ukarofi

12663 Posts
Tinubu na gamsuwa da jagorancinka a Ribas – Ribadu ga Fubara

Tinubu na gamsuwa da jagorancinka a Ribas – Ribadu ga Fubara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mai Bai Wa Shugabab ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro na ƙasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na nuna cikakken gamsuwa da salon jagorancin Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, yana mai jaddada cewa irin yadda yake tafiyar da al’amuran tsaro da siyasa a jihar ya cancanci yabo. Ribadu ya faɗi hakan ne a ranar Litinin yayin da ya jagoranci wata tawagar fadar shugaban ƙasa zuwa Zauren Gwamnatin Jihar Ribas da ke Fatakwal. Tawagar ta ƙunshi Ministan Ayyuka, David Umahi, Ministan Muhalli, Balarabe Lawal, da manyan jami’an Kamfanin Man Fetur na ƙasa, NNPC.…
Read More
Yahaya Bello ne ya naɗa kabal ɗin gwamnatina – Gwamna Ododo

Yahaya Bello ne ya naɗa kabal ɗin gwamnatina – Gwamna Ododo

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya bayyana cewa yana tafiyar da wasu gungu masu tasiri da ake kira kabal a cikin gwamnatinsa, yana mai cewa, wannan tsarin ne ke taimaka masa wajen samun nasara a ayyukan da yake aiwatarwa. Ododo ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga jama’a a wajen ƙaddamar da wani aiki a jihar, inda ya ce ba ya boye gaskiyar cewa yana da waɗanda da ke taimaka masa wajen yanke shawara da aiwatar da manufofi. Ododo ya ƙara da cewa, saɓanin yadda ake kallon samar da makusanta a siyasar Nijeriya a…
Read More
Dalilina na ƙin goyon bayan Tinubu a 2027 – Makinde

Dalilina na ƙin goyon bayan Tinubu a 2027 – Makinde

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana dalilan da suka sa ba zai mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen 2027 ba, yana mai bayyana yadda rarrabuwar kai ke ƙara ta'azzara a cikin jam’iyyar PDP. Makinde ya yi wannan bayani ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a Ibadan, babban birnin jihar, inda ya waiwayi farkon rayuwarsa ta kasuwanci. Ya ce, yana da shekara 29 kacal lokacin da ya samu babbar kwangilarsa ta farko daga kamfanin Mobil, wadda darajarta ta kai dala miliyan ɗaya, lamarin da ya ce ya zama ginshiƙin nasarorinsa a kasuwanci…
Read More
Yadda sanatoci biyu da ’yan majalisa shida masu biyayya ga Wike suka koma APC

Yadda sanatoci biyu da ’yan majalisa shida masu biyayya ga Wike suka koma APC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yanayin siyasar Jihar Ribas na ci gaba da sauya salo bayan da sanatoci biyu da mambobin Majalisar Wakilai shida suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC a hukumance. Sanatocin da suka sauya sheƙa su ne Sanata Allwell Onyesoh mai wakiltar Ribas ta Gabas da Sanata Barinada Mpigi daga Ribas ta Kudu maso Gabas. An sanar da sauyin jam’iyyar ne a yayin zaman Majalisar Dattawa, inda aka dakatar da dokokin majalisar domin bai wa Sakataran APC na ƙasa, Ajibola Basiru, da wasu manyan jam’iyyar damar shiga zauren domin shaida lamarin. Sanatocin biyu, da ake kallon su a…
Read More
Rasuwar mahaifina ta tilasta ni gararamba a titina — Gwamna Akwa Ibom

Rasuwar mahaifina ta tilasta ni gararamba a titina — Gwamna Akwa Ibom

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Bassey Eno, ya bayyana wani sashe mai raɗaɗi amma mai ilmantarwa na rayuwarsa, inda ya ce rasuwar mahaifinsa ta jefa iyalinsu cikin mawuyacin hali, lamarin da ya tilasta masa yin sayar da lemun kwalba a titunan Legas domin taimaka wa mahaifiyarsa. Gwamna Eno ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabin taron kammala karatu na karo na bakwai a Jami’ar Mountain Top da ke Ibafo, Jihar Ogun. A cewarsa, mahaifinsa jami’in ’yan sanda ne da ya rasu yana bakin aiki, lamarin da ya sauya alƙiblar rayuwar iyalinsu baki…
Read More
Ajayi ya sha alwashin kyautata dangantakar DSS da ’yan jarida

Ajayi ya sha alwashin kyautata dangantakar DSS da ’yan jarida

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Daraktan Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta ƙasa (DSS), Oluwatosin Adeola Ajayi, ya sha alwashin samar da yanayi mai sauƙi da adalci da zai bai wa ’yan jarida damar gudanar da aikinsu cikin ’yanci da kariya a Nijeriya. Ajayi ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa mai kwanan wata 19 ga Disamba, 2025, wadda ya sanya wa hannu da kansa, inda ya aika wa Shugaban Cibiyar ƙasa da ƙasa ta ‘Yan Jarida (IPI) reshen Nijeriya, Musikilu Mojeed. Wasiƙar ta zo ne a matsayin martani ga lambar yabo ta karramawa da ƙungiyar ta ba shi…
Read More
Yadda aka ceto ragowar yaran makarantar Katolika daga masu garkuwa – Ribadu

Yadda aka ceto ragowar yaran makarantar Katolika daga masu garkuwa – Ribadu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mai ba Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa ingantaccen bayanan sirri da kuma jajircewar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa na ƙasashen waje, ne suka kai ga nasarar ceto ragowar yara 130 na makarantar Katolika da aka yi garkuwa da su a Jihar Neja. Ribadu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin ta bakin Janar Garba Adamu Laka, yayin tarbar yaran da aka ceto a Fadar Gwamnatin Jihar Neja da ke Minna. Ya ce haɗin kai da tsare-tsaren sirri na Hukumar DSS, Sojojin ƙasa, ’Yan…
Read More
Gyara fasalin haraji na iya tauye tsarin mulki – Farfesa Yadudu

Gyara fasalin haraji na iya tauye tsarin mulki – Farfesa Yadudu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Farfesan shari’a, Auwalu H. Yadudu, ya magantu kan abin da ya bayyana a matsayin wata barazana ga tsarin mulkin dimokurɗiyya, biyo bayan gano bambance-bambance tsakanin dokokin haraji da Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai suka amince da su, da kuma nau’ikan dokokin da gwamnatin tarayya ta wallafa a Jaridar Gwamnati (Gazette). A cikin wani tsokaci mai zurfi, Farfesa Yadudu ya ce bayan duba wata takarda da ke bayyana saɓanin da ke tsakanin dokokin da Majalisar Tarayya ta zartar da kuma irin su da aka wallafa daga baya, ya kai ga wani ƙarshe mai tsanani cewa akwai yiwuwar…
Read More
Sojoji sun cafke ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga a Benuwe

Sojoji sun cafke ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga a Benuwe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sojojin rundunar Forward Operating Base (FOB) Wukari, karkashin rundunar 6 Brigade na Sojojin Nijeriya /Sashe na 3 na rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS), sun cafke wani shahararre kuma ƙasurgumin jagoran 'yan bindiga a ƙaramar Hukumar Ukum ta Jihar Benue. A wata sanarwa da Umar Muhammad, mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cafke jagoran ‘yan bindigar a matsayin gagarumin nasarar aiki ga sojoji. A cewarsa, cafke fitaccen jagoran ‘yan bindigar da ke da alhakin sace-sace da fashi da makami da dama a kan hanyar Benue–Taraba babban…
Read More
Kotu ta ƙwace filayen rukunin gidaje na Goodluck Jonathan 

Kotu ta ƙwace filayen rukunin gidaje na Goodluck Jonathan 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ƙarshe na ƙwace filayen ƙasa masu darajar biliyoyin naira da aka ware domin aikin rukunin gidajen Goodluck Jonathan Legacy Model Housing Estate zuwa Gwamnatin tarayya. Mai shari’a Mohammed Umar ya yanke hukuncin ne bayan amincewa da buƙatar da hukumar ICPC ta gabatar, wadda ba a yi adawa da ita ba.  Kotun ta umurci ICPC, tare da haɗin gwiwar babban bankin bada lamunin gidaje na Nijeriya (FMBN), da su kula da kammala ginin gidaje 962 da aka tsara tun farko. A hukuncin, kotun ta ƙwace Filaye…
Read More