ukarofi

12663 Posts
Ba ni da hannu a yunƙurin kashe Wike – Danagogo

Ba ni da hannu a yunƙurin kashe Wike – Danagogo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon ministan wasanni a Nijeriya, Dakta Tammy Danagogo, ya musanta zargin da ake yi cewa yana da hannu a wani yunƙurin kashe ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike. Cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Fatakwal da yammacin ranar Litinin, tsohon Ministan wasannin ya yi watsi da zarge-zargen da aka yi masa, inda ya ce ba su da tushe balle makama. Sanarwar wadda mataimakinsa na musamman, Barista Obele Briggs ya sanya wa hannu, ta ce Danagogo bai taɓa shiga wata tattaunawa, ko taro ko shiri da ya shafi kitsa tashin hankali, ko…
Read More
Babu gwamnan da ke juya akalar Jam’iyyar APC — Yilwatda

Babu gwamnan da ke juya akalar Jam’iyyar APC — Yilwatda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce babu wani gwamna da ke juya akalar jam’iyyar. Ya bayyana cewa dukkanin shawarwarin da ake zartarwa a APC ana yin su ne a matakin ƙasa, ba ta hannun gwamnonin jihohi ko shugabannin jihohi ba. Ya bayyana hakan ne cikin shirin ‘Sunset a Jay FM’, Jos, Jihar Filato. Ya ce: “A faɗin ƙasar nan, babu wanda zai iya ɗaukar wani sashe na jam’iyya. Duk abin da za a yi a matakin jiha, ana tsara shi ne a matakin ƙasa. “Wannan tsarin APC ne. Muna aiki…
Read More
Dasa bishiyu na tabbatar da lafiyar muhalli da samar da yanayi mai inganci – MD H-JRBDA

Dasa bishiyu na tabbatar da lafiyar muhalli da samar da yanayi mai inganci – MD H-JRBDA

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Manajan Darakta na Hukumar Raya Kogunan Haɗeja–Jama’are (H-JRBDA), Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, ya bayyana cewa dasa bishiyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da lafiyar muhalli, rage dumamar yanayi da kare ƙasa daga zaizayar ƙasa. Ya bayyana hakan ne yayin bikin dashen bishiyoyi guda ɗari da aka gudanar a harabar hukumar a Kano, a wani ɓangare na ƙoƙarin yaƙi da dumamar yanayi. Shirin ya gudana ne tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Injiniyoyi mata ta ƙasa, reshen Jihar Kano. Injiniya Bichi ya jaddada cewa dasa bishiyoyi a wannan lokaci abu ne mai matuƙar muhimmanci, duba…
Read More
‘Yar Atiku Abubakar ta shiga ADC a hukumance

‘Yar Atiku Abubakar ta shiga ADC a hukumance

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fatima Atiku Abubakar, 'yar fari ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ta shiga jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance. An tarbi Fatima cikin jam'iyyar a ranar Litinin a Abuja. Tsohuwar Kwamishinan Lafiya ta Jihar Adamawa ta yi rijista a hukumance a matsayin memba na ADC a gundumarta da ke yankin Wuse na Babban Birnin Tarayya, inda ta kuma karɓi katin zama memba na jam'iyyar. Jami'an jam'iyyar da masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun haɗa da Shugaban FCT na ADC, Clement Oba Ehigiator, shugaban Majalisar ƙaramar Hukumar Abuja ta jam'iyyar,…
Read More
Gwamnan Zamfara ta zargi Ministan Tsaro da amfani da ofishin NSA wajen gallaza wa ’yan adawa

Gwamnan Zamfara ta zargi Ministan Tsaro da amfani da ofishin NSA wajen gallaza wa ’yan adawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta bayyana matuƙar damuwar ta kan abin da ta kira amfani da ƙarfin Gwamnatin Tarayya wajen gallazawa da tsoratar da ’yan adawa a jihar, tana mai cewa wannan al’amari na barazana ga dimokuraɗiyya da tsarin doka a Nijeriya. A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, gwamnatin ta ce ba ta da wani zaɓi face ta sanar da jama’a yadda ƙaramin Ministan Tsaro ke amfani da ofishin Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaro, wato NSA, wajen gallaza wa ’yan adawa da…
Read More
CIA da KGB sun ɗauki nauyin ƙungiyoyin ƙwadago don raunana Nijeriya – Obasanjo

CIA da KGB sun ɗauki nauyin ƙungiyoyin ƙwadago don raunana Nijeriya – Obasanjo

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa a wani lokaci a tarihin Nijeriya, ƙungiyoyin ƙwadago sun faɗa cikin tasirin siyasar Yaƙin Cacar Baki, inda wasu ɓangarori ke samun ɗaukar nauyi daga Hukumar Leƙen Asiri ta Amurka (CIA) yayin da wasu kuma ke karɓar tallafi daga KGB ta tsohuwar Tarayyar Soɓiet. Obasanjo ya bayyana haka ne a Abuja yayin bikin cika shekaru 85 da haihuwa da kuma aaddamar da littafin tsohon shugaban NLC, Hassan Sunmonu. Taron ya samu halartar manyan jagororin ƙwadago, tsofaffin shugabanni da kuma ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar. Tsohon shugaban ƙasar…
Read More
Kamus na Oxford ya saka ‘Abeg’, ‘Moi moi’, ‘Amala’ da wasu kalmomin Nijeriya

Kamus na Oxford ya saka ‘Abeg’, ‘Moi moi’, ‘Amala’ da wasu kalmomin Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamus na Oxford (Oxford English Dictionary – OED) ya sabunta kundinsa inda ya saka wasu kalmomin asalin Nijeriya, ciki har da “abeg”, “moi moi”, “amala”, “nyash” da “mammy market”, a matsayin wata shaida ta ƙaruwar tasirin harshe da al’adar Nijeriya a duniya. Rahoton da News Point Nigeria ta wallafa ya nuna cewa sabuntawar watan Disambar 2025 ta ƙara fiye da kalmomi da jimloli 500, tare da sabunta bayanan sama da kalmomi 1,000 da suka riga suna cikin ƙamus ɗin. Editocin OED sun ce wannan sabuntawa na nuna yadda Ingilishi daga sassa daban-daban na duniya, ciki har…
Read More
Muna cikin talauci, yunwa da rashin matsuguni, inji ɗaliban Nijeriya a Moroko

Muna cikin talauci, yunwa da rashin matsuguni, inji ɗaliban Nijeriya a Moroko

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu ɗaliban Nijeriya da ke karatu a Moroko a ƙarƙashin shirin tallafin karatu na Gwamnatin Tarayya sun bayyana halin da suke ciki, inda suka ce tsawon watanni, kusan ma da shekaru ana watsi da su ba tare da kulawa ba, lamarin da ya jefa da dama cikin yunwa, rashin matsuguni da kuma tangarɗar samun kulawar lafiya. A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ranar Talata, an ga mai sukar al’amuran gwamnati a kafafen sada zumunta, ɓincent Martins Otse, wanda aka fi sani da ɓDM, yana tattaunawa da wasu daga cikin ɗaliban Nijeriya da…
Read More
’Yan ‘One-chance’ sun kashe ma’aikaciyar jinya a Abuja

’Yan ‘One-chance’ sun kashe ma’aikaciyar jinya a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An tabbatar da mutuwar wata ma'aikaciyar jinya 'yar shekara 28, Chinemerem Pascalina Chuwumeziem, bayan da ake zargin ‘yan fashin one-chance ne suka hallaka ta a birnin Abuja.  Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Janairu, 2026, jim kadan bayan ta kammala aikin ta na rana, tana kan hanyar komawa gida. Washegari da safe, ranar 4 ga Janairu, aka tsinci gawarta a gefen hanya, inda daga bisani aka kai ta ɗakin ajiye gawa na Asibitin FMC Jabi domin bincike da tanadin doka. Marigayiyar ma’aikaciya ce a Asibitin Tarayya na FMC Abuja, inda take…
Read More
Kasafin kuɗi: Za a cimma ƙudirorin Tinubu a 2026 – Idris

Kasafin kuɗi: Za a cimma ƙudirorin Tinubu a 2026 – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa an tsara kasafin kuɗin 2026 ne domin ƙarfafa nasarorin da tsarin shirye-shiryen Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka fara samarwa, waɗanda tuni suka fara nuna sakamako mai kyau. Ministan ya bayyana hakan ne a wani sharhin sa da aka wallafa a jaridun ƙasar nan ranar Litinin, mai taken “Muhimmin Lokaci A Nijeriya: Hujjar Da Ta Sa Hanyar Da Aka ɗauka Ita Ce Mai ɓullewa.” A sharhin, Idris ya ce: “’Kasafin Kuɗin ƙarfafa ƙasa, Sabuwar Juriya da Wadata ta Bai-ɗaya’ yana da matuƙar muhimmanci.…
Read More