ukarofi

12719 Posts
Asisat Oshoala: Tauraruwar Nijeriya da ke haskakawa a Saudiya

Asisat Oshoala: Tauraruwar Nijeriya da ke haskakawa a Saudiya

Tauraruwar Super Falcons, Asisat Oshoala, ta ci gaba da haskakawa a gasar mata ta ƙasar Saudiyya, inda aka zaɓe ta a matsayin ‘yar wasa mafi kyau ta watan Satumba, 2025. Oshoala ta jawo hankalin duniya bayan ta ci ƙwallaye a jerin wasanni da dama, lamarin da ya sa ta zama tauraruwa a gasar da ke ci gaba da samun karɓuwa a yankin Gabas ta Tsakiya. “Na yi farin ciki da wannan yabo, amma abin da ya fi min daɗi shi ne ganin yadda mata daga Afirka ke samun damar nuna bajinta,” inji Oshoala. Tawagarta ta fitar da sanarwa tana yaba…
Read More
Joshua ya shirya komawa Nijeriya don fafatawa da Bakole a Rumble in the Jungle II

Joshua ya shirya komawa Nijeriya don fafatawa da Bakole a Rumble in the Jungle II

Fitaccen ɗan dambe ɗan asalin Nijeriya, Anthony Joshua, na iya komawa ƙasar mahaifansa domin yin gagarumin fafatawa da abokin hamayyarsa Martin Bakole a wani babban gasa da ake shirin kira “Rumble in the Jungle II”, wanda ake sa ran gudanarwa a birnin Legas cikin shekarar 2026. Rahotanni daga majiyoyi kusa da masu shirya gasar sun bayyana cewa an kammala tattaunawa tsakanin Joshua da hukumar wasanni ta Nijeriya (NSC), tare da tallafin wasu manyan kamfanonin sadarwa da bankuna da ke son ɗaukar nauyin taron. Idan wannan lamari ya tabbata, zai zama karo na farko da Joshua zai yi fafatawa a wasar…
Read More
Yadda Nijeriya ta tafka asarar biliyoyin Naira a lokacin yajin aikin PENGASSAN – NNPCL

Yadda Nijeriya ta tafka asarar biliyoyin Naira a lokacin yajin aikin PENGASSAN – NNPCL

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Yajin aikin na ƙasa da ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta Nijeriya suka shiga a faɗin Nijeriya ya jawo wa ƙasar nan asarar gangar man fetur 200,000 a kowacce rana wanda hakan ya shafi samar da iskar gas da wutar lantarki. Shugaban kamfanin man NNPC na ƙasa, Bayo Ojulari, ne yasa sanar da hakan a ranar Litinin bayan kammala wani zama da shugaban ƙasa Bola Tinubu a gidan gwamnati da ke Abuja. “Mun rasa sama da ganga 200,000 a kullum na ɗanyen mai. Haka kuma mun samu tsaiko wajen samar da iskar gas. Haka ma…
Read More
An yi walimar haddar Alƙur’ani na ɗalibai 21 na makarantar Tarteelil ƙur’an Wattajweed

An yi walimar haddar Alƙur’ani na ɗalibai 21 na makarantar Tarteelil ƙur’an Wattajweed

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Madarasatul Tarteelil  ƙur'an Wattajweed dake kusa da Almuntada masallacin ɗorayi na Marigayi Sheikh Ja'afar ta gudanar da walimar haddar Al'ƙur'ani mai girma na ɗalibai 21 karo na biyar a ɗakin taro na yaye ɗalibai dake sabuwar Jami'ar Bayero ranar Lahadi. A jawabinsa shugaban cibiyar ƙur'ani na Jami'ar Bayero Farfesa Ahmad Murtala wanda Dakta Ibrahim Ahmad Indabawa ya wakilta ya ce idan aka yi duba da ƙanƙantar shekarun ɗalibai da suka yi haddar, al'umma na da ƙarfin gwiwar gaba za ta yi kyau a tsakanin matasa masu tasowa.  Ya yi kira ga mahaddatan kan suyi ƙoƙarin…
Read More
Badaƙalar Nnaji: Da na gaba ake ganin zurfun ruwa – Atiku ya buƙaci a yi bincike kan takardun karatun Tinubu da ministocinsa

Badaƙalar Nnaji: Da na gaba ake ganin zurfun ruwa – Atiku ya buƙaci a yi bincike kan takardun karatun Tinubu da ministocinsa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kafa tsarin bogi da yaudara a cikin gwamnati, bayan murabus ɗin tsohon Ministan ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, saboda cece-kuce kan takardun karatunsa. A cikin wata sanarwa da Atiku ya fitar a Abuja ranar Talata, ya bayyana murabus ɗin Nnaji a matsayin “abin kunya ga ƙasa,” yana mai cewa hakan alama ce ta lalacewar ɗabi’a a cikin gwamnati mai ci. Atiku, wanda ya riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya ce saƙe-saƙe da jabu sun zama ruwan dare…
Read More
Kuɗin janye tallafin mai: SERAP ta yi barazanar maka gwamnoni 36 da Ministan Abuja a kotu

Kuɗin janye tallafin mai: SERAP ta yi barazanar maka gwamnoni 36 da Ministan Abuja a kotu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar da ke mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Nijeriya ta SERAP ta yi kira ga gwamnonin jihohi 36 da ministan Abuja, Nyesom Wike, su fitar da cikakken bayani kan yadda aka kashe kuɗin da ake raba musu. Kungiyar tana buƙatar bayani ne kan kuɗin da suka samu daga asusun rarraba kuɗi na FAAC bayan cire tallafin man fetur. SERAP ta ce an kiyasta cewa jihohi da Abuja sun karɓi kusan Naira tiriliyan 14 daga irin waɗannan kuɗi tun daga tsakiyar shekarar 2023. Kungiyar ta ce, duk da kuɗin da suka samu amma babu wani…
Read More
Ku ajiye kuɗinku a bankunan da CBN ya bai wa lasisi — NDIC ta gargaɗi ’yan Nijeriya

Ku ajiye kuɗinku a bankunan da CBN ya bai wa lasisi — NDIC ta gargaɗi ’yan Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Ajiyar Kuɗaɗe a Bankunan Kasuwancin Nijeriya (NDIC) ta gargadi ’yan Nijeriya da su tabbata cewa suna ajiye kuɗinsu ne a bankunan da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ba da lasisi. Da yake jawabi a Ranar Musamman ta Hukumar a bikin kasuwanci na ƙasa da ƙasa na Abuja karo na 20, wanda ƙungiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Abuja (ACCI) ta shirya a ranar Alhamis, Manajan Daraktan NDIC, Sunday Thompson, ya kuma shawarci ’yan ƙasa da su guji fazawa cikin tsarukan zamba (ponzi schemes). Thompson, wanda Bimpe Akande, Daraktar Sashen Gudanar da Ayyuka ta NDIC…
Read More
Rashin bai wa mata dama na daƙile cigaban Nijeriya – Sarki Sanusi

Rashin bai wa mata dama na daƙile cigaban Nijeriya – Sarki Sanusi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a ranar Alhamis ya yi kira da a gudanar da sauye-sauye na musamman domin rushe shingayen da ke hana mata a Nijeriya cikakken shiga harkokin siyasa, kasuwanci da shugabanci. Da yake jawabi a taron Gender Impact Inɓestment Summit na uku a da ya gudana a birnin Legas, Sanusi ya bayyana cewa samar da daidaito tsakanin maza da mata ba sadaka ba ce, illa dai wani lamari ne na hankali da adalci. Ya buƙaci a yi gyaran kundin tsarin mulki da kuma tsarin ɓangaren kuɗi…
Read More
Nijeriya ta samu gurbin maiyyata 66,910 a Hajjin 2026 – NAHCON

Nijeriya ta samu gurbin maiyyata 66,910 a Hajjin 2026 – NAHCON

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta sanar da ranar 31 ga Disamba, 2025, a matsayin wa’adi na ƙarshe ga duk wanda yake son zuwa aikin Hajji a shekarar 2026 don kammala biyan kuɗin kujerarsa. Shugaban hukumar na ƙasa, Farfaesa Abdullahi Usman, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar ranar Juma’a a birnin Kano. Usman ya ce, an tsara wannan wa’adi ne domin tabbatar da shirye-shirye cikin lokaci da kuma gudanar da aikin Hajji cikin tsari ba tare da tangarda ba. Ya bayyana cewa, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihohi za su biya aƙalla…
Read More
Dangote ya fara gina kamfanin takin na Naira Tiriliyan uku a Habasha

Dangote ya fara gina kamfanin takin na Naira Tiriliyan uku a Habasha

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban gungun kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ƙaddamar da aikin ginin masana’antar takin zamani a birnin Gode da ke yankin Kudu maso Gabashin Habasha. Masana’antar, wacce za ta kasance ta haɗin gwiwa tsakanin Dangote Group da hukumar zuba jari ta Habasha, za ta rika samar da ton miliyan 3 na taki a shekara bayan kammala ta. Aikin na da nufin amfani da albarkatu don bunkasa noma, samar da ayyukan yi, da tabbatar da wadatar abinci Afrika. Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya bayyana masana’antar a matsayin alamar hadin kai da ci gaban kasa, yana mai cewa…
Read More