ukarofi

12689 Posts
Rashin ofis da abin hawa a Kano ne ƙalubalenmu a shekara 50 da kafuwa – JNI

Rashin ofis da abin hawa a Kano ne ƙalubalenmu a shekara 50 da kafuwa – JNI

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI) na ƙasa, reshen Jihar Kano, Malam Muhammad Nuraddeen Gwagwarwa, ya bayyana cewa shekaru 50 kenan da kafuwar ƙungiyar, sai dai babbar matsalar da take fuskanta a Kano ita ce rashin ofis da abin hawa. Ya ce duk da cewa gwamnatocin da suka gabata sun taimaka sosai wajen inganta addini, amma JNI a Kano ta daɗe tana neman tallafin da bai samu ba. A yayin taron tunawa da cikar ƙungiyar shekaru 50, Malam Gwagwarwa ya ce an kafa JNI ne domin bayar da agajin gaggawa ga masu buƙata—musamman masu fama da…
Read More
Tsadar taki za ta iya kawo ƙarancin abinci a Nijeriya – AFAN

Tsadar taki za ta iya kawo ƙarancin abinci a Nijeriya – AFAN

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Shugaban All Farmers Association of Nigeria (AFAN), Malam Rabiu Faruk Mudi, ya yi gargaɗin cewa tsadar taki, magungunan ƙwari, da sauran kayan aikin gona na iya janyo raguwar noma a Nijeriya idan ba a ɗauki mataki ba. Ya bayyana haka ne yayin taron wayar da kan manoma a bikin Ranar Abinci ta Duniya a Kano. Malam Mudi ya ce hauhawar farashin kayayyakin aikin gona ya sanya manoma da dama kasa iya ci gaba da noma, duk da cewa a yanzu kayan abinci a kasuwa sun samu sauƙi. Ya buƙaci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya…
Read More
Gwamnan Jigawa ya ɗauki matakin kawo ƙarshen mutuwar mata a lokacin haihuwa – Turakin Taura

Gwamnan Jigawa ya ɗauki matakin kawo ƙarshen mutuwar mata a lokacin haihuwa – Turakin Taura

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi (ɗanmoɗi), ya ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar yawaitar mutuwar mata a lokacin haihuwa a ƙaramar Hukumar Taura. Wannan na zuwa ne bayan rahotannin masana lafiya da suka nuna yankin na daga cikin mafi fama da matsalar. Shugaban ƙaramar Hukumar Taura, Hon. Shuaibu Ibn Hambali Zarga (Turakin Taura), ya shaida wa manema labarai cewa Gwamnan ya bada umarni a gyara asibitoci baki ɗaya, lamarin da ya sa aka inganta babban asibitin Taura da ya dade cikin yanayi mara kyau fiye da shekaru 30. Gwamnan zai kaddamar da asibitin da…
Read More
Sani Danjuma Dakin Gari ya zama sabon Sarkin Hausawan Epe a Legas

Sani Danjuma Dakin Gari ya zama sabon Sarkin Hausawan Epe a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas A ranar Lahadin da ta gabata ne aka ƙaddamar da naɗin Alhaji Muhammadu Sani ɗanjuma ɗakin Gari a matsayin sabon Sarkin Hausawan garin Epe bayan amincewar Majalisar Sarkin Hausawan Legas, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Muhammadu Sani Kabiru, tare da goyon bayan Mai Martaba Sarkin Yarbawan Epe, Oba Kamaluddeen Animashawun. Taron ya gudana ne a harabar fadar sabon sarkin da ke Epe, kuma ya samu halartar sarakunan Hausawa daga sassa daban-daban na Legas, shugabannin al’umma, da ɗimbin jama’ar Hausawa mazauna yankin Epe da kewaye. Kafin nadin rawanin sarauta, Sakataren fadar Sarkin Hausawan Legas ya gabatar da tarihin…
Read More
Kwamishinan Yaɗa Labarai ya halarci taron bita na limaman Juma’a a Kano

Kwamishinan Yaɗa Labarai ya halarci taron bita na limaman Juma’a a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano Kwamared Ibrahim Waiya ya halarci taron bita na kwana ɗaya da Majalisar Limaman Masallatan Juma’a ta Jihar Kano ta shirya ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Sheikh Dr.Muhammad Nasir Adam, tare da tallafin ƙungiyar Tallafawa Musulunci ta Nusret. Taron ya gudana ne a Masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani da ke Kofar Mata. A cikin jawabin sa, Kwamishinan ya yi kira ga manyan limamai da malamai masu daraja da su ƙara azama wajen ilmantar da al’umma kan ingancin gudanar da ibada, musamman a fannoni kamar tsarki, alwala da sallah muhimmam…
Read More
Sace ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty

Sace ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar. A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Amnesty ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga. ƙungiyar ta ce bincikenta ya gano cewar…
Read More
Sarkin Musulmi ya buƙaci Gwamnatin Sokoto ta saka sarakuna a tsarin albashin mafi ƙanƙanta

Sarkin Musulmi ya buƙaci Gwamnatin Sokoto ta saka sarakuna a tsarin albashin mafi ƙanƙanta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya roƙi Gwamnatin Jihar Sakkwati da ta haɗa da sarakuna a cikin tsarin aiwatar da albashin mafi ƙanƙanta na Naira 70,000. Sultan Abubakar ya yi wannan roƙon ne yayin taron da Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki ta shirya a matsayin shiri kafin gabatar da kasafin shekarar 2026 na jihar. An wakilci Sultan ɗin ta hanyar Sarkin Sudan na Wurno, Kabiru Cigari-Alhassan, inda ya jaddada goyon bayan sarakunan gargajiya ga aiwatar da duk manufofi da shirye-shiryen gwamnati a jihar. Sa’adatu Abubakar, wakiliyar masu nakasa, ta roƙi gwamnati…
Read More
Kalaman Trump sun ƙara ƙarfin ƙungiyoyin ta’addanci a Nijeriya – Akume

Kalaman Trump sun ƙara ƙarfin ƙungiyoyin ta’addanci a Nijeriya – Akume

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta ce, sabbin hare-haren da ‘yan ta’adda da barayin daji suka ƙaddamar cikin kwanakin nan a sassan Nijeriya sun samo asali ne daga kalaman da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kwanan nan game da Nijeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta yi tsokaci kan yadda ƙungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi da ɓarayin daji ke sake farfaɗowa a faɗin ƙasar. Ya ce, kalaman shugaban Amurka sun ba wa wasu rukunan ta’addanci damar neman tagomashi da janyo hankalin duniya ta hanyar kai hare-hare kan wuraren da ba…
Read More
Kano 2027: Tsofaffin ’yan majalisa sun musanta goyon bayan Sanata Barau

Kano 2027: Tsofaffin ’yan majalisa sun musanta goyon bayan Sanata Barau

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsofaffin mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano sun ƙaryata wani rahoton da ya yaɗu a kafofin watsa labarai da ke cewa sun amince da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2027. Yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ɓullar rahoton da suka kira na bogi, ɗaya daga cikin tsofaffin ‘yan majalisar — wanda ya nemi a ɓoye sunansa — ya ce labarin ba shi da tushe, kuma ba shi da alaƙa da abin da ya kai su wurin taron da suka yi da…
Read More
Gwamnati ta rufe makarantun sakandire a Jihar Filato

Gwamnati ta rufe makarantun sakandire a Jihar Filato

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos Gwamnatin Jihar Filato ta ƙarƙashin Hukumar Kula Da Ilimin Ƙananan Makarantu ta Bai ɗaya (SUBEB), ta fitar da sanarwar rufe dukkan ƙananan makarantun sakandire da ke faɗin jihar, a wani ɓangare na ɗaukar matakin rigakafi don kare ɗaliban jihar daga faɗawa hannun ƴan bindiga da ke satar ƴan makaranta a jihohin Arewa. Sanarwar ta cigaba da cewa, gwamnati ta yanke shawarar ɗaukar matakin ne sakamakon wata buƙatar gaggawa da ta taso. Sai dai ta ce, wannan mataki ne na wucin gadi ba abu ne da zai jima ba. Rufe makarantun zai fara ne daga ƙananan…
Read More