ukarofi

12715 Posts
2027: Ba ido rufe ADC ke neman mulkin Nijeriya ba — David Mark 

2027: Ba ido rufe ADC ke neman mulkin Nijeriya ba — David Mark 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Jam’iyyar ADC, David Mark, ya ce manufar jam’iyyarsa ba wai neman mulki ido rufe ba ne, illa dai hidima ga ‘yan Nijeriya. Da yake jawabi a taron farko na kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar a Abuja, Mark ya ce ADC an kafa ta ne domin gina ƙasa mai adalci da damar ci gaba ga kowa da kowa. Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta zama mai gaskiya, ladabi da gaskiya a shugabanci, tare da tabbatar da cewa cancanta tafi biyayya a muƙamai. Mark ya kuma ce ADC za ta tabbatar da gudanar…
Read More
Siyasar Nijeriya: Har yanzu kamar an gudu ba a tsira ba 

Siyasar Nijeriya: Har yanzu kamar an gudu ba a tsira ba 

Bisa ga dukkan alamu dai sake maimaita aji za a sayi. Ma'ana a yunƙurin talakawa na hutawa da mulkin ɗan Jummai kuma a sake ɗauko ɗan Juma. Al'umman Nijeriya na buƙatar canji, amman har yanzu ba su ɗauko chanji ba. Har yanzu al'umma na cikin ruɗu. Kuɗi da ƙabilanci sun yi musu kanwaya, gaba ɗaya kowa ya ruɗe. Wasu suna bin mayaudara, wasu na bin mawaƙa, wasu kam har yanzu suna bin jahilan malamai. Yaushe malamin da ya ke ɗan siyasa zai gaya maka gaskia akan wanda zaka zaɓa? Yaushe mawakin da kuɗi ya ke nema zai gaya maka gaskia…
Read More
Falalar ’yan uwantaka a Musulunci

Falalar ’yan uwantaka a Musulunci

Bismillahi rahmanir Rahim. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da ɗaukaka, wanda sanya Muminai ’yan uwan juna, sashinsu na taimakon sashi. Salati da sallama su ƙara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da Sahabansa, da waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa, har zuwa ranar sakamako. Lalle ne 'yan uwantaka tsakanin mutane a addini bai taƙaita ga Musulmai kaɗai ba, har ga waɗanda ba Musulmai ba sukan zama 'yan uwa a addininsu, amma yan uwantaka ta Musulunci ya fi kowani irin 'yan uwantaka, saboda shi 'yan uwantaka ne akan addinin gaskiya, kuma alaƙar ɓata yankewa har bayan…
Read More
NEF ta fara taron nema wa Arewa mafita

NEF ta fara taron nema wa Arewa mafita

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta fara gudanar da wani taron kwanaki biyu a Abuja domin neman mafita ga matsalar talauci da kuma ci gaban tattalin arzƙiin yankin arewa. Taron zai kuma kasance dandalin bajakolin ma’adanan asa da ke jibge a yankin, da nufin jan hankalin masu zuba jari. Mai magana da yawun ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jiddare, ya bayyana wa BBC cewa manufar taron ita ce "kawo haske kan damarmaki da albarkatun da ake da su a arewa". Ya ce, “Kowa ya sani yadda tattalin arziƙin arewa ya koma baya", inda ya ce yankin na fama…
Read More
Bai kamata ana yi wa matan Kannywood kuɗin goro ba – Maryam CTV

Bai kamata ana yi wa matan Kannywood kuɗin goro ba – Maryam CTV

Daga MUKHTAR YAKUBU An ɗan samu lokaci ba a ganin fuskar Jaruma Maryam Sulaiman wato Maryam CTV a wajen aikin fim wanda hakan ya sa mutane suka fara cigiyar ta ko ina ta shiga? Jarumar da ta yi fice a fitowa a matsayin uwa a gidan manyan masu kuɗi a cikin fim wadda har ake yi mata laƙabin matar manya, ta daɗe ana damawa da ita, kuma har yanzu tauraruwar ta tana haskawa. Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Maryam CTV dangane da rashin ganin ta, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance. MANHAJA: Maryam…
Read More
Masu dukan mata ku tuba ku daina!

Masu dukan mata ku tuba ku daina!

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Kwanaki wata marubuciya ta yi wani rubutu a shafinta na manhajar Facebook, inda ta bayyana takaicinta game da halayyar wasu azzaluman maza da ke cin zarafin matansu ta hanyar duka, abin da ya jawo muhawara mai zafi daga ɓangarori daban-daban, sakamakon yadda wannan mummunar halayya ke ci musu tuwo a ƙwarya. Mata da dama, musamman masu aure, suna kokawa da yadda wasu mazan ke kasa daurewa fushi da ɓacin ransu, da zarar matansu sun musu wani kuskure ko laifi sai su hau jibgarsu kamar jakuna, ba mutane ba. Wani lokaci ma idan abin ya zo da…
Read More
Asisat Oshoala: Tauraruwar Nijeriya da ke haskakawa a Saudiya

Asisat Oshoala: Tauraruwar Nijeriya da ke haskakawa a Saudiya

Tauraruwar Super Falcons, Asisat Oshoala, ta ci gaba da haskakawa a gasar mata ta ƙasar Saudiyya, inda aka zaɓe ta a matsayin ‘yar wasa mafi kyau ta watan Satumba, 2025. Oshoala ta jawo hankalin duniya bayan ta ci ƙwallaye a jerin wasanni da dama, lamarin da ya sa ta zama tauraruwa a gasar da ke ci gaba da samun karɓuwa a yankin Gabas ta Tsakiya. “Na yi farin ciki da wannan yabo, amma abin da ya fi min daɗi shi ne ganin yadda mata daga Afirka ke samun damar nuna bajinta,” inji Oshoala. Tawagarta ta fitar da sanarwa tana yaba…
Read More
Joshua ya shirya komawa Nijeriya don fafatawa da Bakole a Rumble in the Jungle II

Joshua ya shirya komawa Nijeriya don fafatawa da Bakole a Rumble in the Jungle II

Fitaccen ɗan dambe ɗan asalin Nijeriya, Anthony Joshua, na iya komawa ƙasar mahaifansa domin yin gagarumin fafatawa da abokin hamayyarsa Martin Bakole a wani babban gasa da ake shirin kira “Rumble in the Jungle II”, wanda ake sa ran gudanarwa a birnin Legas cikin shekarar 2026. Rahotanni daga majiyoyi kusa da masu shirya gasar sun bayyana cewa an kammala tattaunawa tsakanin Joshua da hukumar wasanni ta Nijeriya (NSC), tare da tallafin wasu manyan kamfanonin sadarwa da bankuna da ke son ɗaukar nauyin taron. Idan wannan lamari ya tabbata, zai zama karo na farko da Joshua zai yi fafatawa a wasar…
Read More
Yadda Nijeriya ta tafka asarar biliyoyin Naira a lokacin yajin aikin PENGASSAN – NNPCL

Yadda Nijeriya ta tafka asarar biliyoyin Naira a lokacin yajin aikin PENGASSAN – NNPCL

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Yajin aikin na ƙasa da ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta Nijeriya suka shiga a faɗin Nijeriya ya jawo wa ƙasar nan asarar gangar man fetur 200,000 a kowacce rana wanda hakan ya shafi samar da iskar gas da wutar lantarki. Shugaban kamfanin man NNPC na ƙasa, Bayo Ojulari, ne yasa sanar da hakan a ranar Litinin bayan kammala wani zama da shugaban ƙasa Bola Tinubu a gidan gwamnati da ke Abuja. “Mun rasa sama da ganga 200,000 a kullum na ɗanyen mai. Haka kuma mun samu tsaiko wajen samar da iskar gas. Haka ma…
Read More
An yi walimar haddar Alƙur’ani na ɗalibai 21 na makarantar Tarteelil ƙur’an Wattajweed

An yi walimar haddar Alƙur’ani na ɗalibai 21 na makarantar Tarteelil ƙur’an Wattajweed

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Madarasatul Tarteelil  ƙur'an Wattajweed dake kusa da Almuntada masallacin ɗorayi na Marigayi Sheikh Ja'afar ta gudanar da walimar haddar Al'ƙur'ani mai girma na ɗalibai 21 karo na biyar a ɗakin taro na yaye ɗalibai dake sabuwar Jami'ar Bayero ranar Lahadi. A jawabinsa shugaban cibiyar ƙur'ani na Jami'ar Bayero Farfesa Ahmad Murtala wanda Dakta Ibrahim Ahmad Indabawa ya wakilta ya ce idan aka yi duba da ƙanƙantar shekarun ɗalibai da suka yi haddar, al'umma na da ƙarfin gwiwar gaba za ta yi kyau a tsakanin matasa masu tasowa.  Ya yi kira ga mahaddatan kan suyi ƙoƙarin…
Read More