ukarofi

12663 Posts
Gwajin ƙarshen shekara kan ƙoƙarin Bichi da ƙudirin Tinubu na samar da abinci

Gwajin ƙarshen shekara kan ƙoƙarin Bichi da ƙudirin Tinubu na samar da abinci

Daga SHEHU MUSTAPHA CHAJI Engr. Dr. Rabiu Suleiman Bichi shugaban hukumar raya kogunan Hadejia da Jama'are, Kano da manyan daraktocin hukumar da suka haɗa da Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso babban daraktan kuɗi da Alhaji Tijjani Isa babban daraktan tsare tsare da Hajiya Zainab Gamawa babban daraktan noma da Engr. Datti Abdulkadir babban daraktan Injiya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa su kan muƙaman su ranar 18 ga Disamba 2024 suka kama aiki ranar 18th Afrilu - 2025. Hukumar raya kogunan Hadejia da Jama'are kamar sauran hukumomin raya koguna, ma'aikatu ne na Gwamnatin Tarayya da suke da alhakin kulawa da…
Read More
‘Yan majalisa sun buƙaci a jingine sabuwar dokar haraji

‘Yan majalisa sun buƙaci a jingine sabuwar dokar haraji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar wakilan Nijeriya  ta buƙaci gwamnatin tarayya ta jingine shirinta na fara aiwatar da sabuwar dokar haraji mai cike da ce-ce-ku-ce da ruɗani, har sai an kammala bincike kan zargin sauya wasu daga cikin dokokin da majalisar ta amince da su. ɓangaren marasa rinjaye a majalisar sun bayyana bukatar dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji domin gudanar da bincike mai inganci, wanda majalisar ta kafa don gano gaskiyar batun. Wannan kiran ya biyo bayan zargin cewa an sauya wasu sassa na dokokin haraji bayan da majalisar ta amince da su, wanda hakan ya…
Read More
Gwamna Mutfwang ya sauya sheƙa zuwa APC

Gwamna Mutfwang ya sauya sheƙa zuwa APC

Daga HABU ƊAN SARKI, a Jos Gwamnan Jihar Filato Caleb Manasseh Mutfwang ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC a hukumance, bayan raɗe-raɗin da aka riƙa yi a baya. Cikin rakiyar da ɗaruruwan magoya bayansa da wasu muƙarrabansa daga cikin gwamnati, Gwamnan ya sanar da komawarsa Jam'iyyar APC ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da aka gudanar a Jos. Gwamnan wanda tun da farko ya sanar da fitarsa daga Jam'iyyar PDP awa ashirin da huɗu kafin ya koma jam’iyyar APC, ya ce ya yi haka ne domin kawo wa jihar Filato cigaba. A wata sanarwa da kakakin…
Read More
Adamawa: Shugaban ƙaramar hukuma ya nemi a tura sojoji bayan Boko Haram sun halaka mutane 14

Adamawa: Shugaban ƙaramar hukuma ya nemi a tura sojoji bayan Boko Haram sun halaka mutane 14

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla mutane 14 ne aka halaka a wani mummunan harin da mayaƙan Boko Haram suka kai wa wasu ƙauyuka biyu a Ƙaramar Hukumar Hong da ke Jihar Adamawa, lamarin da ya janyo sabunta kiraye-kirayen ƙarfafa dakarun sojoji a yankin. Shugaban ƙaramar hukumar, Usman Inuwa ya tabbatar da faruwar al'amarin a yau Junairun, yana mai cewa maharan sun kai farmaki ne a ƙauyukan Mubang da Zar a ɗaya daga cikin dararen makon da ya gabata. A wata hira da manema labarai ta salula, Inuwa ya ce da misalin ƙarfe 9 na dare mayaƙan suka kai…
Read More
Tinubu ya jinjina wa Hadiza Bala Usman a zagayowar ranar haihuwarta

Tinubu ya jinjina wa Hadiza Bala Usman a zagayowar ranar haihuwarta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai Girma Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Hadiza Bala Usman, wato mai ba sa shawara na musamman akan tsare-tsaren harkokin gwamnati kuma Shugabar Cibiyar Isar da Sakamakon Tsare-tsare (CRDCU) bisa gagarumar gudumawarta ga hidimar ƙasa yayin da take cika shekaru 50 a duniya. A wata sanarwa da Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana Hadiza a matsayin "jajirtacciyar mai kishin ƙasa" wadda aikinta na kusan shekaru 30 a gwamnati ya zama abin misali ga al'umma sakamakon sadaukarwa da himmarta ga ci-gaban ƙasa. Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa ƙoƙarinta…
Read More
Gwamnan Bauchi ya zargi Wike da yunƙurin kitsa faɗuwarsa

Gwamnan Bauchi ya zargi Wike da yunƙurin kitsa faɗuwarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani sabon rikici ya kunno kai yayin da Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi a ranar Alhamis ya zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike da yunƙurin ɓata masa suna da lalata mutuncinsa a idon jama'a a siyasance. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin a wata hira da da gidan talabijin na Channels, inda ya ce ana jifan sa da wasu zarge-zarge marasa tushe ciki har da alakanta shi da batun ta’addanci da ‘yan bindiga, lamarin da ya musanta. A cewarsa, Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewa maso…
Read More
Amurka ta fi Nijeriya haɗarin zama, inji mawaƙin Amurka DDG

Amurka ta fi Nijeriya haɗarin zama, inji mawaƙin Amurka DDG

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mawaƙin Amurka Darryl Dwayne Granberry Jr. da aka fi sani da DDG, ya bayyana farfagandar kafafen watsa labaran ƙasashen yammacin duniya akan Nijeriya a matsayin "bogi". Tauraron na 'Hip-hop', wanda a yanzu yake hutu a Legas, ya ce saɓanin farfagandar 'yan Yamma, Nijeriya ba ta yi kusa da Amurka ba wajen zama haɗari ga al'umma. DDG ya kuma roƙi 'yan ƙasashen waje da su ziyarci Nijeriya domin gane wa idanunsu ko akwai gaskiya akan abin da ake yaɗawa game da Nijeriya. Da yake jawabi yayin wata hirar bidiyo, mawaƙin Amurkan ya ce: " A…
Read More
Gwamnatin Katsina ta karɓi mabarata 11 da aka maido daga Abuja

Gwamnatin Katsina ta karɓi mabarata 11 da aka maido daga Abuja

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan raya Karkara da kyautata rayuwar al'umma Farfesa Abdulhamid Ahmed ne ya karɓi mutanen a hannun wakilan hukumomin Abuja da suka maido su, a madadin Gwamnatin Jihar Katsina. An dai maido mutanen ne a ƙarƙashin Shirin tsaftace birnin tarayya Abuja mai suna "Operation Sweep Abuja" wanda ministan Abuja Nyesom Wike ya ƙirƙiro da shi. Mutanen su 11 sun ƙunshi maza biyar sai mata su shida, kuma daga cikin su akwai ƙananan yara ya'yan wasu daga cikin matan. Da yake jawabi a lokacin da yake karɓar mutanen, Farfesa Abdulhamid Ahmed ya ce, waɗanda aka maido yan…
Read More
‘Yan sanda sun kama direban Anthony Joshua sa’o’i bayan fitowarsa daga asibiti

‘Yan sanda sun kama direban Anthony Joshua sa’o’i bayan fitowarsa daga asibiti

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Direban motar Lexus SUV da ta yi hatsarin da ya rutsa da tsohon zakaran dambe na duniya, Anthony Joshua, ya shiga hannun hukumar ƴan sanda. Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Ogun, Oluseyi Babaseyi ya tabbatar da haka a ranar Alhamis cikin wata sanarwa da ya aike w manema labarai. A daren ranar ne aka sallamo Joshua daga Asibitin Lagoon da ke garin Ikoyi a Jihar Legas bayan likitoci sun gano ya cancanci cigaba da jinya a gida. Joshua, wanda ɗan asalin Nijeriya ne, na cikin motar tare da abokai biyu a lokacin da suka…
Read More
An zargi Gwamnan Bauchi da biyan miliyan $9.7 don ɗaukar nauyin ta’addanci 

An zargi Gwamnan Bauchi da biyan miliyan $9.7 don ɗaukar nauyin ta’addanci 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta danganta Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci da ya kai kimanin dala miliyan 9.7. A ranar Laraba, Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon ƙasa (EFCC), ta gurfanar da Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, tare da wasu mutum uku a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja. Ana zarginsu da haɗa baki wajen karkatar da kuɗin gwamnati da kuma amfani da kuɗin wajen ɗaukar nauyin ta’addanci. Sauran waɗanda ake tuhuma sun haɗa da Balarabe Abdullahi Ilelah, Aminu Mohammed Bose da Kabiru Yahaya Mohammed.…
Read More