ukarofi

12689 Posts
Ina nan a APC – Hon. Bello Bakyasuwa

Ina nan a APC – Hon. Bello Bakyasuwa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon sakataren yaɗa labarai na ɓangaren jam'iyyar APC ta Sanata Kabiru Marafa a Jihar Zamfara Muhammad Bello Soja Bakyasuwa, ya jaddada cewar yana nan a jam'iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin ƙaramin ministan tsaro Hon. Dr. Muhammad Bello Matawalle MON da Sanata Abdul'aziz Yari Abubakar. Bello Bakyasuwa tsohon darakta a harkokin tsaro na gwamnatin Jihar Zamfara, kuma tsohon kwamandan hukumar yaƙi da 'yan ta'adda ta Zamfara ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau yau Juma'a. Bakyasuwa ya ƙara da cewa zai cigaba da kasancewa memba a jam'iyyar APC, yana mai ƙarawa…
Read More
Gwamnatin Katsina ta bada umarnin rufe makarantun jihar saboda tsaro

Gwamnatin Katsina ta bada umarnin rufe makarantun jihar saboda tsaro

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wata sanarwa da ta fito daga jami'in hulɗa da jama'a na ma'aikatar ilimi a jihar Malam Danjuma Sani,ya ce duka makarantun firamare da na Sakandare a faɗin jihar aka basu umarni da su rufe saboda yanayin tsaro. Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati nan na bibiyan yanayin tsaro a Arewacin kasan kafin ɗaukar mataki. Wannan mataki da gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauka na zuwa ne bayan da 'yan bindiga suka sace 'yan mata 25 a wata makaranta a jihar Kebbi. Haka kuma bayan afkuwar haka, aka sake samun labarin sace wasu ɗalibai mata a jihar…
Read More
An samu koma-baya a yaƙin da ake yi da matsalar tsaro – Kwankwaso

An samu koma-baya a yaƙin da ake yi da matsalar tsaro – Kwankwaso

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Jagoran jam'iyyar NNPP a Nijeriya Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce ƙaruwar hare-hare da ake samu na baya-bayan nan a ƙasar ya kai matakin da ke buƙatar matakin gaggawa daga hukumomi, musamman daga gwamnatin ƙasar. A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na ɗ, Kwankwaso ya ce wajibi ne gwamnatin Nijeriya ta sauke babban nauyin da ke kanta na kare rayukan al'umma, ta hanyar ƙarfafa wa jam'ian tsaron ƙasar gwiwa. ''Da farko, sace ɗalibai 'yanmata 25 a Kebbi abin damuwa ne da ke sanya fargabar ko za a maimaita abin da ya faru a…
Read More
Tankin ruwa ya kashe mutum huɗu, wasu sun jikkata a Jigawa

Tankin ruwa ya kashe mutum huɗu, wasu sun jikkata a Jigawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  An shiga jimami a garin Zugai da ke ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa, bayan da wani tankin ruwa ya faɗo tare da kashe mutum huɗu da jikkata wasu. Daga cikin waɗanda suka rasu har da wata mace mai juna biyu. Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku ne kwana uku bayan Shugaban ƙaramar Hukumar, ya raba ruwa ga masu sana’ar sayar da ruwa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu mutane. Tankin ruwa, wanda ke amfani da hasken rana wajen samar da ruwa, ya fashe yayin da mutane da yawa suka…
Read More
Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi

Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Manhaja ta ruwaito cewa, da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, inda bayanai ke nuni da cewa sun yi awon gaba da…
Read More
Tsaro: Nijeriya za ta ɗauki sabbin sojoji 24,000

Tsaro: Nijeriya za ta ɗauki sabbin sojoji 24,000

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Hafsan Sojojin Nijeriya (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana shirin ɗaukar sabbin sojoji 24,000 domin ƙara ƙarfin rundunar sojin ƙasar a yaƙi da matsalolin tsaro. Janar Shaibu ya sanar da hakan ne a Kaduna yayin ziyarar aiki da ya kai Runduna ta 1, inda ya ce sabbin cibiyoyin horaswa guda uku da Shugaba Bola Tinubu ya amince da su za su samar da sojojin da suka ƙware a sabon dabarun yaƙi da horo na zamani. Ya ce rundunar na fatan horas da sojoji 12,000 cikin watanni shida, kuma idan an gudanar da…
Read More
Gwamna Yusuf ya ɗauki masu gadi 1,600 aiki don kula da tsaron makarantu a Kano

Gwamna Yusuf ya ɗauki masu gadi 1,600 aiki don kula da tsaron makarantu a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da tura sababbin ma’aikatan tsaro na makarantu 1,600 zuwa makarantun sakandare a faɗin jihar, a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa tsaron makarantun jihar. Matakin ya biyo bayan sace ɗalibai mata 25 da aka yi a Jihar Kebbi kwanan nan. Gwamnan, a ranar Talata, ya ƙaddamar da rabon takardun ɗaukar aiki na dindindin ga sabbin ma’aikatan. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu, Gwamna Yusuf ya bayyana wannan mataki na tura jami’an tsaron makarantu da yawa a lokaci…
Read More
NDLEA ta kama miji da mata kan zargin mallakar buhuna 360 na tabar wiwi

NDLEA ta kama miji da mata kan zargin mallakar buhuna 360 na tabar wiwi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni na cewa an kama wani mutum, Onun Ikoli, tare da matarsa, Itam Onun, bisa zargin mallakar buhuna 360 na tabar wiwi a Jihar Kuros Riba. Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ce ta cafke ma’auratan a ranar Talata a ƙaramar hukumar Yakurr a jihar ta Kuros Riba. Kwamandan NDLEA na jihar, John Anteyi, yayin zantawarsa da Manhaja a Kalaba, ya ce ababen zargin sun yi iƙirarin cewa tabar wiwin wadda nauyinta ya kai tan 4.706, ta wani mutum ce da suke zaman haya a ɗaya daga cikin ɗakunan gidansa. Ma’auratan…
Read More
Ana ci gaba da alhinin rasuwar Shugaban Sashen Buga Jaridun Blueprint, Malam Yahaya Adamu

Ana ci gaba da alhinin rasuwar Shugaban Sashen Buga Jaridun Blueprint, Malam Yahaya Adamu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Marigayi Yahaya Adamu, Shugaban Sashen Buga Jaridun Blueprint. Ministan ya bayyana marigayin a matsayin ma’aikaci mai himma da gaskiya, inda rasuwarsa ta kasance babban rashi mai raɗaɗi a zuciya. Idris, wanda ya ɗage wata ganawa ta aiki domin wannan ziyara a Kaduna, ya ce marigayin ya samu girmamawa daga jama’a saboda halinsa na kirki da jajircewa wajen aikin sa. Ya yi addu’a da cewa: “Allah Maɗaukakin Sarki Ya sa mutuwa ta zama ga marigayin, ya gafarta masa kurakuransa.” Haka zalika, Shugaban…
Read More
Amnesty ta nuna damuwa kan yunƙurin rufe bakin Malam Yahaya Masussuka

Amnesty ta nuna damuwa kan yunƙurin rufe bakin Malam Yahaya Masussuka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar kare Haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana tsananin damuwarta kan matsin lambar da ake yi wa Malam Yahya Masussuka — wani malamin addini da aka sani da wa’azi cikin natsuwa da neman zaman lafiya. Kungiyar ta ce, yunƙurin wasu ɓangarori na amfani da ƙarfin gwamnati domin dakatar da malamin ko rufe makarantunsa, ba tare da wani shaidar karya doka ba, abu ne da ya saɓa wa doka kuma ya saɓa wa ’yancin ɗan Adam. Ta ce, irin wannan tsattsauran ra’ayi da wariyar ra’ayi na tauye ’yancin addini, tare da murƙushe masu faɗin ra’ayoyinsu cikin…
Read More