07
Jan
Daga AISHA ASAS Masu bibiyar Manhaja sannunku da ƙoƙari, barkanmu da sake kasancewa da ku a shafin Kwalliya. A yau zamu tattauna ne kan tasirin kitso da lalle a kwalliya. Saidai kafin nan, za mu fara da matsayin kitso da lalle a ƙasar Hausa. Idan muka fara da lalle, za mu iya cewa, ba za mu kira shi a matsayin al'ada kawai ba, kamar yadda na ji wani hadisi, wanda ba zan iya faɗar sahihancinsa ba, ya yi bayyanin yadda lalle yake sunnah, kasancewar Manzon rahma (S.A.W) ya ba wa wani umurnin saka lalle a lokacin da ya yi aure.…
