ukarofi

12688 Posts
2027: ACF ta buƙaci ’yan Arewa su yi tururuwa wajen rajistar zaɓe

2027: ACF ta buƙaci ’yan Arewa su yi tururuwa wajen rajistar zaɓe

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kumgiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta yi kira mai ƙarfi ga al’ummar Arewacin Nijeriya da su yi amfani da damar da ake da ita yanzu ta yin rajistar katin zaɓe, domin shiryawa babban zaɓen 2027. Kiran na zuwa ne a lokacin da ake samun ƙarancin kulawa daga jama’a game da rajistar da ake gudanarwa a sassan ƙasa. Yayin ƙaddamar da shugabannin ƙananan hukumomi 27 na ACF a garin Dutse, shugaban ƙungiyar na jihar Jigawa, Aminu Dalhatu, ya nuna takaicinsa kan yadda yankin Arewa ya yi baya a fannin ilimi, lamarin da ya ƙara jefa shi cikin…
Read More
WOTCOSA ta karrama Farfesa Hafsat Ganduje a taronta na cika shekaru 50 

WOTCOSA ta karrama Farfesa Hafsat Ganduje a taronta na cika shekaru 50 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a KANO Kungiyar Tsofaffin ɗalibai na Makarantar Horas da Malamai ta Mata ta Kano (WOTCOSA) da yanzu ake kiran 'makarantar da Goverment Girls College' (WTC), ’yan aji na 1975 sun gudanar da taron cika shekaru 50 da kammala makaratar. Taron tsofaffin ɗaliban da aka gudanar a harabar makarantar ranar talata ya haɗa da buɗe ɗakin karatun makarantar da aka gyara aka sanya littafai da fitulu da fankokin masu aiki da hasken rana da kujjeru da kuma gyara masallacin makarantar da mai ɗakin tsohon Gwamnan jihar Kano tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje Farfesa…
Read More
Rikicin Gaza ya ƙara tsananta duk da tattaunawar diflomasiyya

Rikicin Gaza ya ƙara tsananta duk da tattaunawar diflomasiyya

A daren 19 ga Nuwamba, hare-haren Isra’ila sun ci gaba a unguwannin Shejaiya da Zeitoun, inda aka ruwaito cewa mutane da dama sun rasa rayukansu. Wannan ya haifar da rushewar gidaje da gine-ginen farar hula, ciki har da sansanonin ‘yan gudun hijira. ƙungiyoyin agaji sun bayyana damuwarsu cewa wannan tashin hankali na iya haifar da ƙarin tsanani ga mutanen yankin. Diplomasiyyar duniya, musamman daga Amurka, Masar, da ƙatar, na ƙoƙarin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta. Nabil Abu Rudeineh, kakakin shugaban Falasɗinawa, ya ce, “Ko da akwai yarjejeniya, hare-haren Isra’ila sun nuna rashin gaskiya da niyyar kawo zaman lafiya.” Masana harkokin tsaro…
Read More
Rasha ta musanta batun shirin 28 da Amurka ke yi

Rasha ta musanta batun shirin 28 da Amurka ke yi

Kremlin ta bayyana cewa babu wani sabon shiri na zaman lafiya a Ukraine. Peskov Dmitry wanda ya kasance Kakakin majalisar Rasha, ya ce duk rahotannin da ke nuna Amurka na aiki kan wani shiri mai maki 28 don kawo ƙarshen rikici “ba su da tushe.” Masana harkokin diflomasiyya sun yi tsokaci cewa matakin Kremlin na iya jan hankalin ƙasashen yamma su ƙara matsin lamba kan Rasha. Ukraine kuwa na ci gaba da samun tallafi daga Amurka da Turai wajen kare kanta daga hare-haren Rasha.  Dakta Elena Markova, mai sharhi kan harkokin tsaro, ta ce: “Rasha na ƙoƙarin nuna ƙarfi a…
Read More
Gaza: Rashin tabbas ya sake kunno kai cikin yarjejeniyar tsagaita wuta

Gaza: Rashin tabbas ya sake kunno kai cikin yarjejeniyar tsagaita wuta

Kungiyoyin jin kai sun dakatar da aikin su saboda hare-haren Isra’ila da suka yi ajalin mutane a Gaza City. Wannan ya kawo tsaiko wajen rarraba abinci, magunguna da kayan agaji. UNRWA ta yi gargadin cewa idan har wannan hali ya ci gaba, dubban mutane za su shiga cikin bala’in rashin abinci da lafiya. Dakta Fatima Khalil, kwararriyar lafiya, ta ce: “Yara da mata sune suka fi fuskantar hatsari yanzu. Dole a dauki matakin gaggawa domin ceton rayuka.” ƙasar Amurka ta gabatar da tsarin “Bridge Proposal” domin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta, ciki har da musayar fursunoni, shiga da kayan agaji, da…
Read More
G20: Masu zanga-zanga sun yi barazanar tada tarzoma

G20: Masu zanga-zanga sun yi barazanar tada tarzoma

Kungiyoyin farar hula sun shirya zanga-zangar nuna rashin jin daɗinsu kan tsadar rayuwa da rashin aikin yi. Jami’an tsaro sun ce za su tabbatar an bi doka. Dakta Thandi Nkosi, mai sharhi kan siyasa, ta ce: “Gwamnati na ƙoƙarin daƙile tashin hankali, amma akwai damuwar cewa zanga-zangar za ta jawo matsaloli idan ba a kula ba.” A ɓangare ɗaya kuwa Johannesburg ta yi gyaran fuska sosai—tsabtace kasuwanni, gyaran tituna da kawar da shara—domin karɓar shugabannin duniya. Wannan gyara ya shafi wuraren da masu zanga-zanga za su samu damar bayyana ra’ayi, amma an tsara su domin kiyaye doka da oda. Thabo…
Read More
Putin ya shirya ganawa da shugaban Togo a Kremlin

Putin ya shirya ganawa da shugaban Togo a Kremlin

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, zai gana da shugaban Togo, Faure Gnassingbé, domin tattauna haɗin gwiwa a fannoni kamar noma, makamashi, tsaro da horar da jami’an Togo.  Wannan ziyara na nuna yadda Rasha ke ƙoƙarin faɗaɗa tasirinta a Afirka, yayin da Togo ke neman tallafi wajen bunƙasa noman da makamashi mai ɗorewa. Dakta Issa Kofi, masani kan hulɗa tsakanin Rasha da ƙasashen Afirka, ya ce: “Togo ta zama muhimmiyar abokiyar hulɗar Rasha, musamman wajen samar da albarkatun ƙasa da kasuwannin noma.”
Read More
Cin ganda yana barazana ga masana’antar fata ta Nijeriya, inji Gwamnatin Tarayya

Cin ganda yana barazana ga masana’antar fata ta Nijeriya, inji Gwamnatin Tarayya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi kan yadda ci gaba da cin fatar shanu, wato ganda, wanda wasu ƙabilu suka fi sani da komo, ke barazana ga ɗumbin arzikin masana’antar fata a Nijeriya, wadda darajarta ta kai kimanin dala biliyan biyar. Wannan gargaɗin ya zo ne yayin ƙaddamar da ‘Yaƙin ƙasa Kan Cin Ganda’ da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis. Daraktan Janar na Hukumar Bincike da Haɓaka Kaya (RMRDC), Farfesa Nnanyelugo Ikemounso, ya bayyana cewa karkatar da fata zuwa abinci na rage muhimman kayayyakin da masana’antar fata ke dogaro da su — lamarin da zai…
Read More
Farashin abinci ya sauka a Borno, Yobe da Adamawa – Rahoton NAN

Farashin abinci ya sauka a Borno, Yobe da Adamawa – Rahoton NAN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Farashin kayan abinci ya sauka warwas a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, a cewar binciken da Hukumar Labarai ta Nijeriya (NAN) ta gudanar. Binciken NAN da aka yi a manyan kasuwanni a Maiduguri, Damaturu, Yola ta Arewa da Numan ya nuna raguwar farashin shinkafa, masara, wake, barkono, gero, taliya da man gyaɗa idan aka kwatanta da farashin farkon shekarar. A Kasuwar Litinin da ke Maiduguri, buhun shinkafa mai kilo 50 da aka sayar a tsakanin N78,000 zuwa N82,000 a watan Agusta da Satumba, yanzu tana sayarwa tsakanin N64,000 zuwa N65,000. Haka zalika, buhun masara mai kilo…
Read More
Taron C-PACT zai hanzarta farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya – Shugaban Kwastom

Taron C-PACT zai hanzarta farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya – Shugaban Kwastom

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastom ta ƙasa (NCS), Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa babban taron Kwastom da Haɗin Gwiwar Afirka a Harkokin Cinikayya (C-PACT) da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, 17 ga Nuwamba 2025, zai taka muhimmiyar rawa wajen hanzarta farfaɗowar tattalin arziƙin Nijeriya da faɗaɗa damar fitar da kayayyaki na ƙananan masana’antu ƙarƙashin tsarin AfCFTA. Da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban ƙasa, Adeniyi ya ce, cikakken goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga taron ya nuna muhimmancin da gwamnatin ke bai wa harkar cinikayyar cikin gida. A cewar Adeniyi, sama…
Read More