ukarofi

12663 Posts
Sanatan Nasarawa, Godiya Akwashiki ya rasu

Sanatan Nasarawa, Godiya Akwashiki ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanatan da ke wakiltar Jihar Nasarawa ta Arewa a Majalisar Dattawan Nijeriya, wato Godiya Akwashiki, ya rasu a ranar Alhamis a wani asibitin ƙasar Indiya bayan shafe shekaru 52 a duniya. Rahotanni sun bayyana cewa Sanatan ya yi fama da wani rashin lafiya ne ne ɗan wani lokaci, wanda hakan ya sa aka garzaya da shi Indiya domin neman magani. A ranar 3 ga watan shekarar 1973 ne aka haifi Akwashiki a garin Angba Igga da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa Eggon ta jihar. Ya kuma riƙe muƙaman jagoran mafiya rinjaye da mataimakin kakakin majalisar…
Read More
Monoma 75,000 za su amfana da shirin SAPZ a Kano

Monoma 75,000 za su amfana da shirin SAPZ a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Aƙalla manoma 75,000 daga ƙananan hukumomi 16 na Jihar Kano ake sa ran za su amfana da shirye-shiryen inganta abinci mai gina jiki ta hanyar noma a ƙarƙashin shirin Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ), wani babban shirin gwamnatin tarayya da ke samun tallafi daga Bankin Raya Afirka (AfDB), IFAD, Bankin Raya Musulunci, da sauran abokan hulɗa na ci gaba. An bayyana hakan ne a ranar Laraba a Kano wanda ƙwararre a harkar sadarwa na shirin, Malam Shehu Babangida, yayi a wani taron horaswa na kwana guda ga kafafen yaɗa labarai kan Sauya halayen al’umma (BCC)…
Read More
Gwamnan Filato ya fice daga PDP

Gwamnan Filato ya fice daga PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance, lamarin da ya kawo ƙarshen dogon zangon da ya yi acikinta da kuma nuna sabuwar alƙiblar siyasa a jihar. Bayanin hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 29 ga Disamba, 2025, wanda ya aike wa Shugaban jam’iyyar na Gundumarsa ta Ampang ta Yamma a Ƙaramar Hukumar Mangu, wato Dasjak Sunday Longyol. Saidai, Gwamna Mutfwang bai bayyana cikakken dalilinsa na ficewar ba, amma ya nuna cewa hakan ya yi daidai da burinsa na cigaba da yi wa al'ummar…
Read More
Gwamnan Kano ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na Naira tiriliyan 1.47

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na Naira tiriliyan 1.47

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan dokar kasafin kuɗin shekara ta 2026 da ta kai naira tiriliyan 1.47, wadda ke kafa tubalin aiwatar da shirye-shiryen ci gaban jihar a shekarar kuɗi mai zuwa. Gwamnan ya amince da kasafin kuɗin ne a ranar Laraba, yayin wani taron majalisar zartarwa ta Jihar Kano da aka gudanar a Kano. Dokar kasafin kuɗin, wadda ta kai ₦1,477,829,666,131, majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da ita a makon da ya gabata, a zaman majalisa da Kakakin Majalisar, Alhaji Ismail Falgore, ya jagoranta. An zartar da ƙudirin…
Read More
An sallami Anthony Joshua daga asibiti bayan jinyar sakamakon hatsarin mota

An sallami Anthony Joshua daga asibiti bayan jinyar sakamakon hatsarin mota

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An sallami zakaran gasar damben duniya, Anthony Joshua daga asibiti bayan wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a babban titin Legas zuwa Ibadan ranar Litinin, wanda ya yi sanadin mutuwar abokansa biyu, wato Lateef Ayodele da Cin Gami. A wata sanarwar haɗaka daga Gbenga Omotosho, wanda shi ne Kwamishinan Labarai na Jihar Legas da Mai bada Shawara akan Harkar Labarai na Jihar Ogun, Kayode Akinmade, gwamnatocin jihohin biyu sun miƙa ta'aziyyarsu ga iyalan mamatan. Sun kuma yi musu addu'ar samun rahama tare da fatan juriya ga iyalansu bisa rashin nasu. Sannan,…
Read More
Gwamnatin Katsina ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki akan tsaro

Gwamnatin Katsina ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki akan tsaro

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal Joɓe da ya jagoranci taron da ya gudana a ɗakin taro na fadar gidan gwamnatin jihar. Taron ya haɗa shugabannin hukumomin tsaro na jihar, shugabannin ƙananan hukumomi , da kuma wakilan rundunar Sojin Nijeriya, Hedikwatar Tsaro (Defence Headquarters), hukumar DSS, Rundunar ’Yan Sanda , hukumar shige da fice, hukumar NSCDC, hukumar Kwastam, da hukumar kiyaye haɗurra ta hanya (FRSC). Haka kuma, sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Faskari; kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro , Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa; Kwamishinar Shari’a, Barrista Fadila Mohammed Dikko; tare da manyan shugabannin addini sun…
Read More
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya aike da saƙon shiga sabuwar shekarar 2026

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya aike da saƙon shiga sabuwar shekarar 2026

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Gutteres ya yi kira mai ƙarfi yayin da ake shiga sabuwar shekara (2026), yana gargaɗin cewa duniya tana tsaye a mashigin hanya. Ya ce: “Yayin da muke shiga sabuwar shekara, duniya tana tsaye a kan mashigin hanya. Rikice-rikice da rashin tabbas sun kewaye mu. Rarrabuwar kawuna. Tashe-tashen hankula. Lalacewar yanayi. Da kuma take hakkin dokokin kasa da kasa. An fara ja da baya daga ka’idojin da ke hada mu a matsayin ɗan Adam. "Mutane a ko’ina suna tambaya: Shin shugabanni suna sauraro kuwa? Shin sun shirya ɗaukar…
Read More
Bambancin da ke tsakanin Hikayata da sauran gasa tamkar jami’a ce da kwaleji – Hafsat Sani Tanko 

Bambancin da ke tsakanin Hikayata da sauran gasa tamkar jami’a ce da kwaleji – Hafsat Sani Tanko 

Gasar Hikayata ita ce babbar gasar da babu kamar ta - Fadila Lamiɗo  Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  A bana Gasar Hikayata ta marubuta mata zalla da tashar BBC Hausa ta saba gabatarwa duk shekara ta cika shekara goma. A kowacce shekara kamar yadda muka saba gani, mata marubuta daga sassan duniya daban-daban, inda ake da Hausawa ko masu amfani da harshen Hausa, suna aikawa da labaransu, domin neman shiga gasar ƙirƙirarrun gajerun labarai ta Hikayata. A ƙarshen gasar ana fitar da gwaraza uku da labaransu suka yi fice, tare da jinjina ga rukuni na biyu na mutane goma sha biyu…
Read More
Waƙa: Littafin Tarihin Buhari 

Waƙa: Littafin Tarihin Buhari 

Daga MUHAMMED BALA GARBA 1. Tarihi dai adali ne,               Ba shi yin ƙarya gare ka. 2. Ba shi ƙage ba shi ƙwange,            Kar ka ce ya sammace ka. 3. Tarihi shi ne madubin,           Na dukan wani sha'aninka. 4. Tarihi dai gaskiya ne,              Zai faɗo duka lamarinka. 5. Ya ka rayu da 'yan uwanka,         Har zuwa gun kwanciyarka. 6. Tarihi duka zai bayani,          Aiyukan duka da ka shuka. 7. Ko idan ka ɓoye kalma,        Za ta bayyana babu shakka. 8. Tarihi tamkar Raƙibu,                 Da Atidu suke gare ka. 9. Duka aikhairan da ka yo,           Har da sharri za ya haska. 10.…
Read More
Wane ne Adolf Hitler kuma me ya sa ya yaƙi duniya?

Wane ne Adolf Hitler kuma me ya sa ya yaƙi duniya?

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An aifi Adolf Hitler ranar 20 ga watan Afirilu na shekara 1889, ya kashe kansa ranar 30 ga watan Afirilu na shekara 1945 bayan an ci Jamus da yaki. An aifi Adolf Hitler ranar 20 ga watan Afrilu na shekara 1889 wato shekaru 122 kenan da suka gabata. An aife shi a wani gari mai suna Braunau-am Inn, a ƙasar Austriya kusa da iyakar ƙasar da Jamus. Shi ne na huɗu a gidansu. Mahaifinsa wani jami'in Custum ne, ya rasu a yayin da Hitler ke da shekaru 14 da aihuwa. Marubuta tarihin Hilter sun ce bai…
Read More