ukarofi

12728 Posts
Mun kafa asusun biliyan N200 don taimaka wa masana’antu da ƙananan ‘yan kasuwa, inji Tinubu

Mun kafa asusun biliyan N200 don taimaka wa masana’antu da ƙananan ‘yan kasuwa, inji Tinubu

Daga USMAN KAROFI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kafa asusun tallafi na Naira biliyan 200 domin taimaka wa masana’antu da ƙananan ‘yan kasuwa (MSMEs) wajen ƙarfafa musu da magance matsalolin da ke hana su ci-gaba. Tinubu ya faɗi haka ne a Abuja ranar Litinin yayin buɗe taron tattalin arziƙi na ƙasa (NESG) karo na 31, inda ya ce, bayan nasarar da Nijeriya ta samu na bunƙasar tattalin arziki da ya kai kashi 4.23 cikin 100 a watan Satumba 2025, sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako mai gamsarwa a fannoni…
Read More
Babu cin karo da juna tsakanin dokokin haraji na Kano da na tarayya – Shugaban KIRS

Babu cin karo da juna tsakanin dokokin haraji na Kano da na tarayya – Shugaban KIRS

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano (KIRS), Dakta Zaid Abubakar, ya bayyana cewa babu wani cin karo da juna ko saɓani tsakanin dokokin haraji na hukumar da na Hukumar  Tattara Haraji ta Tarayya (FIRS). Dakta Abubakar ya ce duka hukumomin biyu masu tara kuɗaɗen shiga ne da ke aiki a ƙarƙashin tsarin haraji na ƙasa ɗaya. Ya bayyana hakan ne a lokacin taron tattaunawar masu ruwa da tsaki kan gyaran tsarin haraji da aka gudanar a Kano ranar Litinin, inda Daraktan Bin Doka da Tilasta Aiwatarwa na KIRS, Muhammad Aliyu, ya wakilce shi. A…
Read More
Tinubu na neman amincewar majalisa don ciyo bashin dala biliyan 2.35 

Tinubu na neman amincewar majalisa don ciyo bashin dala biliyan 2.35 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wa majalisar wakilai yana neman amincewarta domin ciyo bashin dala biliyan 2.347 daga kasuwar kuɗin ƙasashen waje domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025 da kuma sake biyan tsohon bashin Eurobond da zai ƙare a watan Nuwamba 2025. Haka kuma, Shugaban ƙasar yana neman amincewar majalisar wajen fitar da tsarin bashi mara ruwa na Sukuk na farko a duniya, wanda darajarsa ta kai dala miliyan 500, domin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa. Tinubu ya ce buƙatar tana da tushe bisa ga tanade-tanaden Dokar Hukumar Gudanar da Bashi…
Read More
Gwamnatin Sakkwato ta gargaɗi masu suka da su daina siyasantar da matsalar tsaro

Gwamnatin Sakkwato ta gargaɗi masu suka da su daina siyasantar da matsalar tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya gargaɗi 'yan hamayya da sauran 'yan jihar da su guji sanya siyasa a cikin matsalar tsaro, inda ya nanata cewa hakan na ƙara ta'azzara matsalar a jihar. Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a ƙaramar hukumar Silame a ci gaba zagayen ziyarce-ziyarcen jaje a wuraren da 'yanbindiga suka kai hare-haren a 'yan tsakankanin nan. "Matsalar tsaro al'amari ne mai matuƙar muhimmanci, don haka ya kamata a riƙa bi a hankali a duk lokacin da ake magana game da tsaro," in ji shi kamar yadda mai magana da yawun…
Read More
‘Yan sanda a Katsina sun kashe ‘yan bindiga biyar da kuɓutar da mutane 80

‘Yan sanda a Katsina sun kashe ‘yan bindiga biyar da kuɓutar da mutane 80

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan ƴan sanda CP Bello Shehu ya shaidawa manema labarai a ofishin sa lokacin da yake bayani kan nasarorin da rundunar yan sandan ta samu a watan da ya gabata. Haka kuma kwamishinan ya sanar da kama mutanen 168 da ake zargi da aikata laifuka daban daban a faɗin jihar. Laifukan sun haɗa da aikata fashi da makami,kisan kai,fyaɗe,lalata da satar wayoyin wutan lantarki na KEDCO mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba. Akwai kuma waɗanda aka kama ɗauke da miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi. CP Bello Shehu ya bayyana wasu daga cikin kayayyakin da aka…
Read More
Dikko Raɗɗa ya kai ziyarar ba zata a wata makarantar sakandare a Katsina 

Dikko Raɗɗa ya kai ziyarar ba zata a wata makarantar sakandare a Katsina 

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina  Gwamna Jihar Katsina Malam Dr. Dikko Umaru Raɗɗa ya kai ziyarar bazata zuwa makarantar kwana ta maza dake garin ɓatagarawa don ganin yanayin makarantar da kuma ɗaliban.  Gwamna ya zagaya cikin makarantar sannan ya duba kitchen inda ake dafa abinci. Da yake ɗaliban makarantar, gwamnan ya hore su da su zama mas ladabi da biyayya da kuma bin dokokin makaranta. Wannan ziyara ta bazata ita ce ta farko da gwamnan Raɗɗa ya fara kaiwa domin gane ma idanunsa halin da ɗalibai ke ciki.  Ya kuma yi kira gare su da su himmatu wajen karatu domin…
Read More
Muna haɗa hannu da jami’an tsaro don tsaftace harkan ma’adanai a Nasarawa – Margaret Elayo

Muna haɗa hannu da jami’an tsaro don tsaftace harkan ma’adanai a Nasarawa – Margaret Elayo

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya Kwamishiniyar ma'aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta Jihar Nasarawa Sarauniya Margaret Itake Elayo tace zuwa yanzu akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin ma'aikatar muhallin da hukumonin tsoron jihar dabandaban a fannin yaƙi da masu harkokin hakar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a jihar. Ta sanar da haka ne a jawabin ta a lokacin da take tattauna da manema labarai a ofishin ta dake ma'aikatar a birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar ranar Juma'a na mako da ake ciki. Tace kawo yanzu ma'aikatar da haɗin gwiwar hukumonin tsoron sun daƙile yunƙurin gudanar da ayyukan hakar ma'adanan ta gurɓataccen…
Read More
AIT Farms ta tallafa wa ɗaliban Gombe da ƙwai 3,000 a bikin Ranar Ƙwai ta Duniya

AIT Farms ta tallafa wa ɗaliban Gombe da ƙwai 3,000 a bikin Ranar Ƙwai ta Duniya

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe A yayin bikin ranar ƙwai ta duniya, kamfanin AIT Integrated Farms da ke Gombe ya gudanar da wani shiri na musamman inda ya raba ƙwai guda 3,000 ga ɗaliban makarantun firamare domin tallafawa lafiyar yara da inganta abincinsu mai gina jiki. Shugaban kamfanin, Abubakar Inuwa Tata, ya bayyana cewa wannan aikin alheri yana nuni da yadda AIT Farms ke ɗaukar nauyin inganta abinci da bunƙasa tattalin arzikin al’umma ta hanyar tallafawa yara da manoma. Ya ce, “Mun ɗauki nauyin koyar da manoma 100 na gida sabbin dabarun kiwon kaji tare da basu kaji domin…
Read More
Sarkin Kano Sunusi ya sallaci Babban Malami Na Madabo

Sarkin Kano Sunusi ya sallaci Babban Malami Na Madabo

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar jana'izar fitaccen Malamin addinin Musulunci nan, Malam Kabiru Ibrahim Na Madabo. An yi Jana'izar ne da ƙarfe 10 na safiyar yau Juma'a a filin Ƙofar Kudu da ke masarautar Kano. Shahararren malamin ya rasu ne a jiya Alhamis, bayan sallar La'asar a gidan sa da ke ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano. Ɗimbin al'ummar musulmi ne suka halaccin janaizar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Read More
Sabuwar hanyar Tinubu tana farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya

Sabuwar hanyar Tinubu tana farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya

A tsawon shekaru, tattalin arzikin Nijeriya ya sha fuskantar ƙalubale iri-iri – daga hauhawar farashi, sauyin farashin mai, zuwa raguwar darajar Naira. Amma a halin yanzu, ana ganin wasu sabbin alamun farfaɗowa da haɓaka, abin da ke nuna cewa ƙoƙarin Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara haifar da sakamako mai kyau. Bisa bayanan da hukumomin gwamnati suka fitar, an samu ci gaba a GDP na ƙasa da kashi 4.4%, tare da ƙaruwa a ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje zuwa dala biliyan 42. Wannan kuwa ba ƙaramin ci gaba ba ne, musamman idan aka yi la’akari da rikicin tattalin arzikin duniya…
Read More