25
Nov
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A Nijeriya, batun tsige gwamna ya kasance ɗaya daga cikin manyan rikice-rikicen siyasa da suka taɓa girgiza jihohi tun bayan dawowar mulkin dimukraɗiyya a shekarar 1999. Halin da Jihar Ribas ta tsinci kanta a ciki a shekarar 2025 ya sake jawo tsoro da cece-kuce, musamman bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar sakamakon rikicin siyasa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon ubangidansa, kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike. Rikicin da ya fara da barazanar tsige gwamna ya rikiɗe zuwa mummunan tashin hankali — har ma aka tayar da bom a majalisar dokokin…
