11
Oct
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a ranar Alhamis ya yi kira da a gudanar da sauye-sauye na musamman domin rushe shingayen da ke hana mata a Nijeriya cikakken shiga harkokin siyasa, kasuwanci da shugabanci. Da yake jawabi a taron Gender Impact Inɓestment Summit na uku a da ya gudana a birnin Legas, Sanusi ya bayyana cewa samar da daidaito tsakanin maza da mata ba sadaka ba ce, illa dai wani lamari ne na hankali da adalci. Ya buƙaci a yi gyaran kundin tsarin mulki da kuma tsarin ɓangaren kuɗi…
