ukarofi

12689 Posts
Tarihin Masarautar Pindiga

Tarihin Masarautar Pindiga

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Pindiga, ita ce helikwatar mulkin masarautar Pindiga, wacce kuma ɗaya ce daga cikin masarautun Jihar Gombe. Wannan gari mai daɗaɗɗen tarihi, Jukunawa suka kafa shi a tsakankanin ƙarni na goma sha shida zuwa ƙarni na goma sha bakwai. Garin ya fara daga ɗan ƙaramin matsugunni na wasu jama’a a kan dutse har zuwa bunƙasarsa kamar yadda yake a yau a matsayin masarautar sarkin yanka mai daraja ta biyu a cikin Jihar Gombe. Asali: Pindiga, gari ne mai tsohon tarihi, asalin kafuwar wannan gari yana farawa daga lokacin da Jukunawa suka shigo yankunan baƙaƙe daga ƙasar Yamen,…
Read More
Shigar-burtu ga Hausawa

Shigar-burtu ga Hausawa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Karya fure ta ke ba ta ‘ya’ya. ‘Yan kwangilar rusa Arewa sun yi tsammanin za su iya basaja da yin shigar-burtu wai su Hausawa ne sai kawai a kyale su, ko ma a rika rarrashinsu don kar su tada hankali ga takarkarewa da su ka yi sai sun kunna fitinar ƙabilanci. Fasa mu su taya da fito da su a matsayin makiya Hausawa da addinin Hausawa ya sa su ka koma zunduma ashar ta uwa ta uba. Yo in ba ɗan banza bakwai na zamanin yau ba, waye zai zayyana hoton gwagwarmayar Hausawa da wani baubawan…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Funtua ya ƙaddamar da masu bashi shawara guda 50

Shugaban ƙaramar hukumar Funtua ya ƙaddamar da masu bashi shawara guda 50

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Da yake ƙaddamar da mashawartan a ɗakin taro na ƙaramar hukumar, shugaban Alhaji Abdulmutallab Suleiman Goya ya shawarce su da su yi amfani da basirar su wajan bada ta su gudunmawar ga cigaban ƙaramar hukumar gaba. Ya bayyana cewa sai da aka ba duk mazaɓu a ƙaramar hukumar damar wajen zaƙulo waɗanda za su bada shawarar da suka haɗa da matasa,masu buƙata ta musamman,mata ,yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar. Hon Abdulmutallab ya sanar da cewa wannan masu bada shawara kashi na farko ne a yayin da kashi na biyu…
Read More
‎Gidauniyar Musa Adamu Gwagware Network za ta raba magungunan cutar fata

‎Gidauniyar Musa Adamu Gwagware Network za ta raba magungunan cutar fata

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban gidauniyar Kwamred Mannir Suleiman ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a Katsina. Ya ce tuni gidauniyar ta sayi magungunan na miliyoyin Naira domin rabawa kyauta ga masu wannan cuta a yankin Funtua. Kwamred Suleiman ya bayyana cewa har wala yau gidauniyar ta baza ƙwararrun malaman kiwon lafiya na fannin cutar fatar zuwa ƙauyukan da ke yankin domin gano da tantance masu ɗauke da cutar kafin basu maganin. Ya ce cutar da ya haɗa da kyasfi da saurar cutukan da suka shafi fatan mutum "yara mabarata suka fi ɗaukar cutar saboda…
Read More
Gobara ta ƙone kasuwar tsofaffin ƙarafa a Gombe

Gobara ta ƙone kasuwar tsofaffin ƙarafa a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Wata gobara ta tashi a daren Talata zuwa safiyar Laraba a kasuwar tsofaffin ƙarafa da katako da ke Gombe, inda ta ƙone shaguna fiye da 30 tare da lalata dukiya mai darajar miliyoyin naira. Shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani A.A. Haruna, ya ziyarci wurin tun lokacin da wutar ke ci, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga al’umma. Ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa hukumar ƙaramar hukumar za ta ci gaba da tallafa musu. Haruna ya kuma yaba wa mazauna unguwannin da ke kusa…
Read More
Kasafin 2026: Gwamnn Kano ya miƙa Naira tiriliyan 1.368

Kasafin 2026: Gwamnn Kano ya miƙa Naira tiriliyan 1.368

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2026 mai nauyin N1,368,127,929,271 ga Majalisar Dokokin Jihar Kano, inda ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kammala muhimman ayyuka da kuma zurfafa ci gaban da ya shafi kowa a faɗin jihar. Gwamna ya bayyana cewa gwamnatin sa ta cimma fiye da kashi 80 cikin 100 na alƙawuran da ta yi a lokacin yaƙin neman zaɓe.‎Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, gwamnan, ya ce kasafin ya ƙunshi kaso 68% na kashe-kuɗi (capital expenditure) wanda ya kai N934.6 biliyan, da 32% na kuɗin gudanarwa…
Read More
Tweakrr: Yadda ’yan Nijeriya suka ƙirƙiri fasahar AI da ke sauya fannin bincike a duniya

Tweakrr: Yadda ’yan Nijeriya suka ƙirƙiri fasahar AI da ke sauya fannin bincike a duniya

Akwai lokuta a rayuwar ɗan adam da wahala kan haifi abin mamaki, da kuka kan zamo dariya. Wannan shi ne labarin yadda wani dare mai duhu a rayuwar ɗan Nijeriya ya zama hasken sabuwar fasahar da ke sauya duniyar bincike gaba ɗaya. A lokacin da Kamil Bello Furƙan ya rasa aikin bincikensa da ya shafe watanni yana rubutawa, bai san cewa asarar nan za ta haifi abin da zai girgiza duniya ba. Amma da ya haɗa kai da abokinsa Lawal Habeeb, suka ƙirƙiri Tweakrr — wata sabuwar manhajar basirar wucin-gadi (AI) wadda ke yin abin da babu wata fasahar da…
Read More
Gudunmawar iyaye wajen nasarar ’ya’yansu a makaranta

Gudunmawar iyaye wajen nasarar ’ya’yansu a makaranta

Tare da BILKISU YUSUF ALI Iyaye su na da rawar gani sosai wajen tabbatar da nasarar ’ya’yansu a makaranta. Rashin kulawa ko rashin goyon baya daga iyaye kan iya shafar karatun ɗalibai ta hanyoyi da dama, yayin da kulawa da haɗin kai tsakanin iyaye da makaranta ke ƙara wa ɗalibai ƙarfi da ƙwarin gwiwa wajen cimma burinsu. Wannan nazarin za ta bayyana yadda iyaye za su iya taimakawa wajen inganta karatun ’ya’yansu da yadda hakan ke kawo canji mai kyau a rayuwarsu.  Muhimman abubuwan da iyaye za su yi don taimakawa nasarar ‘ya’ya: 1. Kulawa da yanayin karatu a gida…
Read More
Alwan Hassan ya nemi afuwar Sanata Barau da Akpabio

Alwan Hassan ya nemi afuwar Sanata Barau da Akpabio

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Alwan Hassan, ya nemi afuwar shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio da mataimakinsa, Barau Jibrin kan zargin da ya yi musu na karɓar cin hancin dala miliyan goma domin hana tabbatar da Ramat Abdullahi a matsayin Shugaban hukumar kula da lantarki ta ƙasa NERC. Hassan ya amince cewa zargin da ya yi musu da sauran jagorancin majalisar dattawa ba gaskiya ba ne, kuma ba adalci ba ne ga majalisar da shugabanninta. A wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a wannan Talata,…
Read More
Gwamna Yusuf ya ƙaddamar da Majalisar Sarakunan Kano

Gwamna Yusuf ya ƙaddamar da Majalisar Sarakunan Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da sabuwar Majalisar Sarakunan Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, tare da sauran sarakuna uku na Gaya, Ƙaraye da Rano a matsayin mambobi. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Kano ranar Litinin. Ƙaddamarwar ta zama sabon babi a tarihin masarautar Kano, bayan rattaɓa hannu kan dokar Kano Emirates Council Law (Repeal Bill) 2024, wacce ta rushe masarautu biyar da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ƙirƙiro. A yayin taron…
Read More