

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana goyon bayansa ga takarar wa'adi na biyu ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da ɗan takarar gwamnan jihar, Kingsley Chinda, a babban zaɓen shekarar 2027. Fubara ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin bikin aza harsashin ginin Riɓen Medical Industries Project a birnin Fatakwal. Ya ce sabanin siyasa da ya raba masu ruwa da tsaki a jihar ya zo ƙarshe, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da za a fifita zaman lafiya da haɗin kai maimakon rikicin siyasa. Gwamnan ya kuma bayyana cewa ya koma…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya bada umarmin dashen bishiyoyi a manyan titinan Katsina

Gwamna Raɗɗa ya bada umarmin dashen bishiyoyi a manyan titinan Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An gudanar da shirin dashen bishiyoyi 16,000 mai taken "Dikko Green", a titunan WTC, Filin Polo da kuma Kofar Sauri zuwa Shinkafi, cikin garin Katsina. Da yake gabatar da jawabinsa, mai bai wa gwamna shawara kan harkokin sauyin yanayi, Prof. Muhammad Al'amin, ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci ƙaddamar da dashen bishiyoyi 16,000 da gwamnatin Jihar Katsina ta samar ƙarƙashin shirin "Dikko Green." Hakazalika, ya bayyana cewa wannan na daga cikin yunƙurin gwamnatin Jihar Katsina na magance matsalar ɗumamar yanayi. Shi ya sa ta ga ya dace a dasa bishiyoyi 16,000 domin samar…
Read More
WAFCON: An yi wa ‘yan wasan Super Falcons fashi a otal ɗin Morocco

WAFCON: An yi wa ‘yan wasan Super Falcons fashi a otal ɗin Morocco

Daga USMAN KAROFI Hukumomin tsaro na ƙasar Morocco sun fara gudanar da bincike kan zargin satar fiye da dala 1,200 daga ɗakunan 'yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, yayin da suke ci gaba da shirye-shiryen shiga gasar kofin nahiyar Afirka ta mata (WAFCON) ta 2026. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya fito fili ne bayan 'yar wasan gaba, Esther Okoronkwo, ta bayyana abin da ya faru a shafinta na Snapchat. 'Yan wasan suna sauka ne a otal ɗin Marriott da ke birnin Casablanca, inda ake zargin ma'aikatan tsaftar otal ɗin da samun damar shiga ɗakunansu…
Read More
KASSAROTA ta fitar da sababbin umarni ga jami’anta a Katsina

KASSAROTA ta fitar da sababbin umarni ga jami’anta a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD A Katsina Hukumar KASSAROTA ta jihar Katsina ta fitar da wasu sabbin umarni da ta ce an tsara su ne domin inganta gudanar da aiki da kuma kare haƙƙin al'umma. A wata sanarwar da sakataren jihar na KASSAROTA, Malam Aminu Lawal Batsari ya fitar, an haramta wa jami'an hukumar yin aiki a kan hanya da sanda ko wani nau'in makami, tare da hana bin mutane da gudu domin kama su. Sanarwar ta kuma ce kada a kama tsofaffi, masu ɗauke da ɗaliban makaranta, ma'aikatan da ke kan aikin agaji kamar na lafiya, ko kuma magidanci da ke…
Read More