ukarofi

12663 Posts
Matasa biyu sun shiga hannu kan yunƙurin yi wa fursunoni safarar wiwi a kotu

Matasa biyu sun shiga hannu kan yunƙurin yi wa fursunoni safarar wiwi a kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS), a Jihar Kano ta kama wasu matasa biyu bisa yunƙurin kai wa fursunoni miyagun ƙwayoyi a harabar Kotun Majistaren Nomansland. Matasan da aka kama su ne Usman Khalid mai shekara 25 da Bello Musa Ahmed mai shekara 24. Dukkaninsu mazauna Tsamiya ne da ke unguwar Brigade a Jihar Kano. Jami’an tsaron Gidan Gyaran Hali na Goron Dutse ne suka kama su yayin da suke ƙoƙarin jefa wa fursunoni tabar wiwi a cikin harabar kotun. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a Kano, CSC Musbahu Lawan…
Read More
Abin da ’yan Nijeriya ke buƙata a 2026

Abin da ’yan Nijeriya ke buƙata a 2026

Shekarun baya-bayan nan sun kasance masu cike da jarrabawa ga ’yan Nijeriya. Bayan zazzafar siyasar zaɓen 2023 da kuma ƙalubalen tsaro da tattalin arziki da suka biyo baya, shekarar 2025 ma ta zo da nata nauyin – daga hauhawar farashi, tsadar rayuwa, zuwa matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan. Yanzu da aka shiga shekarar 2026, al’umma na sa ran ganin sauyi na gaskiya, wanda zai tabbatar musu cewa dimokuraɗiyya da shugabanci na iya kawo sauƙi a rayuwarsu. Abu na farko da ke gabansu shi ne gyaran tsarin zaɓe. Duk da kiraye-kirayen da aka yi bayan babban zaɓen 2023,…
Read More
Yadda aka gudanar da taron ranar marubuta Hausa ta duniya a Jigawa

Yadda aka gudanar da taron ranar marubuta Hausa ta duniya a Jigawa

Daga IBRAHIM HAMISU a Jigawa Haɗakar ƙungiyar ƙungiyoyin marubuta ta Nijeriya ta gudanar da taron ranar marubutan Hausa ta duniya, da ya gudana a Jihar Jigawa, ranar Laraba 31 ga Disambar 2025. Taron wanda aka assasa shi domin al'amura da harkokin marubuta, da kuma bajekolin fasahohin marubuta da littattafai. Kabir Yusuf Anka shi ne mai magana da yawun babban kwamitin shirya taron, ya bayyana cewa manufar shirya taron shi ne sada zumunci da haɗuwa da juna da buɗe ido. Ya ce taron ya kasance ana tattaunawa rubuce-rubucen ƙagaggun labarai na Hausa da al'adu da harshe da tarihi duka na Hausawa.…
Read More
Waƙa: Ina muka dosa?

Waƙa: Ina muka dosa?

Daga BALA MUHAMMED GARBA 1.Rabbana yankin Arewa,    Kullu-yaumin ai kashewa,  Ba mu san usulin hakan ba. 2.     Rabbi an kashe Tajiranmu, Kuma an kashe Malamanmu,                Har Sarakai ba a bari ba. 3.   Makarantu an rufe su,  Kasuwanni an kashe su,  Me ya sa ba zan koka ba? 4. Ga shi an rusa tarbiyyarmu,    Kana an raba al'ummarmu, Ba mu san manufar hakan ba. 5. Yau da namu ake kashe mu,           Su ake sa sui satar mu,         Har kuɗin fansa su karɓa. 6.        Da a ce ba a kashe mu,  Babu wanda yake taɓa mu,      Da ba za nayi baitukan ba.…
Read More
Daga Labarawa Bahaushe ya aro amfani da ƙafiya – Khalid Imam

Daga Labarawa Bahaushe ya aro amfani da ƙafiya – Khalid Imam

"Waƙa saƙa ta ake yi kamar tabarmar kaba, shi kuma zube gina shi ake kamar yadda ake gida" Daga AISHA ASAS Shahararre kuma sanannen marubuci da ake alfahari da shi a duniyar Adabin Hausa Khalid Imam, ya samu damar amsa gayyatar jaridar Blueprint Manhaja inda masu karatu za su ji cikakken tarihi tare da nasarorin da ya samu a duniyar rubutu. An dai ce waƙa a bakin mai ita za ta fi zaƙi, ku biyo wakiliyar mu Aisha Asas don jin wane ne Khalid Imam. MANHAJA: Masu karatu za su so jin tarihinka. KHALID: Sunana Khalid lmam. An haife ni…
Read More
Tsohon daraktan DSS na ƙasa, Lawal Daura ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Katsina

Tsohon daraktan DSS na ƙasa, Lawal Daura ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Tsohon Darakta-Janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Lawal Daura, ya sanar da shirinsa na tsayawa takarar gwamnan Jihar Katsina a zaɓen 2027. Daura, ya soki yadda gwamnatin da ke kan mulki ke tafiyar da al’amura, tare da nuna matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar jihar a matsayin manyan dalilan da suka sa ya yanke shawarar shiga takarar. Da yake zantawa da manema labarai, Daura ya bayyana cewa ya kammala tuntuɓa kan burinsa na siyasa, kuma nan ba da jimawa ba zai bayyana jam’iyyar da zai tsaya a ƙarƙashin ta. Ya ce:…
Read More
APC ta yi zargin hana ‘yan jam’iyyar yin rajista a Zamfara

APC ta yi zargin hana ‘yan jam’iyyar yin rajista a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɓangaren Jam'iyyar APC na Hon. Aminu Sani Jaji a Jihar Zamfara sun yi Allah wadai da abin da suka bayyana a matsayin zargin hana 'yan jam'iyya 'yancin yin rijistar wata E-registration na APC da ke gudana a jihar. Alhaji Isyaka Ajiya Anka shugaban jam'iyyar APC mai suna a Jihar Zamfara ya yi wannan zargi a Gusau yau Laraba a wani taron manema labarai. A cewarsa, suna zargin tsohon Gwamna Abdulaziz Yari da Minista Bello Matawalle da shirya wannan yunƙurin hana sakataren shirye-shirye na Jihar Zama jami'in kula da yin rijistar, wanda hakan ya haifar da…
Read More
Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida a Katsina ya zama babban sakatare

Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida a Katsina ya zama babban sakatare

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da naɗin malam Tukur Ɗan Ali daga ƙaramar hukumar Ɗanmusa kuma shugaban ƙungiyar 'yan jarida ta ƙasa reshen jihar Katsina a matsayin babban sakatare tare da wasu mutane biyu. A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun shugaban ma'aikatan jihar Alhaji Falalu Bakake, sauran sun haɗa da Junaidu Muntari da Yahaya Abdullahi daga ƙananan hukumomin Ƙanƙara da Safana. Ya ce naɗin nasu an yi sh8 ne bisa cancanta inda ya ƙara da cewa sai da suka da suka sami nasarar zama jarabawar da makarantar Civil service institute ta shirya…
Read More
Gwamnatin Katsina ta ɗauki sabbin malamai 250

Gwamnatin Katsina ta ɗauki sabbin malamai 250

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta miƙa takardun kama aiki ga sabbin malamai da ma’aikatan gudanarwa, tare da takardun ɗaukar ɗalibai ga waɗanda aka ɗauka a sabbin makarantun sakandare (Model Secondary Schools) da ke Raɗɗa, Dumurkul da Jikamshi. Da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan ilimin firamare da sakandare, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia,ya buƙaci sabbin ma’aikatan da su nuna ƙwarewa, ladabi, jajircewa da bin ƙa’idojin aiki. Ya jaddada cewa an ɗauki ma’aikatan ne bisa cancanta, kuma an kafa makarantun domin zama cibiyoyin koyi da ingantaccen ilimi ga sauran makarantun gwamnati a faɗin jihar. Kwamishinan ya…
Read More
Karin aure a wurin malam bahaushe (2)

Karin aure a wurin malam bahaushe (2)

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, Allah Ya sa mu dace da rahmar duniya da ta lahira. A makon da ya gabata, mun fara kwararo bayani kan ƙarin aure, inda muka soma da bayanin halaccin yin mace fiye da ɗaya, zuwa inda muka soma bayani akan ababen da ya kamata a yi dubiya kafin a ƙara aure. Mun kawo ƙarfin aljihu a matsayin ɗaya daga cikin ababen da ya kamata a yi dubiya kansu kafin ƙarin aure, kasancewar ci da sha da kuma muhalli yana wuyan miji. Abu na biyu, wanda za mu soma…
Read More