ukarofi

12663 Posts
Daga hasken kyamara zuwa hasken ganye: Yadda jarumi John Dumelo ya zama allon kwaikwayo ga Jaruman Afirka

Daga hasken kyamara zuwa hasken ganye: Yadda jarumi John Dumelo ya zama allon kwaikwayo ga Jaruman Afirka

Daga AISHA ASAS  A tsawon lokaci, rayuwar jarumai ta fi shahara ne a inda hasken fitilu yake, tarukan biki da kuma duk wata sharholiya da ake yi da sunan wayewa. Wannan ne ya sa ba kasafai ka ke iya samun jarumin da ya shahara da bai mayar da hankali kan tara kayan ƙawa da birgewa ba. Wannan kuwa ya zama ɗaya daga cikin ɗabi'un da ake faɗa cikin jerin ababen da ke iya kai fitaccen jarumi ga talauci bayan duniya ta ajiye shi. Sai dai a ɓangaren shahararren jarumin fim ɗan Ghana, John Dumelo, abin ba haka ba ne, domin…
Read More
Manufar ’yan ta’adda kan dawowar hare-hare a wuraren ibada

Manufar ’yan ta’adda kan dawowar hare-hare a wuraren ibada

Daga Abba Abubakar Yakubu  A yayin da al'ummar Musulmi ke gudanar da ibadar sallar Magariba a masallacin Jumma'a na Gomboru da ke birnin Maiduguri na Jihar Borno, a ranar Laraba da ta gabata, wanda ya zo daidai da lokacin da mabiya addinin Kirista a Gwoza da sauran sassan Nijeriya ke shirye-shiryen ƙarshe don gudanar da bikin Kirsimeti, kamar yadda suka saba duk shekara, domin tunawa da haihuwar Yeso Almasihu, wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bom ɗin dake ɗaure a jikinsa, wanda a take ya tarwatse ya kashe mutane aƙalla bakwai da jikkata wasu da dama. Wannan yana…
Read More
Chinasa Nworu ya yi barazana ga Arewa

Chinasa Nworu ya yi barazana ga Arewa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A gurguje na taɓa bayyana tsarin farfagandar Hausa zalla da sak yanda ƙungiyar ‘yan awaren Biyafara IPOB ke kamfen ɗin wargaza Nijeriya ne. Don haka ma ‘yar uwar IPOB ta Arewa ta zama IPOH mai dauke da ‘yan kankambar soshiyal midiya masu hura wutar a kaure da yaki kawai. IPOB na kan gaba cikin waɗanda su ka dasa ‘yan karyar Hausa zalla don dinka rigar karya ta Hausawa su tada fitinar kabilanci a Arewa. Har yau ‘yan Hausa zalla sun kasa tabbatar da cewa su Hausawa ne hasalima a ɓoye su ke rufa wayar salula don…
Read More
Tsakanin Aliko Dangote da Farouk Ahmed da yadda rikicin NMDPRA ya ƙazance

Tsakanin Aliko Dangote da Farouk Ahmed da yadda rikicin NMDPRA ya ƙazance

Daga AISHA ASAS  A cikin makon da ya gabata, Najeriya ta tsinci kanta a tsakiyar wani rikici mai amo wanda ya haɗa fushin jama’a, faɗan manyan masu iko, da kuma damuwar hukumomi. Rikicin da ya ɓarke tsakanin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, da tsohon Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Tsakani da ƙasa (NMDPRA), Injiniya Farouk Ahmed, ya wuce batun mutane biyu kawai, rikici ne da ya shafi makomar gaskiya da amana a harkar mulki, musamman a ɓangaren da ke da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasa. Shekaru da dama ‘yan Najeriya na kuka da rashin bayyana gaskiya, rashin…
Read More
NNPP ta kori shugabanta na Jihar Kano Hashim Dungurawa

NNPP ta kori shugabanta na Jihar Kano Hashim Dungurawa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugabannin Jam’iyyar NNPP na mazaɓar Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun sanar da korar shugaban jam’iyyar na jihar, Dr. Hashimu Sulaiman Dungurawa. Ya ce sun ɗauki matakin ne bisa zargin cewa Dungurawa na tada fitina, korar muhimman ’ya’yan jam’iyya ba bisa ƙa’ida ba, da kuma zagin Gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf. Shugaban jam’iyyar na mazaɓar, Shu’aibu Hassan, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a safiyar yau Talata. Kazalika, sun zarge shi da ƙin halartar tarukan masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar, tare da zargin sa…
Read More
NSCDC a Katsina ta kama mutane takwas da ake zargi da ƙona ofishin su

NSCDC a Katsina ta kama mutane takwas da ake zargi da ƙona ofishin su

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar SC Buhari Hamisu ya fitar da sanarwar haka. Lamarin ya faru ne bayan da 'yan sanda sun kai samame a unguwar inda suka kama Uzairu da aka sani da (DAN'KUDA) da ake zargi yana ɗillancin miyagun ƙwayoyi. To sai dai wanda ake zargin yayi ƙoƙarin amfani da ƙarfi wajan kuɓucewa a hannun su ,sai su ka harbe shi har lahira bayan da yayi ƙoƙarin ƙwace bindiga a hannun su. Ganin haka wasu ɓata gari domin su nuna hushin su suka kaiwa 'yan sandan hari wanda nan ma mutum biyu…
Read More
Tireloli uku sun auka wa masu bikin Kirisimeti a Jihar Nasarawa

Tireloli uku sun auka wa masu bikin Kirisimeti a Jihar Nasarawa

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya Wani mummunan hatsari ya auku a jiya Lahadi 28 ga watan Disambar shekarar 2025 da ake ciki da yamma inda wasu manyan tirela gudu uku suka ƙwace daga babban titi suka auka wa wasu mutane a lokacin da ake wani babban bikin al'adar ƙabilar Eggon wadda ake gudanar a ƙarshen shekara-shekara mai taken "Ame Wo Ba Eggon cikin harshen na Eggon. Lamarin ya auku ne a garin Nasarawa-Eggon a Jihar Nasarawa inda lamarin ya laƙume rayukan mutane biyar nan take tare da raunana dayawa cikin masu bikin. A cewar wani ganau da lamarin ya…
Read More
Kafin a yaba da gudunmawar mace sai ta yi abin da namiji yake yi sau goma – Aisha Lawal 

Kafin a yaba da gudunmawar mace sai ta yi abin da namiji yake yi sau goma – Aisha Lawal 

Ni ce a karan kaina na yi tunanin ƙirƙiro da shirin Mata A Yau Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Ga duk wani ma'abocin kallon tashar talabijin ta Arewa 24 ba zai kasa sanin, ɗaya daga cikin shugabannin tashar ba, mai tsarawa da gabatar da shirye-shirye daban-daban, irin su Mata A Yau, da Zamantakewa, wato Hajiya Aisha Lawal Umar. A wannan makon za mu kawo muku wata tattaunawa da wakilinmu Abba Abubakar Yakubu,  ya yi da wannan ƙwararriyar ma'aikaciya, wacce ta kasance ɗaya daga cikin fitattun mata ýan jarida na Arewa, kuma abin koyi ga matasa da ýan mata ýan jarida masu…
Read More
Karamar Hukumar Bichi ta ƙara tallafin kuɗi ga mata masu sana’ar ƙuli

Karamar Hukumar Bichi ta ƙara tallafin kuɗi ga mata masu sana’ar ƙuli

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano ta ƙara tallafin kuɗi ga mata masu sana’ar matsa man ƙuli, domin ƙarfafa su da bunƙasa harkokinsu na kasuwanci. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’ar Yaɗa Labarai ta Karamar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta raba wa manema labarai, inda ta ce Shugaban ƙaramar Hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ne ya bayyana hakan yayin da ƙungiyar mata masu sana’ar man ƙuli ta kai masa ziyara a ofishinsa da ke sakatariyar ƙaramar hukumar. Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana jin daɗinsa bisa yadda ƙungiyar ta nuna…
Read More
NIPC ta janyo masu zuba jari 3,016 a tsakiyar 2025

NIPC ta janyo masu zuba jari 3,016 a tsakiyar 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Talla da Jawo Hannun Jari ta ƙasa (NIPC) ta bayyana cewa ta jawo masu zuba jari 3,016 kai tsaye a tsakiyar shekarar 2025, sakamakon ayyukan zuba jari da aka aiwatar a ɓangarorin masana’antu, fasahar sadarwa (ICT), sarrafa amfanin gona da lantarki. Babbar Darakta kuma Shugabar Hukumar, Aisha Rimi, ta bayyana hakan yayin ganawar manema labarai da hukumar ta shirya, inda ta ce manyan nasarorin zangon sun haɗa da karɓar tambayoyin masu zuba jari 713, taimaka wa rijistar kasuwanci 71, amincewa da izinin kwararru 186, tare da bai wa kamfanoni 17 tallafin PSI. A cewarta, zangon…
Read More