23
Nov
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Lamunin Ilimi ta Nijeriya (NELFUND) ta bayyana cewa ta raba naira biliyan 116 domin biyan kuɗin makaranta da kuma tallafin kula da ɗalibai a faɗin Nijeriya. Manajan Darakta na NELFUND, Akintunde Sawyerr, ya bayyana haka a wata hira da ‘yan jarida a Abuja, inda ya jaddada ƙudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da ilimi mai rahusa da shigar da kowa cikin tsarin ilimi a matakin jami’a da kwalejojin ilimi. Sawyerr ya bayyana cewa daga cikin wannan adadi, biliyan N65 an biya kai tsaye zuwa ga jami'o'in gwamnati 239 a madadin ɗaliban da suka samu amincewa da…
