ukarofi

12663 Posts
Muhimman abubuwan da suka faru a 2025

Muhimman abubuwan da suka faru a 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shekara ta 2025 ta kasance mai cike da sauye-sauye masu zurfi a Nijeriya, inda aka samu mubimman sauye-sauyen tattalin arziki, canjin siyasa da tsanantar ƙalubalen tsaro. Waɗannan abubuwa ne suka fi ɗaukar hankalin jama’a, tare da barin tasiri mai zurfi a rayuwar al’umma da tafiyar dimokuraɗiyyar ƙasar. A ɓangaren ilimi, shekarar ta fara da taƙaddama tsakanin ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya, ASUU, da Gwamnatin Tarayya. Wannan ne karo na farko da ASUU ta shiga yajin aiki tun bayan hawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan mulki a 2023. A ranar 13 ga Oktoba, 2025, ASUU ta shiga…
Read More
Majalisar Dokokin Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara

Majalisar Dokokin Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, lamarin da ya haddasa ruɗani a siyasar jihar. A zaman majalisar na ranar Alhamis, da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, ya jagoranta, Shugaban Masu Rinjaye, Major Jack, ya karanta takardar zargin da ake yi wa gwamnan bisa aikata manyan laifuka. Ya danganta yunƙurin nasu da Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya. Daga cikin zarge-zargen da ake yi wa Gwamna Fubara, akwai rushe ginin Majalisar Dokokin, kashe kuɗaɗen gwamnati ba tare da amincewa da kasafin kuɗi ba. Sauraun sun…
Read More
‘Yan sanda sun ƙwace babura 104 da adaidaita sahu 68 bisa keta dokar zirga-zirga a Kano

‘Yan sanda sun ƙwace babura 104 da adaidaita sahu 68 bisa keta dokar zirga-zirga a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ƙwace aƙalla babura 104 na haya da kuma adaidaita sahu 68, tare da kama mutane 172, bisa keta dokar da gwamnatin jihar ta kafa ta haramta safarar fasinjoji da babura (Achaba/Okada) da kuma taƙaita zirga-zirgar adaidaita sahu a cikin birnin Kano. Aikin aiwatar da dokar, wanda aka gudanar daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Janairun 2026, rundunar 'yan sandan ta yi shi ne tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, domin tabbatar da bin dokar haramta amfani da babura wajen safarar fasinjoji, da kuma dokar takaita zirga-zirgar adaidaita…
Read More
Dangote ya janye ƙorafin da ya shigar kan tsohon Shugaban NMMPRA

Dangote ya janye ƙorafin da ya shigar kan tsohon Shugaban NMMPRA

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote, ya janye ƙorafin da ya shigar a Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) kan tsoho Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai Fetur ta ƙasa (NMMPRA), Farouk Ahmed. Lauyan ɗangote, Ogwu Onoja ne, ya aike takardar janye ƙorafin. Ya janye ƙorafin ne bayan wata hukumar gwamnati ta ɗauki alhakin ci gaba da bincike game da zargin. A watan Disamban 2025 ne, ɗangote ya buƙaci ICPC ta binciki Ahmed kan zargin amfani da muƙaminsa wajen satar kuɗaɗen gwamnati. ɗangote ya ce yana da hujjoji da suka tabbatar…
Read More
Kungiyar Al’ummar Kawo a Kaduna ta gabatar da lakca kan cigaban al’umma da tsaro

Kungiyar Al’ummar Kawo a Kaduna ta gabatar da lakca kan cigaban al’umma da tsaro

Daga GAMBO ISA a Abuja An gudanar da lakca da bikin bayar da kyaututtuka na gargajiya na Kungiyar Cigaban Al'ummar  Kawo da ke Kaduna a makon da ya gabata a ɗakin taro na Ashanti da ke cikin Seventeen Hotel, Kaduna, inda aka haɗu da shugabannin gargajiya, wakilan gwamnati, jami'an tsaro, da masu ruwa da tsaki don tattauna batutuwan ci gaban al'umma, tsaro, da kuma zamantakewa. Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Galadiman Kawo, Alhaji Hassan Galadima, wanda ya wakilci Shugaban Gundumar Kawo; wakilin Kwamandan Sojojin Sama na Nijeriya, Sojojin Sama na Kaduna, Shugaban Rundunar Sojoji Umar; da…
Read More
Zuri’ar Madugun ƙosai ta gudanar da taronta na ƙasa a Kano

Zuri’ar Madugun ƙosai ta gudanar da taronta na ƙasa a Kano

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Zuri’ar Madugun ƙosai mai dogon tarihi, wadda ke da dubban mambobi a sassa daban-daban na Najeriya, ta gudanar da babban taron ta na ƙasa karo na bakwai a jihar Kano. Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Alhaji Balarabe Madugu Kabara, inda ya samu halartar ’ya’yan zuri’ar Madugu daga jihohi daban-daban na ƙasar nan. An gudanar da taron ne a Gidan Mallam Aminu Kano da ke Mumbayya, unguwar Gwammaja a Kano. Da yake jawabi a wajen taron, jagoran zuri’ar Madugun ƙosai Adakawa Kano ya bayyana cewa babban maƙasudin taron shi ne ƙarfafa zumunci da fahimtar juna…
Read More
Sabunta G.T.C Ungoggo: Gwamna Abba ya nuna kishin ilimi — UNTOBA

Sabunta G.T.C Ungoggo: Gwamna Abba ya nuna kishin ilimi — UNTOBA

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Kungiyar Tsofaffin ɗaliban Government Technical College (G.T.C) Ungoggo ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ware ɗaruruwan miliyoyin naira domin sabunta makarantar. Wannan yabo ya fito ne a yayin taron ƙungiyar na ƙasa da aka gudanar a harabar makarantar a makon da ya gabata, inda mambobin ƙungiyar UNTOBA suka bayyana matakin a matsayin hujja ta kishin ilimi. Da yake jawabi, ɗaya daga cikin tsofaffin ɗaliban makarantar, Alhaji Sulaiman Abdullahi (aji na 1987), ya ce G.T.C Ungoggo makaranta ce da ta shahara wajen fitar da ƙwararrun ɗalibai masu amfani ga Najeriya baki…
Read More
Gombe: Manoma sun koka kan yadda wata dorinar ruwa ke lalata musu amfanin gona

Gombe: Manoma sun koka kan yadda wata dorinar ruwa ke lalata musu amfanin gona

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wasu manoma da ke garin Hinna a ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba a jihar Gombe sun nuna damuwarsu game da wata dorinar ruwa da ke kai wa gonakinsu farmaki da takura wa rayuwarsu. Zakari Ladan, shi ne shugaban manoma a garin Hinna ya bayyana damuwarsu a yayin hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a ranar Litinin. Ladan ya ce harin da dorinar ruwan take kai musu ya jawo musu asara mai yawa, yana mai cewa suna yawan samun dabbobi suna lalata musu amfanin gona da barazana ga mazauna garin. Ya ce, yawan dorinar ruwan…
Read More
Yadda sojoji suka ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna

Yadda sojoji suka ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dakarun sojin Nijeriya da ke aiki a karkashin rundunar ‘Operation FANSAN YAMMA OPFY’ sun ceto mutum shida yayin da suke gudanar da ayyukkan su na samar da tsaro a yankin Kajuru zuwa Kujama dake ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna. Wata majiya mai tushe a rundunar sojin ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN cewa jami’an tsaron sun ceto wadannan mutane bayan rundunar Sub-sector 5 ta sanar da su harin da maharan ke yi a yankin da misalin karfe 9:30 na safe ranar 5 ga Janairu 2026. Majiyan ya shaida cewa jami’an tsaron…
Read More
2027: Matsayar ACF kan ‘yan takarar shugaban ƙasa ga Arewa

2027: Matsayar ACF kan ‘yan takarar shugaban ƙasa ga Arewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Nijeriya ACF, ta bayyana wasu tsare-tsare kan Arewa ga masu neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. ACF mai fafutukar kare muradun yankin arewaci ta ce ba za ta fito fili ta nuna goyon baya ga wani ɗantakarar shugaban ƙasa ɗaya ba a zaɓen 2027, kamar yadda Farfesa Tukur Muhammad-Baba sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar ya shaida wa BBC. Sai dai ya ce za su diba kudurorin 'yan takarar da manufofinsu da kuma alƙawuran da suka ɗauka. Ya ƙara da cewa nan da watanni masu zuwa ACF za ta gana…
Read More