21
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Gaza. A farkon wannan watan ne Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana Nijeriya cikin jerin ƙasashe masu matsala ta musamman. Sannan Trump ya umarci wasu ’yan majalisar Amurka, ciki har da ɗan Majalisa Riley Moore da su binciki lamarin.…
