ukarofi

12726 Posts
Gwamnatin Katsina ta ƙulla yarjejeniya da wata ƙungiya da ke ƙasar Belgium kan cutar kansa

Gwamnatin Katsina ta ƙulla yarjejeniya da wata ƙungiya da ke ƙasar Belgium kan cutar kansa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta sanya hannu kan yarjejeniya da wata kungiya mai suna Revive daga ƙasar Belgium domin tallafa wa mata wajen gano da kuma maganin cututtukan kansar ciwon nono da na mahaifa. A ƙarƙashin wannan haɗin gwiwa, likitoci 25 daga Belgium za su zo Katsina domin bayar da kulawar lafiya, gudanar da gwaje-gwaje, tare da horas da ma’aikatan lafiya na cikin gida har na tsawon mako biyu. Kwamishinan Lafiya, Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana wannan yarjejeniya na nufin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da cutar kansa a tsakanin mata a jihar. Uwargidan Gwamna, Hajiya…
Read More
Majalisar Wakilai na yunƙurin ganin an sanya ido kan Kirifto

Majalisar Wakilai na yunƙurin ganin an sanya ido kan Kirifto

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar wakilan Nijeriya ta fara yunƙurin ganin an ɗauki matakan sanya ido kan harkokin da suka shafi hada-hadar kuɗaɗe na intanet na kirifto da na'urar POS. A ranar Litinin ne kakakin majalisar, Abbas Tajudeen ya ƙaddamar da wani kwamiti wanda zai duba amfani ta ɓangaren tattalin arziki da yadda za a sanya ido kan su da kuma tsaron hada-hadar da ake yi ta hanyar intanet. A jawabin da ya gabatar kakakin majalisar ya ce matakin ya zama dole, idan aka yi la'akari da damuwar da ake nunawa kan damfara da manyan laifukan intanet da samar da…
Read More
Gwamnatin Kaduna ta lashe lambar yabo ta gwamnati mafi goyon bayan mata da iyali

Gwamnatin Kaduna ta lashe lambar yabo ta gwamnati mafi goyon bayan mata da iyali

Daga MAHDI M MUHAMMAD a Kaduna An karrama Jihar Kaduna da lambar yabo ta Gwamnati Mafi Goyon Bayan Mata da Iyali wanda ƙungiyar Muryar Mata ( ɓOW) ta ba shi. ƙungiyar ta ce wannan karramawar tana girmama jihohi da cibiyoyi da ke nuna gagarumin kishin inganta rayuwar mata ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen da suka mayar da hankali kan ƙarfafa mata. Ta ce zaɓen Kaduna ya nuna yadda jihar ke gaba wajen kafa tsarin mulki mai kula da bambancin jinsi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Sanata Uba Sani. Daga cikin muhimman ayyukan da masu shirya taron suka jaddada akwai amincewa da baiwa…
Read More
Abu ne mai muhimmanci haɗa kai domin bunƙasa cigaban al’ummar Rano – Sarkin Rano

Abu ne mai muhimmanci haɗa kai domin bunƙasa cigaban al’ummar Rano – Sarkin Rano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Mai martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammad Isah Umaru ya yi kira ga 'yan asalin ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure akan su cigaba da haɗa kansu da tafiya tare domin  bunƙasa cigaban al'ummar yankin. Ya bayyana haka ne a yayin taron karrama 'yan asalin Rano dake ayyuka daban-daban a faɗin  ƙasar nan da aka yi a garin Rano  ranar Asabar. Ya kuma ja hankalin mutanen da aka karrama su buɗe wata ƙungiya ta daban su haɗa kai da ƙungiyar RAKIBU da za su riƙa fito da al'amuran da zai taimaka ga cigaban al'ummar masarautar Rano.…
Read More
Ranar ‘yancin kai: Har yanzu Nijeriya na da makoma mai kyau, inji Yerima Shettima 

Ranar ‘yancin kai: Har yanzu Nijeriya na da makoma mai kyau, inji Yerima Shettima 

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna Shugaban ƙungiyar Northern Stakeholders Initiatiɓe, Yerima Usman Shettima, ya roƙi ‘yan Nijeriya da su riƙe fata nagari da haɗin kai yayin da ƙasar ke bikin cikar shekaru 65 da samun ‘yancin kai. Yayin da yake jawabi a wani biki da aka gudanar a Kaduna wanda ƙungiyar mahaya manyan babura (power bike) URMC Bikers tare da haɗin gwiwar Capacity Moɓement suka shirya, Shettima ya ce tsayuwar Nijeriya duk da ƙalubale da dama da ta fuskanta alama ce ta cewa har yanzu ƙasar tana da makoma mai kyau. Ya ce, “Abin da ya sa muka kasance ƙasa…
Read More
‘Yan Nijeriya sama da miliyan 33 ne ke fama da rashin abinci – Akpabio 

‘Yan Nijeriya sama da miliyan 33 ne ke fama da rashin abinci – Akpabio 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa fiye da ‘yan Nijeriya miliyan 33 na fuskantar matsanancin rashin abinci, yana mai cewa lamarin na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa na doka. Akpabio ya bayyana haka ne a zaman farko na Majalisar Dattawa bayan hutun shekara a Abuja, inda ya kuma jajanta wa jama’ar da ambaliyar ruwa ta shafa a jihohin Bayelsa, Sakkwato, da Zamfara. Blueprint Manhaja ta rawaito cewa Akpabio ya ce yunwa ba za ta ƙare da magana kawai ba, sai da manufofi da kasafin kuɗi da ƙarfin zuciya, tare da buƙatar inganta…
Read More
PENGASSAN ba ta fi ƙarfin Nijeriya ba, inji Shettima

PENGASSAN ba ta fi ƙarfin Nijeriya ba, inji Shettima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Nijeriya ta yi kira da a yi takatsantsan tsakanin matatar ɗangote da ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta ƙasa (PENGASSAN), tana mai cewa Nijeriya ta fi ƙarfin a tsayar da ita cak. “Ba zai yiwu ba a tsayar da ƙasar nan cak saboda dambarwar ƙungiyar ma’aikata. Nijeriya gaba take da ƙungiyar PENGASSAN. Nijeriya sama take da kowannenmu,” mataimakin shugaban ƙasa ya jaddada a yayin bikin tattalin arziƙi na Nijeriya karo na 31 a Abuja a ranar Litinin. “Wannan matatar an gina ta ne ta hanyar haɗakar zuba hannun jari da karɓar bashi daga bankuna…
Read More
Yadda Jami’ar Ahmadu Bello ta rasa malamai 2,000 bayan samun aiki mai gwaɓi a Nijeriya da ƙasashen waje – VC

Yadda Jami’ar Ahmadu Bello ta rasa malamai 2,000 bayan samun aiki mai gwaɓi a Nijeriya da ƙasashen waje – VC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, ta yi bikin cika shekaru 63 da kafuwa, sai dai Shugaban Jami’ar, Adamu Ahmed, ya ce jami’ar a cikin waɗannan shekaru ta rasa ƙwararrun ma’aikatanta waɗanda suka tafi saboda wasu damarmaki a cikin ƙasar nan da ma a ƙasashen ƙetare. Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa shugaban jami’ar ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a wani ɓangare na bikin cika shekaru 63 da kafuwa. Ya kuma koka da cewa; “ma’aikata na rasa ƙarfin guiwarsu saboda cigaba da lalacewar gine-gine da…
Read More
Mun kafa asusun biliyan N200 don taimaka wa masana’antu da ƙananan ‘yan kasuwa, inji Tinubu

Mun kafa asusun biliyan N200 don taimaka wa masana’antu da ƙananan ‘yan kasuwa, inji Tinubu

Daga USMAN KAROFI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kafa asusun tallafi na Naira biliyan 200 domin taimaka wa masana’antu da ƙananan ‘yan kasuwa (MSMEs) wajen ƙarfafa musu da magance matsalolin da ke hana su ci-gaba. Tinubu ya faɗi haka ne a Abuja ranar Litinin yayin buɗe taron tattalin arziƙi na ƙasa (NESG) karo na 31, inda ya ce, bayan nasarar da Nijeriya ta samu na bunƙasar tattalin arziki da ya kai kashi 4.23 cikin 100 a watan Satumba 2025, sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako mai gamsarwa a fannoni…
Read More
Babu cin karo da juna tsakanin dokokin haraji na Kano da na tarayya – Shugaban KIRS

Babu cin karo da juna tsakanin dokokin haraji na Kano da na tarayya – Shugaban KIRS

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano (KIRS), Dakta Zaid Abubakar, ya bayyana cewa babu wani cin karo da juna ko saɓani tsakanin dokokin haraji na hukumar da na Hukumar  Tattara Haraji ta Tarayya (FIRS). Dakta Abubakar ya ce duka hukumomin biyu masu tara kuɗaɗen shiga ne da ke aiki a ƙarƙashin tsarin haraji na ƙasa ɗaya. Ya bayyana hakan ne a lokacin taron tattaunawar masu ruwa da tsaki kan gyaran tsarin haraji da aka gudanar a Kano ranar Litinin, inda Daraktan Bin Doka da Tilasta Aiwatarwa na KIRS, Muhammad Aliyu, ya wakilce shi. A…
Read More