ukarofi

12689 Posts
Yadda ƙauyuka masu nisa ke zama sababbin sansanonin ta’addanci a Nijeriya

Yadda ƙauyuka masu nisa ke zama sababbin sansanonin ta’addanci a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da Nijeriya ke bikin cikar shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar 1 ga Oktoba, 2025, wata kira ta katse shagulgulan saƙonnin taya murna daga wani tashar rediyo a Legas — kira daga wani mazaunin Mubi, Zephaniah Yako, wanda ya bayyana wahalar rayuwar dubban al’ummomin da ke zaune a lunguna da saƙunan ƙasar, inda gwamnati ba ta isa, kuma ’yan ta’adda suka yi ƙatutu. A cikin wani rahoto da jaridar intanet ta News Point ta wallafa, ta ce, Yako ya yi magana cikin murya mai cike da raɗaɗi, ya ce: “Ku aika mana da…
Read More
Kwankwaso ya gargaɗi Gwamnatin Tarayya kan yawaitar hare-hare a iyakar Kano

Kwankwaso ya gargaɗi Gwamnatin Tarayya kan yawaitar hare-hare a iyakar Kano

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki kan yadda ’yan bindiga ke ci gaba da shigowa da kai hare-hare a wasu yankunan kan iyakar jihar, yana gargaɗin cewa lamarin na iya ta'azzara idan aka yi sakaci. A makonnin baya ne wasu ’yan bindiga suka kutsa cikin ƙauyukan Tsanyawa, Shanono da Bagwai, inda suka kashe jama’a tare da yin garkuwa da wasu kafin dakarun Nijeriya su mayar da martani. Wannan mummunan yanayi, a cewar Kwankwaso, ya zama barazana ga zaman lafiya da jihar ta sha fama wajen…
Read More
Jinkirin biyan fansho ya zama tarihi a Nijeriya, cewar hukumar PenCom

Jinkirin biyan fansho ya zama tarihi a Nijeriya, cewar hukumar PenCom

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Fansho ta ƙasa (PenCom) ta bayyana cewa zamanin jinkirin biyan fansho ga ma’aikata masu ritaya ya zama tarihi. Ibrahim Buwai, shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na PenCom, ya bayyana haka a wata hira da Hukumar Labarai ta Nijeriya (NAN) a Abuja ranar Lahadi. Buwai ya ce, PenCom ta cimma nasara wajen biyan haƙƙokin fansho cikin lokaci, sakamakon tsauraran gyare-gyare da inganta tsarin aika kuɗi. Ya ce, tun daga watan Yuli, hukumar na biyan haƙƙoƙin fansho da aka tara kamar yadda ya kamata, domin tabbatar da cewa masu ritaya suna samun haƙƙoƙinsu a cikin…
Read More
Ana tafka muhawara kan muƙabala da Sheikh Masussuka a Katsina

Ana tafka muhawara kan muƙabala da Sheikh Masussuka a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina  Tun a farko Malam Yahaya Masussuka ya kai koke ga masarautar Katsina kan wata ƙungiyar addini da ta matsa masa kan yadda yake gudanar da wa'azi da ya saɓa wa addinin Musulunci. Masarautar, ƙarƙashin Sarkin Katsina ta zauna da Masussuka mai da'awar ƙur'ani zalla da ƙungiyar Izala inda aka samu masalaha. To daga baya kuma aka sake samun ƙorafi daga ƙungiyar kamar yadda Kwamishinan Yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya shaidawa wata kafar yaɗa labarai. A cewar Kwamishinan, ganin haka gwamnatin Katsina ta kafa kwamiti da ya ƙunshi fitattun malamai da za su yi…
Read More
An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai-da-rai

An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai-da-rai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa shugaban masu fafutikar kafar ƙasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai. Wannan ya biyo bayan hukuncin da Mai Shari'a James Omotosho ya yanke a ranar Alhamis, 20 ga Nuwamba, 2025. A cewar alƙalin, "wanda aka yanke wa hukuncin bai yi abin da ya dace ba a duk lokacin zaman kotun, yana mai jaddada cewa ya jawo tsaiko a shari'ar. Ya ƙara da cewa kotun ba za ta yi la'akari da raini da shugaban IPOB ɗin ya yi a kotu yayin da yake…
Read More
Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a ƙananan hukumomi huɗu saboda matsalar tsaro

Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a ƙananan hukumomi huɗu saboda matsalar tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a ƙananan hukumomin jihar guda huɗu na saboda ƙaruwar hare-hare a jihar cikin sa’o’i 48 da suka gabata. Aƙalla mutane uku sun mutu a garin Bokungi da ke ƙaramar Hukumar Edu a ranar Laraba. Lamarin ya faru ƙasa da sa’o’i 24 bayan mummunan harin da aka kai coci a Eruku, ƙaramar Hukumar Ekiti ta jihar, inda aka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da mutum 30. Majiyoyin al’umma sun ce an fara yin garkuwa da mutane huɗu, ciki har da ɗan sa-kai, a cikin…
Read More
Dole Gwamna Dauda ya yi bayanin yadda ya kashe Naira tiriliyan ɗaya – APC

Dole Gwamna Dauda ya yi bayanin yadda ya kashe Naira tiriliyan ɗaya – APC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar All Progressive Congress APC dake jihar Zamfara ta ƙalubalanci gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal da ya fito fili ya yi wa mutanen jihar bayani kan yadda ya kashe sama da Naira tiriliyan 1 da ya samu daga gwamnatin Tarayya a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa. Jam'iyyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ta Yusuf Idris ya sanya wa hannu kuma aka bai wa Blueprint Manhaja a Gusau jiya Alhamis. Za a iya tunawa ƙaramin Ministan Tsaro Hon. Bello Mohammed Matawalle a lokacin ziyarar da ya kawo jihar…
Read More
Sakataren tsare-tsaren APC ya jajenta wa iyalan da harin Maga ya shafa

Sakataren tsare-tsaren APC ya jajenta wa iyalan da harin Maga ya shafa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Sakataren tsare-tsaren Jam'iyyar APC ta ƙasa kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi  Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu ya jajentawa iyalan waɗanda harin makarantar 'yan matan Maga ya shafa. Ya bayyana cewa babu shakka akwai damuwa mai yawa saboda rashin sanin halin da waɗannan yaran da 'yan bindiga suka sace sai dai babu yadda za a yi sai dai a cigaba da addu'ar Allah ya bayyana su ya kuma sada su da iyayensu cikin ƙoshin lafiya. Ya kuma nemi iyaye da 'yan uwansu da su ɗauki wannan abin a matsayin muƙaddari ne daga Allah wanda babu wani…
Read More
EFCC ta kama wata bishop bisa barin ‘yan ‘Yahoo’ su liƙa wa saniya kuɗi a coci

EFCC ta kama wata bishop bisa barin ‘yan ‘Yahoo’ su liƙa wa saniya kuɗi a coci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayyana cewa jami'anta sun kama Angel Oyeghe, babbar bishop kuma wacce ta kafa Faith Healing Ministry a Warri, jihar Delta. Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ta ce an kama Oyeghe a ranar Talata kan wani bidiyo da ke yawo a yanar gizo inda "an ga wasu mutane da ke ƙarƙashin kulawarta suna watsa wa saniya mai rai kuɗi a lokacin wani shiri na coci". EFCC ta ƙara da cewa za a tuhumi babban bishop a kotu…
Read More
Gwamnatin Zamfara za ta yi wa marayu 200 auren gata

Gwamnatin Zamfara za ta yi wa marayu 200 auren gata

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala shirye-shiryen bikin auren gata ga sama da marayu 200 a faɗin jihar. Sakataren Hukumar Zakkah da Tallafi ta jihar, Malam Habibu Balarabe, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara. Ya ce, za a gudanar da bikin ne a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar. Balarabe ya ce, an kammala tantance duk waɗanda za su amfana da shirin ɗaurin auren, kuma an zaɓe su bisa cancanta. Baya ga bikin auren, hukumar za ta bai wa mata 200 da ke sana'o'in hannu tallafin kuɗi…
Read More