Gwamnatin Katsina ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki akan tsaro

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal Joɓe da ya jagoranci taron da ya gudana a ɗakin taro na fadar gidan gwamnatin jihar.

Taron ya haɗa shugabannin hukumomin tsaro na jihar, shugabannin ƙananan hukumomi , da kuma wakilan rundunar Sojin Nijeriya, Hedikwatar Tsaro (Defence Headquarters), hukumar DSS, Rundunar ’Yan Sanda , hukumar shige da fice, hukumar NSCDC, hukumar Kwastam, da hukumar kiyaye haɗurra ta hanya (FRSC).

Haka kuma, sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Faskari; kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro , Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa; Kwamishinar Shari’a, Barrista Fadila Mohammed Dikko; tare da manyan shugabannin addini sun halarci taron.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan duba halin tsaro na baya-bayan nan, magance ƙalubalen da ke ci gaba da wanzuwa, da kuma ƙarfafa dabaru domin inganta tsaro, zaman lafiya, da ci gaban Jihar Katsina.

A ɗauki tsawon lokaci ba a sami rahoton hare haren yan bindiga a faɗin jihar hakan kuwa ya biyo bayan zaman sasanci da ta Yan bindiga a ƙananan hukumomin da sukai ta fama da ta’addanci.

By ukarofi