26
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Kaduna ta ɗauki sabbin ma’aikatan lafiya 1,800 domin inganta harkokin lafiya a jihar.Farfesa Bello Yusuf-Jamo, babban sakataren a hukumar lafiya ta jihar, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi na raba takardar aiki ga sabbin ma’aikatan a ranar Litinin a Kaduna.Ya ce, an raba takardun ɗaukar aikin na zuwa ne bayan kammala jarrabawar ta baki da rubutu da aka yi a yayin tantancewar domin tabbatar da an yi komai a buɗe da cancanta.Yusuf-Jamo ya ce, jarin sunayen waɗanda aka ɗauka aikin an kafe su ne a shalkwatar hukumar domin…
