28
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce, gwamnatin tarayya ta shirya kakkaɓe ‘yan ta’adda daga dazukan Nijeriya. Idris ya bayyana hakan ne a yayin gana wa da manema labarai na ƙarshen shekara a Abuja a ranar Litinin. Ya yi bayanin cewa, shugaban ƙasa ya bayyana dokar ta-ɓaci a kan tsaro a ƙasa baki ɗaya a shekarar 2025 da muke bankwana da ita. A cewarsa, wannan dokar ta-ɓaci za a ga amfaninsa a watanni masu zuwa musamman ɗaukar sabbin sojoji da jami’an ‘yan sanda. “Kuma za a tura jami’an tsaron…
