25
Jul
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Al’ummar ƙaramar hukumar Bungudu sun shiga cikin baƙin ciki a daren Juma’a, bayan wani hari da yan bindiga suka kai wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro 4, da raunata wasu da dama, tare da sace shugaban ƙaramar hukumar Bungudu. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:40 na dare a ranar Juma’a, kamar yadda rahotannin daga al’umma suka bayyana. Majiyoyi sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce yan bindigar sun yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Bungudu, Hon. Nura Umar Abdullahi, a lokacin harin. An kuma yi garkuwa da wasu fararen hula guda…
