18
Nov
Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da shirya zama tsakanin fitaccen malamin nan Sheikh Yahya Masussuka da kwamitinin malaman jihar domin ya kare kansa. Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce ta buƙaci malamin ya bayyana a gaban kwamitin malaman jihar domin kare kansa game da wasu kalaman da yake furtawa a karatunsa. Tun da farko wasu malamai a jihar ne suka shigar da ƙorafinsu ga gwamnatin jihar saboda zarginsa da wuce gona da iri a karatuttukansa. Bayan ƙorafin malaman sai wasu malaman da ke goyon bayansa suka shigar da ƙorafinsu gaban gwamnati…
