Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babban Hafsan Sojojin Nijeriya (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana shirin ɗaukar sabbin sojoji 24,000 domin ƙara ƙarfin rundunar sojin ƙasar a yaƙi da matsalolin tsaro.
Janar Shaibu ya sanar da hakan ne a Kaduna yayin ziyarar aiki da ya kai Runduna ta 1, inda ya ce sabbin cibiyoyin horaswa guda uku da Shugaba Bola Tinubu ya amince da su za su samar da sojojin da suka ƙware a sabon dabarun yaƙi da horo na zamani.
Ya ce rundunar na fatan horas da sojoji 12,000 cikin watanni shida, kuma idan an gudanar da horaswa a matakai biyu za a iya samar da jimillar dakarun 24,000.
Babban hafsan ya jaddada cewa shirin ba wai ƙara yawan sojoji ba ne kawai, har ma da tabbatar da inganci, ƙwarewa, da shirin tunkarar barazanar tsaro da ke ƙara ƙamari a faɗin ƙasar nan.
Ya kuma tabbatar da ƙudirin rundunar wajen inganta jin daɗin ma’aikata a ƙarƙashin manufar “Soja Na Farko”.
Ana sa ran sabbin dakarun za su ƙarfafa martanin sojoji, kare al’umma, da kuma inganta tsaro a manyan yankunan da ake fama da rikice-rikice.
