ukarofi

12663 Posts
Yadda matatar Dangote ta rage farashin man fetur zuwa N739

Yadda matatar Dangote ta rage farashin man fetur zuwa N739

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar Dangote ta sanar da fara sayar da man fetur a faɗin Nijeriya kan farashin Naira 739 a kan kowane lita, matakin da ake ganin zai kawo sauƙi ga jama’a tare da daidaita kasuwar man fetur a ƙasar. A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar, an fara aiwatar da sabon farashin ne a dukkan gidajen mai na kamfanin MRS, wanda ke da fiye da gidajen mai 2,000 a sassa daban-daban na ƙasar. Wannan na nufin cewa al’ummar Nijeriya za su fara cin gajiyar rage farashin a kusan dukkan yankuna. Matatar ta yaba wa ’yan kasuwar da…
Read More
2026: Nijeriya za ta dakatar da shigo da ababen hawa marasa inganci

2026: Nijeriya za ta dakatar da shigo da ababen hawa marasa inganci

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da sabon tsari mai muhimmanci a ɓangaren ƙira da shigo da ababen hawa, wanda zai fara aiki daga shekarar 2026, domin dakatar da shigo da motoci marasa inganci da ake kira ‘End-of-Life’ – wato motocin da suka riga suka daina amfani a ƙasashen da aka fito da su. Matakin na da nufin kare masu amfani da mota, kare muhalli, bunƙasa tattalin arzikin sake sarrafa kayayyaki, tare da shirya ƙasar domin sauyin duniya zuwa motocin lantarki. Darakta Janar na Hukumar Tsara da Ci gaban Motoci ta ƙasa (NADDC), Oluwemimo Joseph Osanipin, ya…
Read More
Manoman Jihar Nasarawa sun yaba da shirin FG/IFAD–VCDP

Manoman Jihar Nasarawa sun yaba da shirin FG/IFAD–VCDP

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Manoma a Jihar Nasarawa sun bayyana farin cikinsu da ci gaban da shirin Gwamnatin Tarayya tare da IFAD na Value Chain Development Programme (VCDP) ke kawowa, inda suka ce shirin ya sauya fasalin harkokin noma tare da ba su fata na samun girbi mai yawa da riba. Manoman sun ce matakin da gwamnatin Jihar Nasarawa ta ɗauka na ci gaba da aiwatar da shirin VCDP har bayan shekarar 2026 ya ƙara musu kwarin gwiwa, musamman ganin yadda shirin ke tallafa musu da horo, kayan aiki da dabarun zamani na noma. Sun bayyana hakan ne…
Read More
Kungiyoyi sun yaba wa Gwamnatin Kaduna bisa gyaran cibiyoyin lafiya a jihar

Kungiyoyi sun yaba wa Gwamnatin Kaduna bisa gyaran cibiyoyin lafiya a jihar

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Haɗakar ƙungiyoyin agaji da ƙungiyoyin fararen hula, tare da shugabannin addini, Sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin kafafen yaɗa labarai sun yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa nasarar gyaran zaukacin cibiyoyin Lafiya na Matakin Farko (PHC) a faɗin jihar. Haɗakar ta kai ziyarar tantancewa zuwa wasu zaɓaɓɓun cibiyoyin Kula da lafiya domin nuna godiya ga Gwamnatin Jihar Kaduna da Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar bisa gyaran cibiyoyin Kula da lafiya guda 255 a cikin ƙananan hukumomi 23 na jihar. Manufar ziyarar ita ce tantance tasirin sauye-sauyen da ake aiwatarwa a ɓangaren lafiya a matakin ƙasa…
Read More
Legas: Al’umma sun koka da rusau a unguwar Mile 12

Legas: Al’umma sun koka da rusau a unguwar Mile 12

Daga DAUDA USMAN a Legas Al’ummomi mazauna unguwar Mile 12 da ke ƙaramar Hukumar Ikosi–Isheri–Ketu a Jihar Legas sun koka matuƙa kan rushe-rushen gidajensu da wuraren ibada, lamarin da ya jefa ɗaruruwan iyalai cikin mawuyacin hali. Waɗannan al’ummomi, da suka haɗa da Hausawa, Yarbawa da sauran ƙabilu daban-daban, sun ce rushe-rushen ya afku ba tare da wata sanarwa ko gargaɗi daga hukuma ba. ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Alhaji Muktar Jabo, ɗan asalin Jihar Jigawa kuma shugaba a ɓangaren kasuwancin busasshen barkono a kasuwar Mile 12, ya bayyana cewa rushe-rushen ya faru ne a ranar Litinin, 15 ga…
Read More
Dalilin da zai sa na fice daga PDP — Sule Lamiɗo

Dalilin da zai sa na fice daga PDP — Sule Lamiɗo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babbar jam'iyyar hamayya a Nijeriya PDP na iya rasa wani babban jigonta inda tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya ce zai iya ficewa daga jam'iyyar idan har ba a magance rikicinta ba. Alhaji Sule Lamido, ya ce matsawar ba a samu mafita a jam'iyyar PDP ba, zai duba jam'iyyar da zai yi kawance. Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce akwai matuƙar takaici yadda wasu ke ƙoƙarin lalle sai an kai jam'iyyar PDP ƙasa. Cikin wata hira da ya yi da BBC, tsohon gwamnan na Jigawa ya ce idan har abubuwa suka ki tafiya…
Read More
NNPP ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa 

NNPP ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar NNPP ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa. An sake zaɓen Ahmed ne a ranar Asabar a babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda zai yi wa’adin shekaru huɗu karo na biyu. NNPP ta kuma sake zaɓen sauran mambobin kwamitin gudanarwa na kasa, ciki har da Abba Kawu, mataimakin shugaban jam'iyyar na arewa; Onu Nwaze, mataimakin shugaban jam'iyyar na kudu; Dipo Olayokun, sakataren ƙasa; da Oladipo Johnson, sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar. Sauran sun haɗa da Ibrahim Muhammad, mataimakin sakataren ƙasa; Bala Mohammed, sakataren tsare-tsare…
Read More
Wike ya yi alƙawarin yi wa Tinubu aiki a PDP – Makinde 

Wike ya yi alƙawarin yi wa Tinubu aiki a PDP – Makinde 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan sake tsayawar Shugaba Bola Tinubu takara a 2027 ba, yana mai gargaɗin cewa raunana jam’iyyar PDP na iya barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya. Makinde ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a Ibadan, inda ya ce a wani taro da ya halarta tare da Shugaba Tinubu da Ministan Abuja, Nyesom Wike, Wike ya yi tayin “riƙe PDP” domin Tinubu gabanin zaɓen 2027, ba tare da an nemi hakan ba. Ya ce duk da cewa Wike na da ’yancin mara wa…
Read More
‘Yan Majalisar Tarayya shida daga Jihar Ribas sun koma APC

‘Yan Majalisar Tarayya shida daga Jihar Ribas sun koma APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ’Yan Majalisar Wakilai 6 daga Jihar Ribas sun sanar da sauya shekarsu daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudden ne ya karanta takardun sauya sheƙar su a zauren majalisar a ranar Talata. Masu sauya shekar sun haɗa da Dumnamene Dekor, Cyril Hart Godwin, Solomon Bob, ɓictor Obuzor, Blessing Amadi da Feliɗ Uche. ’Yan majalisar sun danganta matakin da suka ɗauka da rikicin shugabanci da rabuwar kai a PDP, wanda suka ce ya hana su cimma manufofin siyasa da na wakilci yadda ya kamata. Lamarin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu ’yan…
Read More
Kuɗin makamai: Rashin takardun sahalewa ya kare Jonathan daga kamun EFCC – Magu

Kuɗin makamai: Rashin takardun sahalewa ya kare Jonathan daga kamun EFCC – Magu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Malam Ibrahim Magu, ya bayyana dalilan da suka sa ba a taba gayyatar tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan domin yi masa tambayoyi kan shahararriyar badaƙalar kuɗin makamai ta dala biliyan 2.1 ba, wadda ta tayar da ƙura a Nijeriya bayan zaɓen 2015. Magu ya ce, binciken EFCC ya nuna cewa takardun da aka tattara tare da bayanan cikin gida sun tabbatar da cewa kuɗaɗen ba su samu sahalewar hukuma ba domin amfani da su wajen kamfen, lamarin da ya sa ya zama abu mai wuya a…
Read More