26
Dec
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta bayyana cewa, Kamfanin Man Fetur na ƙasa wato NNPC, tare da wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya guda 12, sun kasa cika ƙa’idojin ɗa’a da gaskiya, bayan da suka samu maki sifili a sabon rahoton tantance gaskiya da nagartar aiki da hukumar ta fitar.Rahoton, wanda ICPC ta wallafa a ranar Laraba kuma aka samu kwafinsa, ya nuna sakamakon tantancewar da aka yi wa hukumomi 357 na gwamnatin tarayya a shekarar 2025, inda aka auna yadda suke bin ƙa’idojin gaskiya, tsari da yaƙi da cin hanci a cikin ayyukansu…
