02
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa daga yanzu ba wanda zai ƙara kiran ‘Almajirai’ da yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar Jigawa, saboda za a fara koya musu lissafi da koyon karatu da rubutu da koya musu kasuwanci daidai da na waɗanda suke zuwa makarantar boko. Almajirai dai yara ne da ake turo su domin zuwa koyon karatun Alƙur’ani inda suke zama a wurin malamansu. Sai dai mafi yawan irin yaran kan ƙare ne a kan titi suna bara a yayin da wasu ke aikta ƙananun laifuka. Wannan abu ne da ake…
