ukarofi

12715 Posts
Ni Musulmi ne kawai, ba ‘sectless’ ba

Ni Musulmi ne kawai, ba ‘sectless’ ba

Daga ALI ABUBAKAR SADIK Na haura shekaru hamsin a duniya wadda gaba dayanta a cikin nazari da karatun addinin musulunci ta wanzu har zuwa yanzu. Na fara karatun Allo a gidanmu, na je makarantar Malam Manzo Arzai, na kuma halarci makarantar buzu ta Marigayi Malam Auwalu Jazallah. A jami'a na karanci Islamic Studies inda na koyi tarbiyar research. A duk tsawon wannan lokaci, duk da gidanmu yan Darika ne, ban taba wazifa ba, ban taba Mandiri ba, don haka ni tsawon rayuwata tun kafin na yi karatu mai zurfi kungiyar addini bata taba bani sha'awar bin kowacce iri ba. Amma…
Read More
A idonmu aka yi komai, mu ma mun taya daidai gwargwadon ikonmu

A idonmu aka yi komai, mu ma mun taya daidai gwargwadon ikonmu

Daga MUHAMMAD SANI YUNUSA AL-KANAWIY Abduljabbar Kabara ya fara da'awarsa a bisa ƙoƙarin saɓa wa duk wani abu da abokan hamayyarsa suke yarda da shi, hakan ta sa, ya saɓa wa usul ɗin mazhabin da ya ke a kai ya gada daga iyayensa, misali, yarda da sahabban ma'aiki gabaɗaya, a bisa jagorancin Sa’adat, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, a jere, kawai don ’yan Izala suna ƙarfafa hakan! Sai ya fara lalube da neman duk wata shubuha da za ta sanya ya zargi wani sahabi, don ya saba da yan Izala, waɗanda suna tsananin kiyaye wannan fage, kamar yadda…
Read More
Ministar Tinubu ta tallafa wa mata da matasa sama da 1000 a Nasarawa

Ministar Tinubu ta tallafa wa mata da matasa sama da 1000 a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafia Ministar harkokin mata ta Tarayyar Najeriya, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim, a ƙarshen mako mako da ake ciki ta bayar da kayayyaki masu darajar miliyoyin nairori domin taimakawa sama da mata 1000 a ƙananan hukumomi 13 na Jihar Nasarawa a matsayin wani ɓangare na ayyukanta na jin ƙai ga marasa galihu a cikin al’umma. A yayin wannan taro, ministar ta kuma ƙaddamar da shirin lafiya na musamman domin magance matsalolin lafiya a matakin ƙananan hukumomi a cikin jihar. Kayayyakin da aka raba sun haɗa da: injin niƙa, kwalayen iskar gas na girki, injin ɗinki, turamen…
Read More
Gwamnatin Kano ta yi ta’aziyyar Babban Malami na Madabo

Gwamnatin Kano ta yi ta’aziyyar Babban Malami na Madabo

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Cikin kaɗuwa da jimami Gwamnatin Jihar Kano ta samu labarin rasuwar Malam Kabiru Ibrahim, Babban Malami na Madabo. Wanda fitaccen malamin addinin Musulunci ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa ilimin addini da koyar da kyawawan ɗabi’u, abin da ya shafi al'umma da dama a Kano da wajen ta. Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin Malam Kabiru Ibrahim, wanda aka bayyana a matsayin ginshiƙin ilimi, tawali’u, da zaman lafiya. Karatuttukansa da shawarwarinsa sun taka muhimmiyar rawa wajen gina ɗabi’a da ruhin addini a cikin…
Read More
Bola Tinubu ne zai sake kafa gwamnati a zaɓe mai zuwa – Maituraka

Bola Tinubu ne zai sake kafa gwamnati a zaɓe mai zuwa – Maituraka

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban majalisar Dattijai, Alhaji Abdul'aziz Maituraka ya faɗi haka a Katsina a wajen bikin karramashi bayan da gwamna Dikko Raɗɗa da ya bashi muƙamin babban mataimaki na musamman kan faɗakarwa. Ya ce a iya sanin sa jihar Katsina babu wata jam'iyyar da za ta ja da gwamnatin APC ta Dikko Raɗɗa. Maituraka ya godewa Mallam Dikko Raɗɗa bisa wannan nauyi da ya ɗora masa inda ya tabbatar masa da cewa zai tunkari yiwa APC aiki bisa amana da jajircewa. Yayi alƙawarin zama da masu ƙananan sana'o'i a Katsina da suka…
Read More
ADC a Katsina ta yi Allah wadai da kalaman ɓatanci ga Mustapha Inuwa

ADC a Katsina ta yi Allah wadai da kalaman ɓatanci ga Mustapha Inuwa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban Jam'iyyar ADC a jihar Katsina Alhaji Musa Usman Wamba Funtua ya yi wannan magana yayin da yake mai da martani kan kalaman ɓatanci da aka tura wasu a Ɗanmusa da Yantumaki suka yi don ɓata sunan jagoran jam'iyyar adawa na ADC a jihar,Dr Mustapha Inuwa. "Jam'iyyar ta kuma lashi takobin cewa a zaɓ,e na shekara 2027 mai zuwa ,kafin sha biyun rana ta tiƙa APC da ƙasa a jihar Katsina,"inji Wamba. Shugaban jam'iyyar ya ce idan al'ummar Ɗanmusa da Yantumaki ba su gode wa Dr Mustapha Muhammad Inuwa ba, game da samar masu da…
Read More
DA ƊUMI-ƊUMI: Ɗan jaridar Daily Trust ya zama sabon shugaban ƙungiyar manema labarai a Nasarawa

DA ƊUMI-ƊUMI: Ɗan jaridar Daily Trust ya zama sabon shugaban ƙungiyar manema labarai a Nasarawa

DAGA JOHN D. WADA a Lafia Ɗan jaridar Daily Trust da ke wakiltar jaridar a Jihar Nasarawa, Kwamared Abubakar Abdullahi ya zama sabon shugaban masu turo da rahotanni wato Correspondents’ Chapel a turance na Ƙungiyar ƴan Jaridu ta (NUJ) reshen Jihar Nasarawa. Kwamared Abubakar Abdullahi ne sabon shugaban, inda Christopher Nyamtu na gidan radiyon tarayya wato Federal Radio Corporation ya zama sakatare a zaɓen da aka gudanar. Wanda shugaban NUJ na jihar Kwamared Salihu Alkalib ya sa ido a kai. Abdullahi ya lashe zaɓen ne bayan ya samu ƙuri’u 21, yayin da abokin takararsa, Danjuma Joseph na National Accord (jaridar…
Read More
Jam’iyyar APC a Zamfara ta karɓi ɗan takarar PDP na Ƙaura Namoda ta Kudu

Jam’iyyar APC a Zamfara ta karɓi ɗan takarar PDP na Ƙaura Namoda ta Kudu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗan takarar Ƙaura Namoda ta Kudu a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Muhammad Lawal Kurya ya bar jam’iyyar sa ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a ƙasa. Zaɓen cike gurbi da aka gudanar a ranar 16 ga watan Satumba, 2025 inda APC ta yi nasara da gagarumin rinjaye inda ta doke jam’iyyar PDP mai mulki, Muhammad Lawal Kurya shine ya tsaya takarar a Ƙarƙashin jam'iyyar PDP. Muhammad Lawal Kurya ya bayyana goyon bayan sa ga jam'iyyar APC a wajen wani taro da ƙungiyar Hon. Yazid Shehu Danfulani Project ta…
Read More
Gwamna Sule ya samu lambar yabo ta Jakadan Ilimi daga jaridar Independent Newspaper

Gwamna Sule ya samu lambar yabo ta Jakadan Ilimi daga jaridar Independent Newspaper

DAGA JOHN D. WADA, a Lafia A cewar kwamitin lambar yabon na musamman na jaridar Independent Newspaper a wajen taron an bai wa Gwamna Sule wannan lambar yabo ne saboda gagarumin aikinsa a fannin ilimi ta hanyar zuba jari da wayar da kawuna da kuma tallafa wa ilimin yara a jihar sa ta Nasarawa dama ƙasa baki ɗaya. Wata sanarwa daga babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Ibrahim Addra daga bisani da aka raba wa manema labarai ciki har da wakilin mu ya bayyana cewa wannan karramawar ta kuma nuna yadda gwamna Sule ke ƙoƙari wajen faɗaɗa damar samun ilimi,…
Read More
Kano za ta saka wa Tinubu da ruwan ƙuri’u a 2027 — Barau Jibrin

Kano za ta saka wa Tinubu da ruwan ƙuri’u a 2027 — Barau Jibrin

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce mutanen Jihar Kano za su rama kyakkyawar alherin da Shugaba Bola Tinubu yake nunawa gare su da zaben sa da kuri’u masu yawa a zaben 2027 mai zuwa. Sanata Barau, wanda ke wakiltar Mazabar Kano ta Arewa a majalisar dattawa, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ƙaddamar da Shirin Tallafin Karatu ga Dalibai ƙarƙashin gidauniyarsa, a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano. Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da Shugaba Tinubu ya yi wa Kano shine amincewa da haɓaka Kwalejin Ilimi ta…
Read More