ukarofi

12663 Posts
Dokar haraji: Gwamnati ta kare shirin aiwatarwa a watan Janairu

Dokar haraji: Gwamnati ta kare shirin aiwatarwa a watan Janairu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta kare shirinta na fara aiwatar da sabbin dokokin haraji daga watan Janairu 2026. Fadar Shugaban ƙasa ta fuskanci suka daga jama’a kan zargin sauya wasu sassa da bambance-bambancen da ke tsakanin dokokin da Majalisar Dokoki ta amince da su da kuma wanda aka wallafa a kundin gwamnati. Shugaban Kwamitin Shugaban ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Sauye-sauyen haraji, ya yi gargaɗi cewa jinkirta aiwatar da sauye-sauyen zai iya ƙara tsadar kayan masarufi da ayyuka, ciki har da abinci, kiwon lafiya da ilimi, tare da ci gaba da ɗora wa ma’aikata da kananan…
Read More
’Yan sanda sun ƙarfafa yaƙi da ƙungiyoyin asiri da shaye-shaye a Gombe

’Yan sanda sun ƙarfafa yaƙi da ƙungiyoyin asiri da shaye-shaye a Gombe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ’Yan sandan sun ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ƙungiyoyin asiri, shan miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u a Jihar Gombe. Rundunar ’yan sandan jihar ta gudanar da tattaki tare da shirin wayar da kan jama’a a manyan titunan birnin Gombe gabanin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara. An gudanar da shirin ne ƙarƙashin Shirin ’Yan Sanda na Yaƙi da ƙungiyoyin Asiri da Sauran Munanan Halaye (POCACOɓ), bisa manufar Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, na ƙarfafa tsaro ta hanyar rigakafi da haɗin gwiwa da al’umma. Jami’an rundunar tare da masu ruwa da tsaki…
Read More
Gidauniyar zuri’ar Baso ta gudanar da taron tallafa wa zumunci a Kano

Gidauniyar zuri’ar Baso ta gudanar da taron tallafa wa zumunci a Kano

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Gidauniyar Zuri’ar Baso (Baso Family Foundation) mai shelkwata a birnin Kano ta gudanar da taron shekara-shekara na tallafa wa juna da ƙarfafa zumunci a tsakanin ‘ya’yan zuri'ar Baso. Taron ya gudana ne a Gidan Tunawa da Marigayi Malam Aminu Kano (Mambayya) da ke unguwar Gwammaja a Kano. Shugaban zuri'ar Baso na ƙasa, Alhaji Hamza Muhammad, tare da shugaban gidauniyar a Jihar Kano, Alhaji Salisu Ibrahim Yahaya, sun bayyana cewa Baso mutum ne da ya fito daga gidan sarauta amma ba sarauta ba, wanda ya yi ƙaura daga Jamhuriyar Nijar zuwa Kano shekaru da dama da…
Read More
An shirya walimar taya mahaddata Alƙur’ani uku a mako guda a Kano

An shirya walimar taya mahaddata Alƙur’ani uku a mako guda a Kano

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Malam Ahmad Tijjani Lawan Baƙo Maishunku, wanda aka fi sani da Malam Ahmad Maiturare, ya jagoranci shirya walimar taya murnar ɗalibai uku da suka kammala haddar Alƙur’ani mai girma a makarantar tsangayar Khalifah Sheikh Isyaka Rabiu da ke unguwar Goron Dutse a Kano. An fara walimar ne a Masallacin Khalifah Isyaka Rabiu a ranar Lahadi, inda malamai, iyaye da al’umma suka halarta domin taya mahaddatan murna da yi musu addu’ar samun albarka da tsoron Allah. A Lahadi ta biyu kuma aka sake shirya walima ta musamman a gidan Malam Tijjani Lawan Maishunku bayan sallar Azahar,…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta kafa dokoki ga masu sana’ar gwangwan

Gwamnatin Katsina za ta kafa dokoki ga masu sana’ar gwangwan

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan ciniki, masana'antu da yawon shaƙatawa na jihar Katsina Hon. Yusuf Rabi'u Jirdede ne ya sanar da hakan yayin taron shugabanin ƙungiyar masu sana'ar ta gwangwan na ƙananan hukumomi 34 dake faɗin jihar katsina. Kwamishinan ya gabatar masu da kundin dokokin ta hannun lauyan ma'aikatar shari'a Aliyu Isa domin tsaftace masu sana'ar su tare da tantance ya'yan ƙungiyar da irin kallon da wasu jama'a ke yima sana'r tasu. Hon. Yusuf Rabi'u jirdede ya ƙara da cewa za a buɗe ofis a kowace ƙaramar hukuma domin kula da yadda ake tafiyar da wannan sana'ar ta gwan-gwan.…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya yi ta’aziyar waɗanda aka kashe a harin masallacin Borno

Gwamna Raɗɗa ya yi ta’aziyar waɗanda aka kashe a harin masallacin Borno

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina kuma shugaban gwamnonin Arewa maso Yamma Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan mummunan harin da aka kai wa masu ibada a wani masallaci a Jihar Borno. Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin “hari mai zalunci, marar ma’ana kuma abin Allah-wadai da aka kai wa fararen hula marasa laifi da ke cikin ibada, tare da take tsarkin wuraren ibada,"inji shi. Ya ce harin ya yi sanadin salwantar rayuka masu daraja tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya jefa iyalai da al’ummomi cikin jimami da makoki. A…
Read More
Maikaya ya yaba da bikin bajekolin al’adu da farauta na Irewha 2025

Maikaya ya yaba da bikin bajekolin al’adu da farauta na Irewha 2025

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya Mai neman takarar kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa a inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen 2027 mai zuwa, honorabul Musa Mohammed Maikaya ya yaba wa ƙungiyar al'adun gargajiyar nan na ƙabilar Igbira na ƙasa baki ɗaya da ake kira Shafa Abakpa Community Association (SACA) a turance bisa ƙoƙarin da suke yi wajen cigaba da ɗaukaka al'adun Igbira a jihar Nasarawa dama ƙasa baki ɗaya. Honorabul Maikaya ya bayyana haka ne a ranar Asabar 27 ga watar Disambar shekarar 2025 da ake ciki a lokacin da ya halarci wani babban bikin ƙungiyar Shafa Abakpa…
Read More
Fashewar bom ya halaka mutane biyar a Zamfara

Fashewar bom ya halaka mutane biyar a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Kimanin mutane biyar ne suka mutu sakamakon fashewar bam a kan hanyar Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara. A cewar shaidar gani da ido, Malam Yunusa Isah, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da wasu 'yan bindiga ɗauke da makamai suka tare babbar hanyar da misalin ƙarfe 12:00 na ranar a yau. A cewarsa, waɗanda suka rasa rayukansu sun kasance a kan babura kuma sun taka na'urorin fashewar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen biyar. Ya ce, jami'an tsaro sun riga sun mayar da martani kuma sun kori 'yan bindigar daga wurin…
Read More
Barista Tumsa ya bayar da tallafin abinci ga Kiristoci a Yobe don Kirsimeti da sabuwar shekara

Barista Tumsa ya bayar da tallafin abinci ga Kiristoci a Yobe don Kirsimeti da sabuwar shekara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wani mai fafutukar kare haƙƙin jama'a kuma mai neman takarar gwamna a ƙarƙashin jam'iyyar APC a jihar Yobe, Barr. Kashim Musa Tumsah(KMT) ya bayar da gudummawar abinci iri-iri ga reshen mata na ƙungiyar kiristocin Najeriya CAN a Yobe domin su gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekarar cikin sauƙi. A cewar mai magana da yawun sa, Abubakar Ahmed a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gusau, ya ce wannan tallafin wani ɓangare ne na gudummawar da ya bayar domin murnar bikin Kirsimeti da sabuwar shekara. Abubuwan da ya bayar sun…
Read More
Shugaban APC ya naɗa tsohon Sanata, Imran Mohammed da wasu mutane 14 a matsayin mataimaka

Shugaban APC ya naɗa tsohon Sanata, Imran Mohammed da wasu mutane 14 a matsayin mataimaka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Nentawe Yilwatda, ya amince da nadin mataimaka 15, ciki har da tsohon sanata da wani mashahurin mai amfani da kafafen sada zumunta, domin ƙarfafa ayyukan gudanarwa da tsare-tsaren jam’iyyar.Naɗin sun haɗa da mashawarta na musamman da mashawarta, da manyan mataimakan musamman, kuma an tsara su ne domin bunkasa haɗin kai, tsara manufofi, da kuma hulɗa da masu ruwa da tsaki a Babban Ofishin Jam’iyyar.Wannan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Mustapha Dawaki, Babban sakataren Shugaban ƙasa na APC, ya fitar.Sanarwar ta ce ana sa ran wadanda aka…
Read More