Makarantun tsangaya: Mun yi wa almajirai gata, inji Gwamna Namadi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa daga yanzu ba wanda zai ƙara kiran ‘Almajirai’ da yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar Jigawa, saboda za a fara koya musu lissafi da koyon karatu da rubutu da koya musu kasuwanci daidai da na waɗanda suke zuwa makarantar boko.

Almajirai dai yara ne da ake turo su domin zuwa koyon karatun Alƙur’ani inda suke zama a wurin malamansu. Sai dai mafi yawan irin yaran kan ƙare ne a kan titi suna bara a yayin da wasu ke aikta ƙananun laifuka. Wannan abu ne da ake samun sa a jihar Jigawa da mafi yawan jihohin Arewacin Nijeriya.

A yayin da yake magana a ranar Litinin a lokacin da yake tattaunawa da malaman tsangaya, Namadi ya ayyana sabon tsarin gyara harkar karantar da Alƙur’ani a jihar.

“Ina son mutane su fashimci cewa Almajirai ba yara ne da ba sa zuwa makaranta ba; Almajirai yara ne da ke zuwa makaranta kuma ɗalibai,” ya bayyana.

“Wannan ne ya sa na yanke shawarar inganta tsarin karatun, kuma da haɗin kanku, insha Allah, za mu dawo da martabar wannan tsari na koyo,” ya shaida wa malaman a yayin taron.

Gwamnan ya bayyana tattaunawar a matsayin wata nasara da aka taɓa samu a babban mataki irin wannan da ya haɗa da shugabanni kamar mataimakin gwamnan jihar da ‘yan majalisar dokokin jihar waɗanda suka tattauna da malaman Alƙur’ani ta nayar hukumar kula da ilimin Tsangaya.

A ƙarƙashin tsarin, Namadi ya ce, za a kawo sauyi a makarantun Tsangaya yadda za su koma makarantu masu koyar da abubuwa da yawa da manhajar karatu da zai haɗa da: haddar karatun Alƙur’ani da lissafi da koyar da rubutu da karatu da sana’o’in hannu domin tabbatar da dogaro da kai.

“Burinmu shi ne da zarar yaro ya kammala matakin farko, zai samu shaidar karatu. Haka ma a matakin karatun Alƙur’ani da yardar Allah,” gwamna Namadi ya bayyana.

Gwamnan ya amince cewa akwai babban aiki a gaba. Ya ce, jihar Jigawa na da makarantun Tsangaya guda 4,000 da yara sama da miliyan 1.3 — yawan yaran da ya haura na ɗaliban da ke zuwa makarantar boko a jihar.

Domin tallafa wa wannan tsari, gwamnan ya ce tuni aka bai wa malaman Alƙur’ani 100 horo da shaida tare da haɗin guiwar hukumar kula da karatun addinin Musulunci da ilimin Arabiyya ta ƙasa (NBAIS).

Ta ƙara da cewa jihar na da tunanin ɗaukar ƙarin malamai 500 ga makarantun Tsangaya a cikin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026 da kuma shigar da ilimin tsangaya cikin tsarin kasafin kuɗi na dindindin na jihar domin kaucewa yin watsi da yaran da suka kai miliyan 1.3.

Abubakar Hamisu, babban sakataren hukumar Tsangaya ya yi ƙarin haske kan shirin kawo ƙarshen barace-barace. Ya ce tuni shirin ya ceto yara 2,000 da ke yawo a kan titi tare da shigar da sa su a makarantun Tsangaya mallakin gwamnatin jihar Jigawa da ke manyan biranen Dutse, Hadejia da Gumel.

Jigawa ta daɗe tana zama kan gaba wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya . Yawanci dai, ana tattara alƙaluman yaran da ba sa zuwa makaranta ne ta la’akari da waɗanda suke zuwa makarantar boko. Don haka, saboda Almajirai suna zuwa makarantun Tsangaya da ake ganin ba su da tsarin manhajar karatu da kuma ganinsu a kan titi suna bara, shi ya sa ake ayyana su a matsayin waɗanda ba sa zuwa makaranta.

Wasu alƙaluma na baya-bayan nan kamar wanda asusun tallafa wa yara (UNICEF) ta fitar ya nuna jihar jigawa ce take da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya .

Sai dai ba tare da samun tallafin gwamnati ba, mafi yawan yaran da ke zuwa makarantun Tsangaya (Almajiri) sukan hau kan titi ne suna bara wanda ke sa wa su zama abin amfani ta munanan hanyoyi cikin sauƙi da kuma rashin samun ingantaccen tattalin arziƙi gaba a rayuwarsu.

Gwamna Namadi ya ce, gwamnatinsa na son cike wannan giɓi ne ta hanyar kawo ƙarshen tsohon tsarin ta hanyar shigo da su tsari na gwamnati.

Kuma ta hanyar koya musu sana’o’i da darusa na ilimin zamani, jihar na fatan maishe da yaran su zama masu amfanar da al’umma da dogaro da kansu a nan gaba.

By ukarofi