Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɓangaren Jam’iyyar APC na Hon. Aminu Sani Jaji a Jihar Zamfara sun yi Allah wadai da abin da suka bayyana a matsayin zargin hana ‘yan jam’iyya ‘yancin yin rijistar wata E-registration na APC da ke gudana a jihar.
Alhaji Isyaka Ajiya Anka shugaban jam’iyyar APC mai suna a Jihar Zamfara ya yi wannan zargi a Gusau yau Laraba a wani taron manema labarai.
A cewarsa, suna zargin tsohon Gwamna Abdulaziz Yari da Minista Bello Matawalle da shirya wannan yunƙurin hana sakataren shirye-shirye na Jihar Zama jami’in kula da yin rijistar, wanda hakan ya haifar da damuwa game da makomar tabbatar da adalci da kuma haɗin kai.
Ya zargi tsohon Gwamna Abdulaziz Yari da ministan tsaro Hon. Bello Matawalle da hana Bashir Ahmad sakataren shirye-shiryen jam’iyyar na Jiha a Jihar Zamfara shiga cikin shirin yin rijistar E-registration na membobin APC da ke gudana.
Ya bayyana cewar suna zargin cewa wannan wariya ta shafi jiha, ƙananan hukumomi da matakan mazaɓu, waɗanda suka kasance cikin shirye-shiryen raba kashi 40% a lokacin taron APC na ƙarshe lokacin da Matawalle ya koma Jam’iyyar APC.
Anka ya ƙara da cewa akwai fargabar cewa ana yin rijistar na membobin jam’iyyar ta hanyoyin da suka saɓawa dokar jam’iyyar musamman hana sakataren shirye-shiryen jam’iyyar na Jihar Zamfara Bashir Ahmed ya jagoranci gudanar da yin rijistar.
Ya yi zargin cewa haɗin gwiwa tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Abdulaziz Yari, da Ministan Tsaro Bello Matawalle, da Sakataren shirye-shiryen jam’iyyar na ƙasa ne yasa aka bayar da umarnin kada a yi musu rijista a cikin shirin yin rijistar na APC da ke gudana a jihar.
“Wannan lamarin ya haifar da damuwa game da adalci, haɗin kai da kuma sahihancin aikin yin rijistar, wanda hakan ka iya barazana ga haɗin kan jam’iyyar kafin ayyukan da ke tafe”.
Ya yi kira ga hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa da ta binciki tsarin yin rijistar na membobin APC a Jihar Zamfara domin gano kurakurai, ciki har da, idan ya cancanta, rushewa ko sake daidaita tsarin shugabancin gudanar da yin rijistar a tabbatar da shi cikin gaggawa.
“Hedikwatar APC ta ƙasa ta ɗauki ƙa’idodi masu muhimmanci da hanyoyin sa ido don tabbatar da adalci da bin ƙa’idodin jam’iyyar ta APC da dokokin da suka dace wajen gudanar da yin rijistar ga ɗaukacin mambobin jam’iyyar”.
Anka ya ce, suna ci gaba da jajircewa wajen bin doka, haɗin kai, da kuma ɗaukar matakin da ya dace, Yana mai jaddada cewar manufar ita ce dawo da aminci da ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya na jam’iyyar ta APC.
