ukarofi

12663 Posts
An samu zaman lafiya a Katsina, inji Gwamna Raɗɗa 

An samu zaman lafiya a Katsina, inji Gwamna Raɗɗa 

Daga UMAR GARBA a Katsina  Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, ya tabbatar wa mazauna jihar gagarumin ƙudIrin gwamnatinsa na samar da shugabanci mai inganci a cikin sabuwar shekarar 2026.  A cikin saƙonsa na sabuwar shekara, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa shekarar 2026 za ta kawo ci gaba mai yawa, zaman lafiya mai ɗorewa da kuma ci gaban jihar baki ɗaya. Gwamnan ya bayyana cewa zaman lafiya yana dawowa sannu a hankali a Jihar Katsina bayan ƙoƙarin gwamnati, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a jihar. "Wasu daga cikin ƙananan hukumominmu da ke kan gaba a…
Read More
Na janye ƙararrakin ɓatanci da na shigar saboda wa’azin da na ji, inji Akpabio

Na janye ƙararrakin ɓatanci da na shigar saboda wa’azin da na ji, inji Akpabio

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bayar da umarni ga lauyoyinsa su janye duk ƙararrakin ɓatanci da ya shigar a kotu kan mutane daban-daban, ciki kuwa har da Sanata Natasha Akpoti, yana mai cewa, wa’azin da ya saurara a yayin taron sabuwar shekara ne ya ratsa shi ya ɗauki wannan mataki. Akpabio ya bayyana hakan ne a cocin Sacred Heart Parish da ke Uyo a ranar Alhamis, inda ya ce a wancan lokaci yana da kusan ƙararraki tara a kotu a kan mutanen da ya zarga da ɓata masa suna. A cewarsa, ya shigar…
Read More
Naira 100,000 aka biya ni na kai harin bom masallacin Borno, inji wanda ake zargi

Naira 100,000 aka biya ni na kai harin bom masallacin Borno, inji wanda ake zargi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani mutum da ake zargin ɗan Boko Haram ne, Ibrahim Mohammed, ya amsa cewa an biya shi kuɗi har naira 100,000 domin kai harin bom a wani masallaci da ke Maiduguri, Jihar Borno, tare da masu ibada a cikinsa. Maganar ta fito ne a ranar Laraba ta bakin masani kan yaƙin da ake yi da ta’addanci, Zagazola Makama, a shafinsa na ɗ, inda ya ce majiyoyin tsaro sun tabbatar masa da kama Ibrahim ta hannun dakarun Operation Haɗin Kai tare da taimakon mafarauta na gargajiya a Jihar Yobe. A cewar majiyoyin, Ibrahim ya amsa rawar da…
Read More
An kama fasto a Ghana kan ayyana duniya za ta ƙare a ranar 25 ga Disamba

An kama fasto a Ghana kan ayyana duniya za ta ƙare a ranar 25 ga Disamba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar 'yan sandan Ghana ta tabbatar da kama Evans Eshun, wanda aka fi sani da Ebo Noah, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin sa ido da magance ayyukan da suka shafi yanar gizo a gabanin ibadar addini ta dare na 31. Tawagar tantance bayanai ta musamman ta Sufeto Janar na 'yan sanda, wacce aka kama a wajen, ta bayyana a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin yanar gizon 'yan sanda a ranar Laraba. Ko da yake sanarwar ta tabbatar da kamawar, ba ta bayyana takamaiman zarge-zargen da ake yi wa Eshun ko…
Read More
Mun ci ribar Naira biliyan 502 a wata ɗaya – NNPCL

Mun ci ribar Naira biliyan 502 a wata ɗaya – NNPCL

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPCL) ya bayyana cin ribar Naira biliyan 502 a watan Nuwamba 2025, duk da raguwar samar da ɗanyen mai a watan. Hakan ya zo ne a daidai lokacin da kamfanin na gwamnati ya shiga gasar rage farashin man fetur a kasuwar, inda ya rage farashin litar man zuwa ƙasa da N800. Rahoton kuɗi da ayyukan NNPC na watan Nuwamba 2025, wanda aka fitar a ranar Laraba, ya nuna cewa kamfanin ya samu kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 4.36 a cikin watan, wanda ya ɗan ɗara na watan Oktoba. An…
Read More
Gwamnan Bauchi ya zargi gwamnatin Tinubu da amfani da EFCC don tilasta wa ‘yan adawa komawa APC

Gwamnan Bauchi ya zargi gwamnatin Tinubu da amfani da EFCC don tilasta wa ‘yan adawa komawa APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da zargin amfani da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) don cin zarafi da tsoratar da shugabannin adawa a faɗin ƙasar. Mohammed ya yi wannan zargin ne a ranar Laraba a Bauchi yayin da yake magana cikin yanayi mai ratsa zuciya bayan ya samu kyautar Jakadan Tsaro daga Cibiyar ƙwararrun Tsaro ta Nijeriya (ISPON). Gwamnan ya yi iƙirarin cewa Gwamnatin Tarayya da APC ke jagoranta tana cin zarafin cibiyoyin gwamnati, ciki har da kotuna da hukumomin yaƙi da…
Read More
Yahaya Bello ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata a Kogi ta tsakiya

Yahaya Bello ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata a Kogi ta tsakiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Kogi ta tsakiya a zaɓen 2027 mai zuwa. Bello ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai fadar Ohinoyi na Ebiraland, inda ya gana da sarakunan gargajiya, malaman addini da masu ruwa da tsaki na yankin majalisar dattawa. An yaɗa bidiyon ziyarar da kuma bayaninsa a shafin Facebook mai tabbatar da Bello a ranar Litinin. "Na yarda in tsaya takarar majalisar dattawa a 2027," inji tsohon gwamnan yayin da yake jawabi a wurin taron. Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman…
Read More
An kashe manoma bakwai a sabon harin ‘yan bindiga a Filato

An kashe manoma bakwai a sabon harin ‘yan bindiga a Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Aƙalla manoma bakwai ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai ƙauyen Bum na gundumar ɓwang da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato. Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren Laraba, lokacin da yawancin mutanen ƙauyen ke barci. A ranar Alhamis, mai magana da yawun ƙungiyar matasan Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an riga an gano gawarwakin waɗanda suka mutu, yayin da ake ci gaba da bincike da aikin ceto a yankin. A cewarsa,…
Read More
Kwato dazuka daga hannun ’yan ta’adda

Kwato dazuka daga hannun ’yan ta’adda

Sanarwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi cewa daga yanzu ’yan fashi, masu garkuwa da mutane, ƙungiyoyin daba da duk wasu masu riƙe da makamai za a riƙa ɗaukarsu a matsayin ’yan ta’adda, alama ce ta sabon salo a tsarin tsaron Nijeriya. Wannan matsaya, da aka bayyana yayin gabatar da kasafin kuzin shekarar 2026, ta zo ne tare da shirin tura jami’an tsaron gangun daji sama da 7,000 a jihohi bakwai, wato Borno, Sakkwato, Yobe, Adamawa, Neja, Kwara da Kebbi zuwa cikin dazuka. Tambayar da ke yawo a zukatan ’yan Nijeriya ita ce: shin wannan sabon tsari zai yi nasara…
Read More
Hajjin 2026: NAHCON ta buƙaci a bi sahihan matakan gwajin lafiya

Hajjin 2026: NAHCON ta buƙaci a bi sahihan matakan gwajin lafiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta jaddada tsattsauran matakan da aka ɗauka na tantance lafiyar maniyyata a yayin aikin Hajjin 2026, inda ta yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci rashin cika ƙa’idojin kiwon lafiya da ƙasar Saudiyya ta gindaya ba. Hukumar ta jaddada wannan mataki ne a yayin zaman da ta yi da jami’an tawagar lafiya daga jihohin Nijeriya wanda ta yi a Abuja a ranar Talata. A yayin zaman, wanda Manhaja ta bibiya, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya ce, lallai ne a cika dukkan ƙa’idojin lafiya da Saudiyya ta shar'anta. Shugaban…
Read More